{"id":4846,"date":"2025-06-30T11:44:24","date_gmt":"2025-06-30T11:44:24","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=4846"},"modified":"2025-06-30T11:44:24","modified_gmt":"2025-06-30T11:44:24","slug":"jamian-gwamnatin-tarayya-sun-isa-saudiyya-wajen-janaizar-aminu-dantata","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jamian-gwamnatin-tarayya-sun-isa-saudiyya-wajen-janaizar-aminu-dantata\/","title":{"rendered":"Jami&#8217;an Gwamnatin Tarayya Sun Isa Saudiyya Wajen Jana&#8217;izar Aminu Dantata"},"content":{"rendered":"<p>Wata tawagar gwamnatin tarayyar ta isa kasar Saudiyya domin karbar gawar marigayi dattijon dan kasuwa kuma dan kishin kasa Alhaji Aminu Alhassan Dantata, gabanin jana&#8217;izar sa a birnin Madina.<\/p>\n<p>Alhaji Dantata, wanda ya rasu a ranar Asabar a birnin Abu Dhabi na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, yana da shekaru 94 a duniya, ya samu karbuwa sosai saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen harkokin kasuwanci, da taimakon jama\u2019a da kuma ci gaban kasa.<\/p>\n<p>A cewar wata sanarwa da mataimaki na musamman ga ministan yada labarai da wayar da kan jama&#8217;a na kasa ya fitar, tawagar ta Najeriyar ta bar kasar ne a ranar Lahadin inda suka isa birnin Madina da sanyin safiyar Litinin domin halartar jana&#8217;izar.<\/p>\n<p>Ministan tsaro kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ke jagorantar wannan ayarin Gwamnatin Tarayya.<\/p>\n<p>Sauran mambobin sun hada da ministan shari\u2019a kuma babban lauyan gwamnai, Prince Lateef Fagbemi, SAN; da Ministan yada labarai da wayar da kan jama\u2019a, Alhaji Mohammed Idris; da kuma ministan kasa a ma&#8217;aikatar gidaje, Honorabul Yusuf Abdullahi Ata.<\/p>\n<p>Haka kuma a cikin tawagar akwai fitattun malaman addinin musulunci da suka hada da Dr. Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da Khalifa Abdullahi Muhammad limamin masallacin Dantata dake Abuja. Har ila yau, jami\u2019an ofishin jakadancin Najeriya da ke Jeddah, karkashin jagorancin Ambasada Muazzam Ibrahim Nayaya, sun bi sahun tawagar tare da gudanar da shirye-shiryen jana\u2019izar da za a yi a yau (Litinin) a birnin Madina.<\/p>\n<p>Sanarwar ta bayyana cewa, Alhaji Aminu Dantata shahararren dan kasuwa wanda aka sheda da rikon amana, da yi wa kasa hidima wanda ya dauki tsawon shekaru da dama yana shafar rayuka da dama a fadin Najeriya da ma sauran wurare.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Wata tawagar gwamnatin tarayyar ta isa kasar Saudiyya domin karbar gawar marigayi dattijon dan kasuwa kuma dan kishin kasa Alhaji Aminu Alhassan Dantata, gabanin jana&#8217;izar sa a birnin Madina. Alhaji Dantata, wanda ya rasu a ranar Asabar a birnin Abu Dhabi na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, yana da shekaru 94 a duniya, ya samu karbuwa [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":18,"featured_media":4847,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1292,1291,629,1293],"class_list":["post-4846","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-aminu-dantata","tag-janaizar","tag-saudiyya","tag-tawaga"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/06\/IMG-20250630-WA0038-735x400-1.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4846","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/18"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4846"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4846\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4848,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4846\/revisions\/4848"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4847"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4846"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4846"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4846"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}