{"id":4281,"date":"2025-05-04T08:58:37","date_gmt":"2025-05-04T08:58:37","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=4281"},"modified":"2025-05-04T08:58:37","modified_gmt":"2025-05-04T08:58:37","slug":"an-share-filin-noma-kadada-100-don-karfafa-matasa-su-yi-noma-a-babura-jihar-jigawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/an-share-filin-noma-kadada-100-don-karfafa-matasa-su-yi-noma-a-babura-jihar-jigawa\/","title":{"rendered":"An Share Filin Noma Kadada 100 Don Karfafa Matasa Su Yi Noma A Babura Jihar Jigawa"},"content":{"rendered":"<p>Shugaban karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa, Malam Hamisu Muhammad Garu, ya kaddamar da shirin karfafa aikin gona da nufin sanya matasa aikin noman shinkafa a wani bangare na kokarin inganta ayyukan yi da samar da abinci a yankin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da aikin aka gudanar a garin Babura, shugaban ya bayyana cewa, Gwamna Malam Umar Namadi ne ya bullo da shirin a matsayin wani muhimmin mataki na samar da guraben ayyukan yi ga matasa, da habaka tattalin arzikin kananan hukumomi, da karfafa samar da abinci a fadin jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cewarsa, gwamnatin jihar ta samar da muhimman kayayyakin amfanin gona da suka hada da takin zamani, magungunan kashe kwari, irin shinkafa mai yawan gaske, da injinan feshi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Malam Hamisu Garu ya yi nuni da cewa, za a raba kayayyakin ga matasa 200 da aka zabo daga sassa daban-daban na karamar hukumar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kara da cewa, karamar hukumar ta ware tare da share fili mai fadin hekta 100 domin fara aikin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban ya nuna jin dadinsa ga gwamnatin jihar da ta fara shirin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce, shirin zai hana matasa yin kaura zuwa birane domin neman ayyukan yi, lamarin da yakan jefa su cikin hatsari da kuma gurgunta makomarsu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nasa jawabin, babban daraktan cibiyar bincike ta jiha Dakta Suleman Rufa\u2019i, ya bayyana shirin a matsayin wani kokari na farko, inda ya kara da cewa akwai shirye-shiryen kara fadada shi bisa burin gwamnati na mayar da jihar Jigawa a matsayin jihar da ke kan gaba wajen samar da abinci a Nijeriya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Rediyon Nijeriya ya ruwaito cewa, sarakunan gargajiya da suka halarci taron sun hada da Hakimin Babura, Sarkin Ban Ringim, Alhaji Muhammad Nata\u2019ala Mustapha, da Hakimin Garu, Dan-makwayon Ringim, Alhaji Suhailu Abubakar Usman, sun yabawa gwamnati kan wannan shiri.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugabannin sun bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin su nuna kishin kasa da alhaki ta hanyar amfani da tallafin yadda ya kamata domin tabbatar da nasarar shirin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>USMAN MZ\/Dutse<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa, Malam Hamisu Muhammad Garu, ya kaddamar da shirin karfafa aikin gona da nufin sanya matasa aikin noman shinkafa a wani bangare na kokarin inganta ayyukan yi da samar da abinci a yankin. &nbsp; Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da aikin aka gudanar a garin Babura, shugaban ya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":4282,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,11,10],"tags":[846,59],"class_list":["post-4281","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","category-noma","tag-babura","tag-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/05\/804f3623-d37e-43bf-9de4-ad770bfbe41f.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4281","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4281"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4281\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4283,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4281\/revisions\/4283"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4282"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4281"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4281"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4281"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}