{"id":4706,"date":"2025-06-01T10:42:20","date_gmt":"2025-06-01T10:42:20","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=4706"},"modified":"2025-06-01T10:42:20","modified_gmt":"2025-06-01T10:42:20","slug":"ecowas-da-coret-sun-shirya-taro-domin-cigaban-makarantun-fulani-a-kaduna","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/ecowas-da-coret-sun-shirya-taro-domin-cigaban-makarantun-fulani-a-kaduna\/","title":{"rendered":"ECOWAS Da CORET Sun Shirya Taro Domin Cigaban Makarantun Fulani A Kaduna"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ECOWAS, tare da ha\u0257in gwiwar Kungiyar Ha\u0257in Kan Masu Kiwon Gargajiya ta Afrika CORET, ta shirya taron horaswa domin \u0199arfafa fahimta kan tsarin ciyar da \u0257alibai a makarantu, musamman a cikin al\u2019ummomin makiyaya a Jihar Kaduna.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da yake \u0199addamar da taron a Ladugga, cikin Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna, Ko\u2019odinetan Shirin na CORET, Dr. Abdu Umar Ardo, ya bayyana cewa wannan horo wani bangare ne na \u0199o\u0199arin tallafa wa shirin ciyar da \u0257alibai a wasu makarantun Fulani da aka za\u0253a.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-4707\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/06\/Screenshot_20250601-111905-291x300.jpg\" alt=\"\" width=\"291\" height=\"300\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/06\/Screenshot_20250601-111905-291x300.jpg 291w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/06\/Screenshot_20250601-111905.jpg 712w\" sizes=\"auto, (max-width: 291px) 100vw, 291px\" \/><\/p>\n<p>Wannan shiri, wanda ke samun goyon bayan ha\u0257in gwiwa daga Swiss Cooperation, na nufin tallafa wa makarantun Fulani da ke Ladugga a Kaduna da kuma Maigatari a Jihar Jigawa, inda ita kuma CORET ke zama jagorar aiwatar da shirin a jihohin biyu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ko\u2019odinetan Shirin, Dr. Abdu Umar Ardo ya ce horon yana da nufin \u0199arfafa \u0199warewar Kwamitocin Gudanar da Makarantu (SBMC), \u0198ungiyoyin Iyaye Mata da na PTA, domin tallafa wa ilimin \u2018ya\u2019ya mata da rage yawan yaran da ke zaman gida ba tare da zuwa makaranta ba, musamman a cikin al\u2019ummomin makiyaya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Dr Ardo wanda ya samu wakilincin Baban Jami\u2019in Sa Ido da Kimantawa na CORET, Alhaji Bimbi Adamu Tahir, ya shawarci mahalarta taron su yi amfani da ilimin da suka samu domin amfanar da al\u2019ummominsu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nata jawabin, Shugabar \u0198ungiyar Reube Fulbe Development Rights Initiative, Hajiya Halima Yoman, ta jaddada muhimmancin ha\u0257a \u0198ungiyoyin Iyaye Mata da Kwamitocin Gudanarwar Makarantu domin kara yawan yaya mata a makarantu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ta ce hakan zai taimaka wajen shawo kan matsalar \u0199arancin halartar \u2018ya\u2019ya mata a makarantun Fulani, tana mai cewa \u201cIlmantar da mace kamar ilmantar da gaba \u0257aya al\u2019umma ne.\u201d<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nata jawabin, Wakiliyar Hukumar Ba da Ilimin Bai \u018aaya ta Jihar Kaduna (SUBEB), Hajiya Hauwa\u2019u Muhammad, ta yi karin bayani game da aikin Kwamitin kula da makarantu kamar haka.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cKwamitocin Gudanar da Makarantu suna zama hanyar sadarwa tsakanin makaranta da al\u2019umma, inda suke \u0199arfafa shiga tsakanin iyaye da shugabannin al\u2019umma da \u0199ungiyoyi na cikin gida wajen gudanar da harkokin makaranta.\u201d<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cSuna kuma marawa baya shigar \u2018ya\u2019ya mata da sauran marasa galihu makaranta, ta hanyar warware matsalolin al\u2019ada da na zamantakewa da ke hana su halarta.\u201d<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cKwamitocin na taimakawa wajen sa ido kan ingancin koyarwa da karatun \u0257alibai da malamai, domin tabbatar da gaskiya da inganci a harkar ilimi.\u201d<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wasu daga cikin mahalarta taron da suka yi magana da Radio Nigeria Kaduna sun nuna farin cikinsu, inda suka bayyana taron a matsayin mai matu\u0199ar amfani kuma daidai lokacin da ake bukata.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-4708\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/06\/Screenshot_20250601-111921-286x300.jpg\" alt=\"\" width=\"286\" height=\"300\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/06\/Screenshot_20250601-111921-286x300.jpg 286w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/06\/Screenshot_20250601-111921.jpg 706w\" sizes=\"auto, (max-width: 286px) 100vw, 286px\" \/><\/p>\n<p>Sun kuma tabbatar wa CORET cewa za su yi amfani da ilimin da suka samu wajen inganta halartar makaranta da gudanar da ita a al\u2019ummominsu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Taron ya mayar da hankali ne kan manyan al\u2019ummomin Fulani guda uku da ke Ladugga a Kachia: Wuro Nyako da Mbela Biradam da kuma Tiggirde.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>COV: Adamu Yusuf<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; &nbsp; Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ECOWAS, tare da ha\u0257in gwiwar Kungiyar Ha\u0257in Kan Masu Kiwon Gargajiya ta Afrika CORET, ta shirya taron horaswa domin \u0199arfafa fahimta kan tsarin ciyar da \u0257alibai a makarantu, musamman a cikin al\u2019ummomin makiyaya a Jihar Kaduna. &nbsp; Da yake \u0199addamar da taron a Ladugga, cikin Karamar Hukumar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":21,"featured_media":4709,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11,10],"tags":[959,1026,1252,49,1254,33,1253,972,50],"class_list":["post-4706","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","category-noma","tag-cigaban","tag-coret","tag-domin","tag-ecowas","tag-fulani","tag-kaduna","tag-makarantun","tag-shirya","tag-taro"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/06\/Screenshot_20250601-111839.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4706","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/21"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4706"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4706\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4710,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4706\/revisions\/4710"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4709"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4706"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4706"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4706"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}