{"id":4893,"date":"2025-07-02T10:38:47","date_gmt":"2025-07-02T10:38:47","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=4893"},"modified":"2025-07-02T10:40:57","modified_gmt":"2025-07-02T10:40:57","slug":"mutane-sama-da-207-sun-rasu-sakamakon-ambaliyar-ruwa-a-mokwa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/mutane-sama-da-207-sun-rasu-sakamakon-ambaliyar-ruwa-a-mokwa\/","title":{"rendered":"Mutane Sama Da 207 Ne Suka Rasu Sakamakon Ambaliyar Ruwa A Mokwa"},"content":{"rendered":"<p>Mutane sama da dari biyu da bakwai (207) ne suka rasu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afkawa al\u2019ummar karamar hukumar Mokwa a jihar Neja.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban Hukumar Kula da Yanayi da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Abdullahi Baba Arah, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Minna, game da kokarin da hukumar ke yi wajen rage radadin bala\u2019o\u2019i da dama da suka hada da fashewar tankokin mai a Agaie da Diko, hare-haren &#8216;yan bindiga da kuma ambaliya mai muni da ta auku kwanan nan a Mokwa, domin hana faruwar hakan nan gaba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cewarsa, mutane sama da 500 ne suka jikkata sakamakon ambaliyar, yayin da ba a tantance adadin wadanda suka bace ba tukuna. Ya ce, ko a jiya Talata, 2 ga watan Yuli na wannan shekara, wasu jami\u2019an hukumar za su tashi daga Minna zuwa Mokwa domin ci gaba da aikin taimakon gaggawa da tattara bayanai.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da yake magana kan wadanda gidajensu ko kadarorinsu suka lalace, ya bayyana cewa an baiwa kowane mutum Naira 500,000 domin samun damar haya a wuri mai kyau, tare da wasu tallafin kayan abinci da aka raba ga dukkan wadanda bala\u2019in ya shafa don rage musu radadi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Abdullahi Baba Arah, ya kara da cewa an\u00a0 samu nasarar wannan kokari ne bisa goyon baya da gaggauta daukar mataki da Gwamnan jihar , Mohammed Umar Bago ya yi, wanda ya bayyana a matsayin jajirtaccen gwamna.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban hukumar ya mika sakon ta\u2019aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa tare da nuna godiya ga dukkan wadanda suka bada gudunmawa domin rage radadin bala\u2019in da ya auku, tare da yin kira da a ci gaba da bayar da taimako domin cimma nasara.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Abdullahi Baba Arah ya kuma yi amfani da damar wajen yi kira al\u2019ummar jihar Neja da ke zaune a yankunan bakin kogi, musamman wadanda ke kan hanyoyin ruwa, da su gaggauta barin wuraren\u00a0 domin kaucewa hadurran da ke tattare da ambaliya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Aliyu Lawal<\/em><\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Mutane sama da dari biyu da bakwai (207) ne suka rasu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afkawa al\u2019ummar karamar hukumar Mokwa a jihar Neja. &nbsp; Shugaban Hukumar Kula da Yanayi da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Abdullahi Baba Arah, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Minna, game da kokarin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":4060,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[320,836],"class_list":["post-4893","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-ambaliya","tag-neja"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/04\/Facts-About-Niger-State-Population.webp","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4893","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4893"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4893\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4897,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4893\/revisions\/4897"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4060"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4893"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4893"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4893"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}