{"id":3810,"date":"2025-04-09T18:41:08","date_gmt":"2025-04-09T18:41:08","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=3810"},"modified":"2025-04-09T18:41:08","modified_gmt":"2025-04-09T18:41:08","slug":"rundunar-yan-sandan-jihar-zamfara-ta-tabbatar-da-harin-yan-bindiga-a-banga","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/rundunar-yan-sandan-jihar-zamfara-ta-tabbatar-da-harin-yan-bindiga-a-banga\/","title":{"rendered":"Rundunar &#8216;Yan Sandan Jihar Zamfara Ta Tabbatar Da Harin &#8216;Yan Bindiga A Banga"},"content":{"rendered":"<p>Rundunar \u2018yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da wani mummunan hari da \u2018yan bindiga suka kai a garin Banga, da ke cikin karamar hukumar Kauran Namoda, inda aka kashe mutane biyu tare da sace wasu da dama.<\/p>\n<p>Jami\u2019in hulda da jama\u2019a na rundunar \u2018yan sanda ta jihar, DSP Yazid Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilinmu da ke Gusau, babban birnin jihar.<\/p>\n<p>DSP Abubakar ya ce bincike na ci gaba da gudana domin gano adadin mutanen da aka sace a harin.<\/p>\n<p>Ya tabbatar da cewa ana kokari don ganin an ceto mutanen da aka sace cikin koshin lafiya.<\/p>\n<p>Yazid ya kara da cewa an kara kaimi wajen daukar matakan tsaro domin hana faruwar irin wannan lamari a nan gaba.<\/p>\n<p>Shaidu sun shaida wa Rediyon Najeriya cewa maharan sun farmaki garin ne da misalin tsakar dare a ranar Laraba, inda suka buda wuta daga wurare da dama, lamarin da ya haifar da firgici ga mazauna garin.<\/p>\n<p>Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa \u2018yan bindigar sun yi ta barna na tsawon sa\u2019o\u2019i, inda suka kashe wani dattijo da wata yarinya \u2018yar shekara 18 mai suna Amina.<\/p>\n<p>Ya ce da farko maharan sun sace kimanin mutane 26, amma ba su samu nasarar guduwa da su baki daya ba, sakamakon hanzarin da jami\u2019an tsaro da \u2018yan sa-kai suka yi.<\/p>\n<p>Wakilinmu ya samu rahoton cewa hadin gwiwar jami\u2019an tsaro da \u2018yan sa-kai ya kai ga kashe wasu daga cikin \u2018yan bindigar, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga. An kuma tabbatar da cewa maharan sun kasa guduwa da shanun da suka sace.<\/p>\n<p>A cewar shaidu, jami\u2019an tsaro da taimakon jiragen saman rundunar sojin saman Najeriya sun toshe hanyar da maharan ke kokarin tserewa ta kusa da kauyen Yamutsawa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><em><strong>Daga Aminu Dalhatu<\/strong><\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Rundunar \u2018yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da wani mummunan hari da \u2018yan bindiga suka kai a garin Banga, da ke cikin karamar hukumar Kauran Namoda, inda aka kashe mutane biyu tare da sace wasu da dama. Jami\u2019in hulda da jama\u2019a na rundunar \u2018yan sanda ta jihar, DSP Yazid Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":950,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[970,115],"class_list":["post-3810","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-hari","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/Bandits.webp","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3810","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3810"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3810\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3812,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3810\/revisions\/3812"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/950"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3810"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3810"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3810"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}