{"id":4795,"date":"2025-06-11T13:49:51","date_gmt":"2025-06-11T13:49:51","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=4795"},"modified":"2025-06-11T20:03:58","modified_gmt":"2025-06-11T20:03:58","slug":"an-kama-mutane-da-dama-a-los-angeles-bayan-sanya-dokar-hana-fitar-dare","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/an-kama-mutane-da-dama-a-los-angeles-bayan-sanya-dokar-hana-fitar-dare\/","title":{"rendered":"An Kama Mutane Da Dama A Los Angeles Bayan Sanya Dokar Hana Fitar Dare"},"content":{"rendered":"<p>&#8216;Yan Sanda a birnin Los Angeles da ke Amurka sun ce sun yi nasarar kama mutane da dama, bayan da aka shiga rana ta biyar ana zanga-zangar nuna adawa da kamen bakin haure da gwamnatin Donald Trump ke yi.<\/p>\n<p>Har yanzu dai ana ci gaba da farautar ba\u0199in haure a yankin, duk kuwa da zanga-zangar adawa da matakin da aka faro a ranar Juma&#8217;ar da ta gabata, inda a yanzu aka tura dakarun tsaro don ba da kariya ga jami&#8217;an shigi da fici su samu damar gudanar da ayyukansu.<\/p>\n<p>Wannan mataki dai ya haifar da musayar yawu tsakanin hukumomin jihar da kuma Trump, duk da cewa ya sha alwashin ci gaba da aiwatar da \u0199udurinsa, matakin da ya sanya gwamnan jihar ta Califonia Gavin Newsom, ya zargin shi da yi wa dimodara\u0257iyya karan tsaye.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A jiya Talata ne dai Trump ya kare matakinsa na tura dakaru dubu 4 da sojojin ruwa 700 yankin na Los Angeles, ya na mai cewa ya yi hakan ne don dakatar da ma\u0199iyan mamaye birnin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Dakarun dai basu da ikon yin kame, aikinsu shi ne tabbatar da tsaron jami\u2019an da ke gudanar da kamen da kuma kayayyakin gwamnati.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Magajiyar garin Los Angeles, Karen Bass ta sanya dokar hana fita a daren jiya da kuma safiyar yau Laraba a wani yanki na birnin, inda ta ce an \u0257auki matakin ne sakamakon yadda ake fasha shaguna da kuma sace kayayyaki.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Bayan sanya dokar hana fitar da ta fara aiki daga \u0199arfe 2 na daren jiya agogon Amurka, \u01b4ansanda sun kutsa yankuna da dama, inda suke harba alburushin roba don tarwatsa masu zanga-zangar.<\/p>\n<p><strong><em>rfi<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&#8216;Yan Sanda a birnin Los Angeles da ke Amurka sun ce sun yi nasarar kama mutane da dama, bayan da aka shiga rana ta biyar ana zanga-zangar nuna adawa da kamen bakin haure da gwamnatin Donald Trump ke yi. Har yanzu dai ana ci gaba da farautar ba\u0199in haure a yankin, duk kuwa da zanga-zangar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":4796,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1282,18],"class_list":["post-4795","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-los-angeles","tag-zanga-zanga"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/06\/QO4ZSQNAMNME5LBLCU5ZUL2XAI.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4795","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4795"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4795\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4797,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4795\/revisions\/4797"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4796"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4795"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4795"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4795"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}