{"id":4763,"date":"2025-06-05T21:19:11","date_gmt":"2025-06-05T21:19:11","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=4763"},"modified":"2025-06-05T21:19:11","modified_gmt":"2025-06-05T21:19:11","slug":"sabon-tsarin-sufuri-na-brt-zai-rage-kudin-sufuri-da-zirga-zirga-a-kaduna","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/sabon-tsarin-sufuri-na-brt-zai-rage-kudin-sufuri-da-zirga-zirga-a-kaduna\/","title":{"rendered":"Sabon Tsarin Sufuri Na BRT Zai Rage Kudin Sufuri Da Zirga-Zirga A Kaduna"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Kaduna tace shirin Bus Rapid Transit BRT da ake shirin kaddamarwa zai taimaka matuka wajen rage kudaden sufuri ga mazauna jihar, da zarar an fara aiwatar da shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Daraktan Hukumar, Injiniya Inuwa Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Kada Hive da ke Kaduna.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>An shirya taron ne domin wayar da kan jama\u2019a game da shirin BRT, sannan matakan da aka dauka ya zuwa yanzu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Taron an gudanar da shi ne domin sauraron ra\u2019ayoyin al\u2019umma kan yadda za a aiwatar da shi cikin nasara.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Injiniya Inuwa ya bayyana cewa tsarin BRT zai taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa da kara tsaro da aminci, da kuma inganta rayuwar al\u2019umma baki daya a Jihar Kaduna.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya tuna cewa kimanin watanni biyu da suka gabata ne Gwamna Uba Sani ya kaddamar da sama da motoci 100 masu amfani da iskar gas na CNG, wadanda za su rika zirga-zirga a cikin Birnin Kaduna, Zariya da Kafanchan, a wani bangare na kokarin gyara tsarin sufuri a fadin jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya bukaci mahalarta taron su yada ilimin da suka samu zuwa cikin al\u2019ummominsu domin kara fahimta da goyon bayan jama\u2019a don nasarar wannan shiri.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nasa bangaren, Ted Regino, shugaban Rebel Artic Joint Venture, wanda ke sa ido kan kwangilolin aikin, ya ce kamfaninsa ne ke lura da yadda ake gudanar da aikin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya tabbatar da cewa za a kammala aikin BRT kafin shekarar 2027, tare da karin bayani cewa kamfaninsu ya taba aiwatar da manyan ayyuka a kasa da kasa, kuma hakan zai maimaitu a Jihar Kaduna.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nata jawabin, Shugabar Jam\u2019iyyar Matan Arewa, Hajiya Rabi Saulawa, ta yaba da wannan shiri, tana mai cewa zai rage wa mata wahalhalun sufuri, musamman wadanda ke yawan zirga-zirga zuwa asibitoci, kasuwanni, wuraren aiki da makarantu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wasu daga cikin mahalarta sun jaddada bukatar kulawa da kiyaye motocin, tabbatar da dorewar shirin, da kuma kawo karshen matsalar sayar da tikiti ba bisa ka\u2019ida ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Taron ya samu halartar wakilai daga sashen sufuri, shugabannin addinai da na gargajiya, \u2019yan jarida da sauransu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>COV: Adamu Yusuf<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; Hukumar Kula da Sufuri ta Jihar Kaduna tace shirin Bus Rapid Transit BRT da ake shirin kaddamarwa zai taimaka matuka wajen rage kudaden sufuri ga mazauna jihar, da zarar an fara aiwatar da shi. &nbsp; Daraktan Hukumar, Injiniya Inuwa Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":21,"featured_media":4764,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,9],"tags":[33,1279,1278,398,1280],"class_list":["post-4763","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tattalin-arziki","tag-kaduna","tag-kudin","tag-sabon-tsarin-sufuri-na-brt-zai-rage","tag-sufuri","tag-zirga-zirga"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/06\/Screenshot_20250605-220026.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4763","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/21"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4763"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4763\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4765,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4763\/revisions\/4765"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4764"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4763"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4763"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4763"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}