{"id":4539,"date":"2025-05-20T08:54:17","date_gmt":"2025-05-20T08:54:17","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=4539"},"modified":"2025-05-20T08:54:17","modified_gmt":"2025-05-20T08:54:17","slug":"dalibai-makarantun-sakandare-a-kwara-sun-kar%c9%93i-tallafin-karatu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/dalibai-makarantun-sakandare-a-kwara-sun-kar%c9%93i-tallafin-karatu\/","title":{"rendered":"Dalibai Makarantun Sakandare A Kwara Sun Kar\u0253i Tallafin Karatu"},"content":{"rendered":"<p>Akalla dalibai marasa galihu 300 da ke makarantun gaba da sakandare daga zababbun al\u2019ummomi a kananan hukumomin Edu\/Patigi\/Moro na jihar Kwara sun samu tallafin karatu don tallafa musu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da yake jawabi a wajen taron rabon tallafin karatu da aka gudanar a Ilorin, mai taken \u201cHatsarori na Shaye-shayen Miyagun Kwayoyi Tsakanin Dalibai A Manyan Makarantu\u201d wanda Michael Imoudu tare da hadin gwiwar mamba mai wakiltar mazabar Edu\/Moro\/Patigi na Jihar Kwara, Ahmad Adamu -Saba ya shirya, ya ce za a yi rabon ne kashi biyu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Dan majalisar wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa, Muhammed Salihu, ya ce manufar shirin bayar da tallafin shi ne tallafawa daliban da iyayensu ba za su iya biyan wasu kudadensu a makaranta ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Saba ya bayyana cewa wasu \u2019yan gata da ke makaranta suma za su iya amfani da kudin wajen siyan littattafansu ko biyan kudin hayar gidansu .<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya shawarci daliban da su tabbatar sun yi amfani da naira dubu dari da ake baiwa kowannen su domin manufar da aka sa a gaba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Saba ta bukace su da su guji shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran munanan dabi\u2019u domin samun ingantacciyar rayuwa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nasa jawabin mukaddashin Darakta Janar Michael Imoudu National Institute For Labour Studies (MINILS), Fasto Ezekiel Ayorinde, wanda babban jami\u2019in kula da harkokin kasuwanci na Cibiyar, Hassan Surajudeen ya wakilta, ya ce an raba tallafin ne da nufin inganta ilimin daliban.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma shawarce su da su sanya kudin cikin hikima wajen neman ilimi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A jawabansu daban daban wasu shugabannin al\u2019umma a kananan hukumomin Moro\/Edu\/Patigi, Muhammed Aliyu Labas da Mohammed Baba (Shonga) sun yabawa mai gudanar da wannan karimcin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sun bukaci wadanda suka ci gajiyar kudin da su tabbatar sun yi amfani da kudin don manufar da ake son yi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cikin laccar sa mai taken \u201cHadarin Shaye-shayen Miyagun Kwayoyi A Tsakanin Dalibai A Manyan Makarantu\u201d Babban Malamin, Abdullahi Galadima ya ce daga bayanan da ake da su matasa na da dabi\u2019ar shiga shaye-shayen miyagun kwayoyi saboda matsin lamba na tsarawa da dai sauransu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya shawarci matasa da su guji shaye-shayen miyagun kwayoyi, su kuma yi karatun ta natsu domin kyautata rayuwarsu<\/p>\n<p>COV\/ALI MUHAMMAD RABIU<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Akalla dalibai marasa galihu 300 da ke makarantun gaba da sakandare daga zababbun al\u2019ummomi a kananan hukumomin Edu\/Patigi\/Moro na jihar Kwara sun samu tallafin karatu don tallafa musu. &nbsp; Da yake jawabi a wajen taron rabon tallafin karatu da aka gudanar a Ilorin, mai taken \u201cHatsarori na Shaye-shayen Miyagun Kwayoyi Tsakanin Dalibai A Manyan Makarantu\u201d [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":4540,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[7,3,5,1,11],"tags":[643,67],"class_list":["post-4539","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-fasaha","category-ilimi","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","tag-ilorin","tag-karatu"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/05\/3d83e065-6dbe-44d0-88d0-02897460b40e.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4539","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4539"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4539\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4541,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4539\/revisions\/4541"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4540"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4539"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4539"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4539"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}