{"id":388,"date":"2024-03-11T08:55:50","date_gmt":"2024-03-11T08:55:50","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=388"},"modified":"2024-03-11T08:55:50","modified_gmt":"2024-03-11T08:55:50","slug":"yadda-azumin-bana-ya-riski-alummar-musulmi-a-sassan-duniya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/yadda-azumin-bana-ya-riski-alummar-musulmi-a-sassan-duniya\/","title":{"rendered":"Yadda azumin bana ya riski al&#8217;ummar musulmi a sassan duniya"},"content":{"rendered":"<div id=\"attachment_389\" style=\"width: 310px\" class=\"wp-caption alignnone\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" aria-describedby=\"caption-attachment-389\" class=\"size-medium wp-image-389\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/2015-06-21T181552Z_52652242_GF10000135273_RTRMADP_3_RELIGION-RAMADAN_0-300x202.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"202\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/2015-06-21T181552Z_52652242_GF10000135273_RTRMADP_3_RELIGION-RAMADAN_0-300x202.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/2015-06-21T181552Z_52652242_GF10000135273_RTRMADP_3_RELIGION-RAMADAN_0-1024x691.jpg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/2015-06-21T181552Z_52652242_GF10000135273_RTRMADP_3_RELIGION-RAMADAN_0-768x518.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/2015-06-21T181552Z_52652242_GF10000135273_RTRMADP_3_RELIGION-RAMADAN_0-1536x1036.jpg 1536w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/2015-06-21T181552Z_52652242_GF10000135273_RTRMADP_3_RELIGION-RAMADAN_0-2048x1382.jpg 2048w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><p id=\"caption-attachment-389\" class=\"wp-caption-text\">Muslims wait to have their Iftar meal during the month of Ramadan at Al-Rajhi mosque in Riyadh June 21, 2015. REUTERS\/Faisal Al Nasser<\/p><\/div>\n<p>Ba kamar yadda aka saba\u00a0 a baya ba, a bana an ga watan na Ramadan akan lokaci a kusan dukannin kasashen duniya, lamarin da ke tabbatar da yau Litinin matsayin daya ga watan na Ramadan.<\/p>\n<p>Azumin na bana ya riski al\u2019ummar musulmi kusan biliyan 2 a fadin duniya a yanayi daban-daban da ya shafi matsin tattalin arziki, tsadar rayuwa da kuma yake-yake.<\/p>\n<p><strong>Yadda Azumin ya riski \u2018yan Africa<\/strong><\/p>\n<p>A kasashe irin su Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi da ke yammacin Africa jama\u2019a sun fara azumin cikin karuwar rashin tsaro, matsanancin talauci, sauyin yanayi da kuma tsadar rayuwa da ke walagigi da mutanen su.<\/p>\n<p>Kasashen da ke cikin na kan gaba masu yawan al\u2019ummar musulmi a nahiyar Africa na fatan gwamnatoci zasu yi ruwa da tsaki wajen kawo karshen wadannan matsaloli.<\/p>\n<p>A yankin gabashin Africa ma kusan haka abin yake, inda azumin ya riski kasashe irin su Kenya, Uganda da Rwanda cikin mastin tattalin arziki da tsadar rayuwa, su kuwa al\u2019ummar jamhuriyar dimokradiyyar Congo sun marabci azumin cikin fargabar yaki da tashin hankali da kuma hare-haren M23 da sauran kungiyoyin masu rike da makamai.<\/p>\n<p>Duk da kiraye-kirayen kasashen duniya, amma har yanzu babu wata tartibiyar yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin bangarorin da ke rikici a Sudan mai yawan al\u2019ummar musulmi, lamari da ba shakka zai kara tsananta azumin ga jama\u2019ar su.<\/p>\n<p>Masar, Habasha da Somalia suma dai duk babu wani sauyi game da rikive-rikice tsakanin \u2018yan tawaye da dakarun gwamnati da kuma tsananin talauci da ke addabar \u2018yan kasar.<\/p>\n<div class=\"m-em-image\">\n<figure class=\"m-figure m-figure--original\"><picture><source srcset=\"https:\/\/s.rfi.fr\/media\/display\/1341e0b8-d797-11ec-810a-005056bf30b7\/Islam%20en%20Inde%203.webp 0\" type=\"image\/webp\" sizes=\"\" \/><\/picture><\/figure>\n<p><strong>Yadda Azumin ya riski gabas ta tsakiya<\/strong><\/p>\n<p>Duk da yadda wannan yanki na duniya yayi kaurin suna wajen rashin zaman lafiya, amma jama\u2019a sun jima basu fara azumi ciki fargaba da rashin tabbas irin na bana ba, wannan kuwa ya faru ne saboda ruwan wutar da Isra\u2019ila da shafe wattani biyar tana yi a Gaza, da kuma martani ta hanyar kai hari da mayakan Houthi na Lebanon ke kaiwa jiragen ruwan kasashe da ke yunkurin shigar da kaya Isra\u2019ila ta kan tekun Maliya, yayin da wannan yaki ke barzanar fantsama zuwa sauran kasashe makwafta.<\/p>\n<p>Ko a tattaunawar da aka zauna juma\u2019ar da ta gabata tsakanin Hamas da Isra\u2019ila an tashi ne baram-baram ba tare da cimma wata yarjejeniyar tsagaita wuta saboda\u00a0 Ramadan din ba.<\/p>\n<p>Isra\u2019ila ta sha alwashin ci gaba da bar\u00edn wuta, ba tare da la\u2019akari da masu azumin ba, har sai Hamas ta bi dukannin ka\u2019idojin da ta gidaya mata, dokokin da Hamas ta yi fatali da su.<\/p>\n<p>Kasashe a wannan yanki na ci gaba da zaman doya da manja, ganin yadda aka ki fitowa kiri-kiri a nuna goyon baya ko akasin haka ko kuma kira ga Isra\u2019ila da tsagaita wuta.<\/p>\n<p><strong>Yaya aka fara azumi a Turai<\/strong><\/p>\n<p>Turawan yammacin duniya ma ba\u2019a bar su a baya ba wajen fara azumin na bana ba duk kuwa da fargabar rashin ingantaccen tsaro a kasashe irin su Faransa da Amurka, yayin da ake fama da matsin tattalin arziki a Burtaniya da makwaftanta sai kuma tsadar rayuwa da Belgium da Jamus da sauran su.<\/p>\n<p><strong>Azumin bana a yankin Asia<\/strong><\/p>\n<p>Yankin Asia da ya kunshi kasashe irin su China, Japan, Koriya da sauran su a iya cewa azumin na bana ya riski jama\u2019a da sauki-saukin rayuwa, idan an kwatanta da sauran sassan duniya, duk da rikicin kan iyaka da ke tashi lokaci-lokaci tsakanin China da Taiwan, sai kuma gwaje-gwajen muggan makamai da Koriya ta arewa ke yi sa\u2019i da lokaci.<\/p>\n<p>Akwai dama-dama a fannin tsadar abinci da kuma karfin tattalin arziki, yayin da ake da zaman lafiya mai inganci idan aka kwatanta da sauran sassan duniya.<\/p>\n<p>Bisa al\u2019ada dai al\u2019ummar musulmi kan kwashe tsahon kwanaki 29 ko kuma 30 suna azumtar watan na Ramadan da ke da matukar muhimanci a gare\u00a0 su, yayin da yake cikin manyan ginshikan da ke rike da adddinin.<\/p>\n<div id=\"attachment_390\" style=\"width: 310px\" class=\"wp-caption alignnone\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" aria-describedby=\"caption-attachment-390\" class=\"size-medium wp-image-390\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/Islam-en-Inde-3-300x200.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"200\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/Islam-en-Inde-3-300x200.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/Islam-en-Inde-3-1024x683.jpg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/Islam-en-Inde-3-768x512.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/Islam-en-Inde-3-1536x1024.jpg 1536w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/Islam-en-Inde-3-2048x1365.jpg 2048w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><p id=\"caption-attachment-390\" class=\"wp-caption-text\">Muslim devotees offer a special morning prayer to start the Eid al-Fitr festival, which marks the end of their holy fasting month of Ramadan, at the Jama Masjid mosque in the old quarters of New Delhi on May 3, 2022. (Photo by Jewel SAMAD \/ AFP)<\/p><\/div>\n<\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ba kamar yadda aka saba\u00a0 a baya ba, a bana an ga watan na Ramadan akan lokaci a kusan dukannin kasashen duniya, lamarin da ke tabbatar da yau Litinin matsayin daya ga watan na Ramadan. Azumin na bana ya riski al\u2019ummar musulmi kusan biliyan 2 a fadin duniya a yanayi daban-daban da ya shafi matsin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":389,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,12],"tags":[],"class_list":["post-388","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-labaran-ketare"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/2015-06-21T181552Z_52652242_GF10000135273_RTRMADP_3_RELIGION-RAMADAN_0.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/388","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=388"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/388\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":391,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/388\/revisions\/391"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/389"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=388"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=388"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=388"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}