{"id":4890,"date":"2025-07-01T17:22:41","date_gmt":"2025-07-01T17:22:41","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=4890"},"modified":"2025-07-01T17:24:37","modified_gmt":"2025-07-01T17:24:37","slug":"dalibai-sama-da-200-sun-sami-digiri-mai-daraja-ta-daya-a-fud","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/dalibai-sama-da-200-sun-sami-digiri-mai-daraja-ta-daya-a-fud\/","title":{"rendered":"Dalibai Sama Da 200 Sun Sami Digiri Mai Daraja Ta Daya A FUD"},"content":{"rendered":"<p>Jami\u2019ar Tarayya ta Dutse (FUD) ta ce dalibai 209 za su karbi shaidar digiri mai daraja ta daya a taron yaye dalibai karo na 8 da na 9 da aka shirya gudanarwa a wannan wata.<\/p>\n<p>Shugaban Jami\u2019ar, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da \u2018yan jarida kan shirye-shiryen da aka kammala domin taron yaye daliban a Dutse, Jihar Jigawa.<\/p>\n<p>Ya ce, kididdigar yawan daliban da za a yaye ta nuna cewa, jimillar dalibai 1,271 sun samu digiri mai daraja ta biyu matakin farko(SecondClassUpper), yayin da dalibai 2,034 suka samu digiri mai daraja ta biyu,\u00a0 mataki na biyu, kasa (Second Class Lower), sannan kusan dalibai 559 suka samu digiri mai daraja ta uku (Third Class).<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa, adadin jimillar daliban da za a yaye ya kai 4,277.<\/p>\n<p>Farfesa Abdulkarim ya kara da cewa, adadin daliban da ke karatu a jami\u2019ar ya karu daga 202 a shekarar 2011\/2012 zuwa 18,000 a halin yanzu, tare da karuwar kwasa-kwasai daga guda 5 a 2011\/2012 zuwa guda 45 a yau.<\/p>\n<p>Shugaban Jami\u2019ar ya bayyana cewa, za a gudanar da laccar taron yaye dalibai karo na 8 da 9, inda tsohon Shugaban Jami\u2019ar na farko, Farfesa Jibrilla Dahiru Amin, zai gabatar da makala.<\/p>\n<p>Ya ce taken laccar shi ne: <em>&#8220;Amfani da Bincike da Kirkire-kirkire Domin Cimma Ci gaba mai Dorewa a Najeriya: Rawar da Manyan Makarantu Ke Takawa.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>Haka zalika, ya bayyana cewa, an kammala ginin sashen ilimin shari&#8217;a na jami\u2019ar,\u00a0 inda za a fara karbar dalibai a wannan sashe daga zangon karatu na gaba.<\/p>\n<p>Ya ce, shirin kafa Sashen Kimiyyar Magunguna (Pharmaceutical Sciences) na daga cikin abubuwan da ake kan tsarawa a halin yanzu.<\/p>\n<p>Farfesa Abdulkarim ya bayyana cewa, cikin shekaru hudu da suka gabata, jami\u2019ar ta samu tallafin bincike fiye da Naira miliyan 800, ciki har da Naira miliyan 113 da kamfanin Google ya bayar domin kafa dakin binciken Artificial Intelligence(binciken kwakwaf ta yanar gizo), wanda shi ne na farko a cikin manyan makarantu a yankin Arewa maso Yamma.<\/p>\n<p>Haka kuma, Farfesa Abdulkarim ya bayyana cewa, kwanan nan jami\u2019ar\u00a0 ta rattaba hannu kan yarjejeniya da Ma\u2019aikatar Ilimi ta Tarayya da Hukumar Samar da Wutar Lantarki ga Yankunan Karkara domin gina rukunin hasken rana na zamani mai karfin megawatt 1.6 wanda zai tabbatar da cewa harabar jami\u2019ar za ta rika amfani da wutar lantarki ta hasken rana.<\/p>\n<p>Ya kuma jaddada cewa daga cikin ayyukan da aka kammala a jami\u2019ar akwai sabon ginin Majalisar makarantar(Senate Building), ginin sashen koyar da ilimin shari\u2019a\u00a0 (Faculty of Law), sabon dakin karatu(Library) , dakunan daukar darasi gudabiya masu cin daliba 250 kowannensu, da dakunan koyar da Kimiyya da Fasaha (STEM), da dakunan kwana guda biyu na mata da sauran su.<\/p>\n<p>Farfesa Mohammed ya nuna godiyarsa ga \u2018yan jarida a fadin jihar Jigawa da wajen jihar bisa hadin kai da goyon baya da suke baiwa jami\u2019ar.<\/p>\n<p>Daga karshe, ya yaba wa ma\u2019aikatan jami\u2019ar bisa hadin kai da jajircewarsu, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen cimma nasarorin da Jami\u2019ar ta samu.<\/p>\n<p><em><strong>Usman Muhammad Zaria<\/strong><\/em><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Jami\u2019ar Tarayya ta Dutse (FUD) ta ce dalibai 209 za su karbi shaidar digiri mai daraja ta daya a taron yaye dalibai karo na 8 da na 9 da aka shirya gudanarwa a wannan wata. Shugaban Jami\u2019ar, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da \u2018yan jarida kan shirye-shiryen da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":4892,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11],"tags":[986,59],"class_list":["post-4890","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","tag-fud","tag-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/07\/IMG-20250701-WA0029.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4890","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4890"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4890\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4891,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4890\/revisions\/4891"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4892"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4890"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4890"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4890"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}