{"id":3947,"date":"2025-04-15T19:52:04","date_gmt":"2025-04-15T19:52:04","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=3947"},"modified":"2025-04-15T19:52:04","modified_gmt":"2025-04-15T19:52:04","slug":"gwamnatin-jigawa-ta-bukaci-jamian-tsaro-mata-su-rika-sanya-hijabi-yayin-aiki","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-jigawa-ta-bukaci-jamian-tsaro-mata-su-rika-sanya-hijabi-yayin-aiki\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Jigawa Ta Bukaci Jami\u2019an Tsaro Mata Su Rika Sanya Hijabi Yayin Aiki"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da amfani da Hijabi ga jami\u2019an tsaro mata a fadin jihar.<\/p>\n<p>Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al\u2019adu, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa da aka gudanar a fadar gwamnatin\u00a0 jihar da ke Dutse.<\/p>\n<p>A cewarsa, majalisar ta bayar da umarni ga kamfanonin tsaro guda uku da ke aiki a jihar, su bai wa jami\u2019an tsaro mata daga cikin matasa 9,969 da aka dauka aiki, damar sanya Hijabi yayin aiki, a matsayin girmamawa ga addini da al\u2019adu.<\/p>\n<p>Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, wannan matsaya ta biyo bayan rahoton da kwamitin majalisar kan tsaron makarantu, asibitoci da kotuna ya gabatar, kuma aka sake jaddada kudurin gwamnatin na tabbatar da tsarin aiki mai cike da mutuntaka, da daidaito.<\/p>\n<p>Ya ce, majalisar zartarwar ta kuma amince da kaddamar da makon kirkira da kere-kere na jihar (JISCIW) daga shekarar 2025.<\/p>\n<p>Ya jaddada cewa, wannan tsari na nuna jajircewar gwamnatin wajen bunkasa basira da hazakar matasa, da kuma inganta kirkire-kirkire da tunani mai zurfi a fadin jihar.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Sagir ya bayyana cewa, JISCIW zai kara zaburar da matasa a fannoni daban-daban kamar fasaha, zane, kasuwanci da kuma harkokin fasaha.<\/p>\n<p>Ya kara da cewa, majalisar ta amince da fitar da sama da Naira miliyan 516 domin sayen tikitin jirgi ga daliban jihar Jigawa 185 da ke karatu a fannin likitanci da kimiyyar kiwon lafiya a Jami\u2019ar Near East dake kasar Cyprus, domin shirye-shiryen zangon karatu na shekarar 2024\/2025.<\/p>\n<p>Kwamishinan ya kara da cewa, wannan tallafi ya nuna yadda gwamnatin ke ci gaba da daukar nauyin ilimi da jin dadin daliban da ke karatu a kasashen waje, musamman a muhimman fannoni kamar likitanci da kiwon lafiya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Usman Muhammad Zaria\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da amfani da Hijabi ga jami\u2019an tsaro mata a fadin jihar. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al\u2019adu, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa da aka gudanar a fadar gwamnatin\u00a0 jihar da ke Dutse. A cewarsa, majalisar ta bayar da umarni [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":3948,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[1117,59],"class_list":["post-3947","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-hijabi","tag-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/04\/IMG-20250412-WA00141.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3947","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3947"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3947\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3949,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3947\/revisions\/3949"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3948"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3947"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3947"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3947"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}