{"id":3928,"date":"2025-04-14T19:50:39","date_gmt":"2025-04-14T19:50:39","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=3928"},"modified":"2025-04-14T19:50:39","modified_gmt":"2025-04-14T19:50:39","slug":"shugaba-tinubu-ya-yi-allah-wadai-da-harin-jihar-filato","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/shugaba-tinubu-ya-yi-allah-wadai-da-harin-jihar-filato\/","title":{"rendered":"Shugaba Tinubu Ya Yi Allah-wadai Da Harin Jihar Filato"},"content":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Tinubu ya bayyana bakin cikinsa kan harin da aka kai\u00a0 Jihar Filato wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 40.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa, Shugaban kasa ya la\u2019anci wannan tashin hankali tare da mika ta\u2019aziyyarsa ga Gwamna Caleb Mutfwang, Gwamnatin Jihar, da al\u2019ummar Filato.<\/p>\n<p>Sanarwar da Mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan Harkokin Yada Labarai Mista Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, ta bukaci Gwamnan da ya nuna cikakken ikonsa wajen warware rikicin da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin soyayya da hadin kai a maimakon\u00a0 bambancin addini da kabila.<\/p>\n<p>Ya bukaci shugabannin al\u2019umma, da na addinai, da ma na siyasa a ciki da wajen jihar, da su hada kai domin kawo karshen ramuwar gayya da rikice-rikicen da suka jima suna addabar al\u2019umma.<\/p>\n<p>\u201c<em>Ya zaman wajibi a kawo karshen rikicin da ke faruwa tsakanin al\u2019umma a Jihar Filato wanda ya samo asali daga rashin fahimta tsakanin kabilu da addinai daban-daban.<\/em>\u201d In ji Shugaba Tinubu.<\/p>\n<p>\u201c<em>Na umarci hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan wannan rikici, da gano wadanda ke da hannu a shirya wadannan ayyukan tashin hankali. Ba za mu amince da wannan barna da hare-haren ramuwar gayya ba. Ya isa haka.<\/em><\/p>\n<p>Ya ce Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da ba Gwamna Mutfwang da Gwamnatin Jihar Filato goyon baya wajen karfafa tattaunawa, inganta zaman tare, da tabbatar da adalci don magance wannan rikici har abada.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Bello Wakili<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Tinubu ya bayyana bakin cikinsa kan harin da aka kai\u00a0 Jihar Filato wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 40. A cikin wata sanarwa, Shugaban kasa ya la\u2019anci wannan tashin hankali tare da mika ta\u2019aziyyarsa ga Gwamna Caleb Mutfwang, Gwamnatin Jihar, da al\u2019ummar Filato. Sanarwar da Mai ba Shugaban Kasa shawara na [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":482,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[1114,89],"class_list":["post-3928","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-filato","tag-tinubu"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/Tinubu-ECOWAS.webp","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3928","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3928"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3928\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3929,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3928\/revisions\/3929"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/482"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3928"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3928"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3928"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}