{"id":4769,"date":"2025-06-06T22:05:10","date_gmt":"2025-06-06T22:05:10","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=4769"},"modified":"2025-06-06T22:05:10","modified_gmt":"2025-06-06T22:05:10","slug":"shugaban-majalisar-dokokin-jihar-kaduna-ya-nemi-hadin-kan-alummar-jihar","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/shugaban-majalisar-dokokin-jihar-kaduna-ya-nemi-hadin-kan-alummar-jihar\/","title":{"rendered":"Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ya Nemi Hadin Kan Al&#8217;ummar Jihar"},"content":{"rendered":"<p>Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman ya bi sahun sauran al\u2019ummar Musulmi ta duniya domin bikin murnar babbar Sallah.<\/p>\n<p>A jawabinsa da safiyar ranar Sallah, shugaban majalisar ya yi godiya ga Allah Ma\u0257aukaki bisa damar da ya ba shi da sauran al\u2019umma na ganin wannan rana.<\/p>\n<p>Ya jaddada darussan da ke cikin biyayya da \u0199aunar Allah kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) da dansa Annabi Isma\u2019il (AS) suka nuna, inda ya bukaci Musulmi da su rungumi dabi\u2019un \u0199auna, tausayi, da ha\u0257in kai a wannan lokaci.<\/p>\n<p>Rt. Hon. Liman ya kuma bukaci jama\u2019ar Jihar Kaduna da su ci gaba da goyon bayan gwamnatin Gwamna Uba Sani, inda ya yaba da jajircewar gwamnan wajen ci gaban jihar.<\/p>\n<p>Ya yi addu\u2019ar neman zaman lafiya, da ha\u0257in kai a fadin Najeriya, tare da yin addu\u2019a ta musamman ga mahajjatan da ke gudanar da aikin Hajji, yana rokon Allah ya kar\u0253i ibadunsu kuma ya dawo da su gida lafiya.<\/p>\n<p>Kakakin Majalisar ya kammala da cewa: <em>\u201cEid Mubarak ga daukacin al\u2019ummar Musulmi,\u00a0 tare fatan Allah ya sa wannan lokaci ya kawo zaman lafiya da albarka a gidajenmu da ma \u0199asa baki daya.\u201d<\/em> in ji shi.<\/p>\n<p>Tun da farko yayin gabatar da hudubar sallar idi, Babban Limamin Masallacin Makera Central, Sheikh Jibril Ibrahim Maihanji, ya shawarci Musulmi da su kiyaye koyarwar addinin Musulunci bisa dokokin da aka shimfida domin samun dacewa.<\/p>\n<p>Sheikh Jibril Maihanji ya yi amfani da hudubar wajen kiran gwamnati a dukkan matakai da su samar da ayyukan yi ga matasa da dama a cikin \u0199asa, a matsayin hanyar magance miyagun dabi\u2019u da laifuka.<\/p>\n<p>Babban Limamin ya kuma shawarci matasa da su nemi ilimin zamani tare da na addini, sannan su koyi sana\u2019o\u2019i domin su zama masu amfani ga al\u2019umma.<\/p>\n<p>Sallar Idin ta samu halartar daruruwan Musulmi daga Makera da kewaye.<\/p>\n<p><em><strong>Shamsuddeen Mannir Atiku<\/strong><\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman ya bi sahun sauran al\u2019ummar Musulmi ta duniya domin bikin murnar babbar Sallah. A jawabinsa da safiyar ranar Sallah, shugaban majalisar ya yi godiya ga Allah Ma\u0257aukaki bisa damar da ya ba shi da sauran al\u2019umma na ganin wannan rana. Ya jaddada darussan da ke [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":4770,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1073,33,761],"class_list":["post-4769","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-bikin-sallah","tag-kaduna","tag-shugaban-majalisa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/06\/Fyf8IvAXwAAmEZN-e1701161515655-1.webp","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4769","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4769"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4769\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4771,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4769\/revisions\/4771"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4770"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4769"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4769"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4769"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}