{"id":456,"date":"2024-03-17T17:24:57","date_gmt":"2024-03-17T17:24:57","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=456"},"modified":"2024-03-17T17:24:57","modified_gmt":"2024-03-17T17:24:57","slug":"sudan-ta-kudu-ta-rufe-makarantun-kasar-saboda-tsananin-zafi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/sudan-ta-kudu-ta-rufe-makarantun-kasar-saboda-tsananin-zafi\/","title":{"rendered":"Sudan ta Kudu ta Rufe Makarantun Kasar Saboda Tsananin Zafi"},"content":{"rendered":"<div>\n<div>\n<p>Gwamnatin Kasar Sudan ta Kudu ta sanar da cewa za ta rufe duka makarantun \u0199asar daga ranar Litinin sakamakon tsananin zafin da ake fargabar \u0199asar za ta fusakanta.<\/p>\n<p>Ma\u2019aikatun ilimi da na lafiya sun bayar da shawara ga iyayen yara kan yara su zauna a gida sakamakon ana fargabar zafi a \u0199asar zai kai har maki 45 a ma\u2019aunin Celsius.<\/p>\n<p>Ma\u2019aikatun sun yi garga\u0257i kan cewa duk wata makaranta da aka kama a bu\u0257e za ta fuskanci hukunci wanda hakan zai iya kaiwa ga har a \u0199wace lasisinta.<\/p>\n<p>Duk da cewa ma\u2019aikatun ba su sanar da tsawon lokacin da makarantun za su kasance a rufe ba, amma hasashen yanayi ya nuna cewa za a shafe kusan mako biyu ana fuskantar wannan zafin.<\/p>\n<p>Ma&#8217;aikatun sun ce za su ci gaba da sanya ido kan lamarin tare da sanar da jama&#8217;a yadda ya kamata.<\/p>\n<p>Peter Garang, wani mazaunin Juba babban birnin kasar, ya yi maraba da matakin.<\/p>\n<p>Ya ce \u201cya kamata a saka wutar lantarki a makarantu\u201d domin a samu damar shigar da na\u2019urorin sanyaya \u0257aki.<\/p>\n<p>Sudan ta Kudu wadda tana daga cikin sabbin \u0199asashe a duniya, na fama da matsalar sauyin yanayi tare da tsananin zafi na gama gari amma ba kasafai yake kai maki 40 ba a ma\u2019aunin Celcius.<\/p>\n<p>Rikicin cikin gida dai ya addabi kasar da ke gabashin Afirka wadda ita ma take fama da fari da ambaliyar ruwa, lamarin da ya jefa mazauna kasar cikin wahala.<\/p>\n<\/div>\n<\/div>\n<div>\n<div class=\"article-source\">AP<\/div>\n<\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Kasar Sudan ta Kudu ta sanar da cewa za ta rufe duka makarantun \u0199asar daga ranar Litinin sakamakon tsananin zafin da ake fargabar \u0199asar za ta fusakanta. Ma\u2019aikatun ilimi da na lafiya sun bayar da shawara ga iyayen yara kan yara su zauna a gida sakamakon ana fargabar zafi a \u0199asar zai kai har [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":18,"featured_media":457,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,12],"tags":[152,155,154,151,153],"class_list":["post-456","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-ketare","tag-kudu","tag-makarantu","tag-rufe","tag-sudan","tag-zafin-yanayi"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/Sudan-ta-Kudu.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/456","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/18"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=456"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/456\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":458,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/456\/revisions\/458"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/457"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=456"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=456"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=456"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}