{"id":385,"date":"2024-03-11T08:39:53","date_gmt":"2024-03-11T08:39:53","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=385"},"modified":"2024-03-11T08:39:53","modified_gmt":"2024-03-11T08:39:53","slug":"ku-karanta-jerin-kamen-da-hukumar-ndlea-ta-yi-a-farkon-watan-maris","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/ku-karanta-jerin-kamen-da-hukumar-ndlea-ta-yi-a-farkon-watan-maris\/","title":{"rendered":"Ku Karanta Jerin Kamen Da Hukumar NDLEA Ta Yi A Farkon Watan Maris"},"content":{"rendered":"<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-386\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/NDLEA-Buba-Marwa-300x168.webp\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"168\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/NDLEA-Buba-Marwa-300x168.webp 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/NDLEA-Buba-Marwa.webp 750w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Jami\u2019an Hukumar Ya\u0199i da Sha da Fataucin Miyagun \u0198wayoyi ta Kasa NDLEA reshen Jihar Borno, sun kama wasu dattawa biyu kan zargin safarar miyagun \u0199wayoyi.<\/p>\n<p>Hukumar ta bayyana cewa, daga cikin ababen zargin da suka shiga hannu akwai dattijo mai shekara 70 da kuma mai shekara 65.<\/p>\n<p>Femi Babafemi, Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na NDLEA ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.<\/p>\n<p>Ya ce, an kama wadanda ake zargin ne ranar Asabar 9 ga watan Maris tare da wa\u0257anau matasa biyu \u2014 mai shekaru 24 da kuma mai shekaru 28 \u2014 a Maiduguri da Gamboru-Ngala.<\/p>\n<p>A ranar Asabar \u0257in kuma, jami\u2019an NDLEA a Karamar Hukumar Geidam da ke Jihar Yobe, sun tare wata mota kirar Golf 3 da ke kan hanyar zuwa Gagamari a Jamhuriyar Nijar, inda aka kama wani matashi mai shekaru 28 zai kai tabar wiwi mai nauyin kilogiram 24.5 ga wani dila.<\/p>\n<p>Hakazalika, hukumar ta ce a ranar Talata 5 ga watan Maris, ta kwace kwali 42 mai \u0257auke da kwalabe 8,400 na maganin mura mai sa maye, da ke da nauyin kilogiram 1,260 a hannun wani direba mai shekaru 29 a hanyar Katsina.<\/p>\n<p>Kakakin hukumar ya bayyana cewa, sun yi nasarar damke wani dilan haramtattun \u0199wayoyin da ya \u0253oye kayan mayen a injin wata motar bas.<\/p>\n<p>Ya ce \u201cSun kama wani da wiwi da ta kai kilo 5 a cikin injin motar bas mai lamba VDY 187 XA ranar Alhamis, 7 ga Maris 2024, a kan titin Gbongan-Ibadan da ke Jihar Osun bayan jami\u2019anmu sun tsananta bincike.\u201d<\/p>\n<div class=\"google-auto-placed ap_container\"><ins class=\"adsbygoogle adsbygoogle-noablate\" data-ad-format=\"auto\" data-ad-client=\"ca-pub-7943548946436796\" data-adsbygoogle-status=\"done\" data-ad-status=\"unfilled\"><\/p>\n<div id=\"aswift_2_host\" tabindex=\"0\" title=\"Advertisement\" aria-label=\"Advertisement\">Babafemi ya ce \u201ca yanzu haka an kama direban bas \u0257in mai shekaru 35, inda aka bayar da ajiyarsa a gidan gyaran hali gabanin kammala bincike.\u201d<\/div>\n<p><\/ins><\/div>\n<p>A ranar Laraba, 6 ga watan Maris kuma, hukumar ta kama wata mata mai shekaru 26 da ake zargi da sayar da kayan maye.<\/p>\n<p>Babban jami\u2019in na NDLEA ya ce matar ta shiga hannu ne yayin wani samame da jami\u2019ansu suka kai maboyarta a Osogbo, babban birnin Jihar Osun.<\/p>\n<p>A Jihar Kano kuma, an kama wani matashi mai shekaru 35 da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 62 a Gadar Tamburawa, inda shi ma wani mai shekaru 40, ya shiga hannu da kwalaben maganin mura 244.<\/p>\n<div class=\"google-auto-placed ap_container\"><ins class=\"adsbygoogle adsbygoogle-noablate\" data-ad-format=\"auto\" data-ad-client=\"ca-pub-7943548946436796\" data-adsbygoogle-status=\"done\" data-ad-status=\"unfilled\"><\/p>\n<div id=\"aswift_3_host\" tabindex=\"0\" title=\"Advertisement\" aria-label=\"Advertisement\">A ranar Alhamis, 7 ga watan Maris kuma, an kama wani mai shekaru 28, da \u0199wayoyin tramadol guda 49,800 a kan titin Kano-Maiduguri.<\/div>\n<p><\/ins><\/div>\n<p>A kwanakin baya ne Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe, Mai Martaba Sarkin Fika, Dokta Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa, ya bayyana shaye-shayen miyagun \u0199wayoyi a matsayin abin da ke rura wutar rashin tsaro a jihohin Najeriya.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Jami\u2019an Hukumar Ya\u0199i da Sha da Fataucin Miyagun \u0198wayoyi ta Kasa NDLEA reshen Jihar Borno, sun kama wasu dattawa biyu kan zargin safarar miyagun \u0199wayoyi. Hukumar ta bayyana cewa, daga cikin ababen zargin da suka shiga hannu akwai dattijo mai shekara 70 da kuma mai shekara 65. Femi Babafemi, Daraktan yada labarai da bayar da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":386,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,2,9,8],"tags":[23],"class_list":["post-385","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-siyasa","category-tattalin-arziki","category-tsaro","tag-tsaro"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/NDLEA-Buba-Marwa.webp","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/385","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=385"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/385\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":387,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/385\/revisions\/387"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/386"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=385"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=385"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=385"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}