{"id":449,"date":"2024-03-14T17:27:22","date_gmt":"2024-03-14T17:27:22","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=449"},"modified":"2024-03-14T17:27:24","modified_gmt":"2024-03-14T17:27:24","slug":"gwamnatin-jigawa-za-ta-kafa-cibiyoyin-bada-abincin-buda-baki-a-manyan-makarantu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-jigawa-za-ta-kafa-cibiyoyin-bada-abincin-buda-baki-a-manyan-makarantu\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Jigawa Za Ta Kafa Cibiyoyin Bada Abincin Buda Baki A Manyan Makarantu"},"content":{"rendered":"\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Gwamnatin Jihar Jigawa  za ta kafa cibiyoyin bada abincin buda baki a manyan makarantun jihar guda 10, domin tallafa wa dalibai a lokacin azumi.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al\u2019adu na jihar Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai sakamakon taron majalisar zartaswar jihar da aka gudanar a gidan gwamnati na Dutse.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">A cewarsa, gwamnatin jihar na shirin ciyar da mutane sama da miliyan uku da dubu dari takwas a watan Ramadan na bana domin tallafawa gajiyayyu da marasa galihu.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Alhaji Sagir Musa Ahmed ya yi nuni da cewa, gwamnatin jihar ta amince da  naira kusan miliyan dubu dari uku domin ciyar a watan Ramadan a cibiyoyi 609 da aka kafa a fadin jihar.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Ya ce shirin tallafin da aka tsara ya yi daidai da manufofin gwamnati na  rage wahalhalu ga marasa galihu musamman a wannan lokaci na da ake ciki.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Kwamishinan ya kara da cewa, majalisar ta kuma amince da kafa kwamitin wucin gadi a dukkanin kananan hukumomi 27, wanda kwamishinan kananan hukumomi ko kuma manyan mashawarta na musamman a kananan hukumomin za su jagoranta  domin tabbatar da gaskiya.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Sagir Musa ya ce, sauran mambobin kwamitin sun hada da \u2018yan majalisar dokokin jihar, mataimaka na musamman, shugabannin kananan hukumomi  da DPO na \u2018yan sanda.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><br>Sauran sun hada da jami\u2019in tsaro na DSS na karamar hukumar, wakilin hakimai, da sakataren karamar hukuma wanda zai zama sakataren kwamitin.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\">Hakazalika majalisar ta kuma amince da sama da Naira Biliyan daya da miliyan 125 don \u0199arin siyan kayan abinci da za a raba ga marasa galihu, a \u0199o\u0199arin da ake yi na rage wahalhalun rayuwa.<\/p>\n\n\n\n<p class=\"wp-block-paragraph\"><em><strong>Usman Muhammad Zaria<\/strong><\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Jigawa za ta kafa cibiyoyin bada abincin buda baki a manyan makarantun jihar guda 10, domin tallafa wa dalibai a lokacin azumi. Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al\u2019adu na jihar Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai sakamakon taron majalisar zartaswar jihar da aka [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":450,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11],"tags":[150,149],"class_list":["post-449","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","tag-cibiyoyin-buda-baki-a-manyan-makarantu","tag-gwamnatin-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/1679249049167.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/449","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=449"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/449\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":451,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/449\/revisions\/451"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/450"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=449"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=449"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=449"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}