{"id":4220,"date":"2025-04-30T13:22:10","date_gmt":"2025-04-30T13:22:10","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=4220"},"modified":"2025-04-30T13:26:20","modified_gmt":"2025-04-30T13:26:20","slug":"hajj-2025-kaduna-ta-gaddamar-da-ayarin-likitoci-da-za-su-kula-da-alhazan-jihar","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/hajj-2025-kaduna-ta-gaddamar-da-ayarin-likitoci-da-za-su-kula-da-alhazan-jihar\/","title":{"rendered":"Hajj 2025: Kaduna Ta Kaddamar Da Ayarin Likitoci Da Za Su Kula Da Alhazan Jihar"},"content":{"rendered":"<p>Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya kaddamar da ayarin likitoci su tara domin kula da lafiyar maniyata aikin hajjin na wannan shekaran.<\/p>\n<p>Shugaban Hukumar Jin Da\u0257in Alhazan Jihar Kaduna, Malam Salihu S. Abubakar, ne ya bayyana hakan bayan ganawar farko da ayarin da kuma shugabannin hukumar.<\/p>\n<p>Ayarin likitocin \u0199ar\u0199ashin jagorancin Dr. Bello Jamoh, za su gudanar da cikakken binciken lafiyar maniyata kafin tafiyar su zuwa kasa mai tsarki da zai gudana a sansanin alhazai da ke Mando, Kaduna.<\/p>\n<p>Sannan kuma za su bayar da taimakon gaggawa a kasar Saudiyya tare da ha\u0257in gwiwar Ayarin likitocin daga Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON).<\/p>\n<p>Shugaban hukumar ya ce mambobin ayarin za su kasance cikin tsari na duba lafiyar mahajjata a tsawon lokacin aikin hajjin.<\/p>\n<p>&#8220;<em>Lafiya maniyata aikin hajjin tana da matu\u0199ar muhimmanci, mun za\u0253i ayarin ne bisa \u0199warewarsu, kuma muna da tabbacin za su bayar da ingantaccen kulawa ta lafiya a lokacin aikin hajjin<\/em>,&#8221; In ji shi.<\/p>\n<p>Shugaban ya \u0199ara da cewa za a gudanar da cikakken gwajin lafiya ga dukkan masu niyyar zuwa aikin Hajj, musamman don gano mata masu juna biyu.<\/p>\n<p>&#8220;<strong><em>Babu sassauci ko ka\u0257an wajen barin mata masu juna biyu su tafi Hajj.<\/em><\/strong>&#8221; in ji Malam Salihu, yana mai jaddada cewa gudunmuwar da ayarin likitocin za su bada wajen tabbatar da wannan doka, na da muhimmanci don bin \u0199a\u2019idodin aikin Hajjin.<\/p>\n<p>Ya ja hankalin ayarin likitocin su gudanar da aikinsu cikin \u0199warewa da sadaukarwa, domin tabbatar da cewa mahajjata sun samu aikin hajji mai sau\u0199i cikin koshin lafiya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Adamu Yusuf<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya kaddamar da ayarin likitoci su tara domin kula da lafiyar maniyata aikin hajjin na wannan shekaran. Shugaban Hukumar Jin Da\u0257in Alhazan Jihar Kaduna, Malam Salihu S. Abubakar, ne ya bayyana hakan bayan ganawar farko da ayarin da kuma shugabannin hukumar. Ayarin likitocin \u0199ar\u0199ashin jagorancin Dr. Bello Jamoh, za [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":611,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[294,33],"class_list":["post-4220","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-hajj","tag-kaduna"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/hajj2023-750x375-1.png","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4220","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4220"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4220\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4223,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4220\/revisions\/4223"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/611"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4220"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4220"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4220"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}