{"id":4690,"date":"2025-05-30T20:05:46","date_gmt":"2025-05-30T20:05:46","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=4690"},"modified":"2025-05-30T20:06:46","modified_gmt":"2025-05-30T20:06:46","slug":"4690-2","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/4690-2\/","title":{"rendered":"Milk Value Chain Foundation Da CORET Sun Horasda Mata Harkar Kiwo Da Sarrafa Madara A Kaduna"},"content":{"rendered":"<p style=\"text-align: left;\">Gidauniyar Inganta Madara (Milk Value Chain Foundation) tare da ha\u0257in gwiwar Kungiyar Hadin Kan Masu Kiwon Gargajiya ta Africa, wato CORET, sun shirya taron karawa juna sani domin inganta harkar kiwo da samar da isasshen madara a Najeriya, tare da bai wa matasa da mata damar dogaro da kai.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Taron wanda ya gudana a garin Kaduna, ya mayar da hankali kan horar da mahalarta kan sabbin hanyoyin kiwon dabbobi, dabarun samar da ciyarwa, da kuma yadda za su inganta sarrafa madara domin samun ci gaba mai \u0257orewa.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Shirin ya samu goyon bayan \u0199ungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, ECOWAS, da kuma tallafin ku\u0257i daga gwamnatin Swiss Cooperation.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Gudanarwan CORET, Dr. Abdu Umar Hardo, ya bayyana cewa wannan shiri yana da nufin sauya tsarin kiwon gargajiya zuwa na zamani, tare da samar da damammakin tattalin arziki ga matasa da mata musamman a cikin al\u2019ummomin makiyaya.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Dr. Ardo ya ce aiwatar da wannan shiri da gaske zai taimaka wajen rage zaman kashe wando da matsalar rashin aikin yi, ba kawai a Jihar Kaduna ba har ma da Najeriya baki \u0257aya.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Haka zalika, wakilar gidauniyar Milk Value Chain Foundation, Dr. Bilkisu Yusuf, ta yaba da hadin gwiwar, tare da jaddada muhimmancin amfani da ilimin da mahalarta suka samu domin amfanar al\u2019ummarsu.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">A kasidarsa mai taken \u201cInganta Halittar Dabbobi Don Kara Yawan Madara a Najeriya\u201d, Dr. Sabo Mohammed Abubakar ya bukaci gwamnati a matakai daban-daban da ta zuba jari a fannin kiwo da samar da ciyawa mai inganci domin bunkasa tattalin arzikin kasa.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Wani jami\u2019i daga Hukumar Bada Ilimin Makiyaya ta Kasa, Alhaji Abubakar Lawal Boro, ya bayyana taron a matsayin muhimmin ci gaba wanda zai zama madogara ga makiyaya, tare da fatan shirin zai ci gaba da gudana don tallafa musu da kuma \u0199arfafa tattalin arzikin \u0199asa.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Shugaban al\u2019umma na Ladugga, Madakin Ladugga, Alhaji Salihu Yunusa, ya bayyana jin da\u0257insa da yadda mambobinsa suka amfana da horon, musamman wajen fahimtar yadda za su inganta hanyoyin tara da sayar da madara.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Daga cikin masu gabatar da kasidu akwai Malam Attahiru Alhassan Jaoji daga Jami\u2019ar Ahmadu Bello Zaria, wanda ya gabatar da makala kan \u201cManufofi da Tsokaci Kan Shirin Sarrafa Madara a Yammacin Afirka,\u201d da kuma Jonathan Jatau wanda ya yi bayani kan dabarun bunkasa yawan madara ta hanyar inganta halittar dabbobi.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Mahalarta taron sun fito ne daga yankunan Damau, Ladugga da Luma Kwasam, dukkansu daga cikin Jihar Kaduna.<\/p>\n<p>Cov: Adamu Yusuf<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gidauniyar Inganta Madara (Milk Value Chain Foundation) tare da ha\u0257in gwiwar Kungiyar Hadin Kan Masu Kiwon Gargajiya ta Africa, wato CORET, sun shirya taron karawa juna sani domin inganta harkar kiwo da samar da isasshen madara a Najeriya, tare da bai wa matasa da mata damar dogaro da kai. Taron wanda ya gudana a garin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":21,"featured_media":4691,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1],"tags":[1237,1026,256,1239,1238,33,1047,1241,234,1235,1240,1236],"class_list":["post-4690","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","tag-chain","tag-coret","tag-foundation","tag-harkar","tag-horasda","tag-kaduna","tag-kiwo","tag-madara","tag-mata","tag-milk","tag-sarrafa","tag-value"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/05\/Screenshot_20250530-172301.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4690","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/21"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4690"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4690\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4694,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4690\/revisions\/4694"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4691"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4690"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4690"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4690"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}