{"id":3754,"date":"2025-04-03T22:00:32","date_gmt":"2025-04-03T22:00:32","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=3754"},"modified":"2025-04-03T22:00:32","modified_gmt":"2025-04-03T22:00:32","slug":"an-nada-shugaban-hukumar-fasahar-sadarwa-da-inganta-tattalin-arziki-ta-jihar-jigawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/an-nada-shugaban-hukumar-fasahar-sadarwa-da-inganta-tattalin-arziki-ta-jihar-jigawa\/","title":{"rendered":"An Nada Shugaban Hukumar Fasahar Sadarwa Da Inganta Tattalin Arziki Ta Jihar Jigawa"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin Dr. Mohammed Hassan a matsayin Darakta Janar na farko na Hukumar Fasahar Sadarwa da inganta Tattalin Arzikin ta fasahar zamani ta Jihar Jigawa.<\/p>\n<p>Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar a Dutse.<\/p>\n<p>Kafin nadin nasa, Dr. Muhammad Hassan shi ne shugaban hukumar Fasahar Sadarwa da Kimiyya ta Jigawa, wato Galaxy ITT.<\/p>\n<p>Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa sabo\u00a0 shugaban hukumar ya sami digirinsa na farko a fannin Lissafi daga Jami&#8217;ar Bayero, Kano, a shekarar 2008. Daga bisani, ya samu digiri na biyu a fannin Kimiyyar Kwamfuta daga Jami&#8217;ar Kimiyya da Fasaha ta Afirka (AUST), Abuja, a shekarar 2011, sannan ya ci gaba da karatu har ya samu digirin digirgir (Ph.D) a fannin Kimiyyar Kwamfuta da Injiniyanci daga Jami&#8217;ar Aizu da ke kasar Japan, a 2018.<\/p>\n<p>Haka nan, Gwamnan ya amince da na\u0257in Baffajo Beita a matsayin sabon shugaban Galaxy ITT.<\/p>\n<p>Kafin na\u0257insa, Beita\u00a0 Babban Jami&#8217;in Bayanan Fasaha ne a Galaxy Backbone da ke Abuja. Yana da \u0199warewa mai zurfi a fannin fasahar sadarwa, musamman a tsarin gudanar da cibiyoyin sadarwa, tsaro na yanar gizo, da \u0199ir\u0199irar fasahar yanar gizo.<\/p>\n<p>Beita ya kammala digirinsa na farko a fannin Kwamfuta daga Jami&#8217;ar Anglia Ruskin, kuma ya fara aikinsa ne a Makarantar Informatics ta Jihar Jigawa da ke Kazaure, kafin ya taka muhimmiyar rawa a manyan ayyukan fasahar sadarwa a Turai, Gabas ta Tsakiya, da Afirka (EMEA) a fannoni daban-daban, ciki har da masana&#8217;antar mai da gas, da sarrafa kayayyaki, da harkokin ku\u0257i&#8221;.<\/p>\n<p>Bugu da \u0199ari, Gwamnan ya amince da na\u0257in Muhammad Nura Zubairu a matsayin Daraktan Zartarwa na Ayyukan Fasaha, da Umar Ibrahim Gumel a matsayin Daraktan Zartarwa na Harkokin Kasuwanci a\u00a0 Galaxy ITT.<\/p>\n<p>Kafin wannan matsayi, Muhammad Nura ya kasance Injiniyan Tallafin Sadarwa a Galaxy ITT, kuma ya kammala babbar difloma (HND) a fannin Tattalin Arzikin Hadin Gwiwa da Gudanarwa daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kano a shekarar 2010.<\/p>\n<p>&#8220;Wadannan muhimman nade-nade na cikin shirye-shiryen Gwamna Namadi na \u0199arfafa tattalin arzikin\u00a0 Jihar Jigawa ta fasahar zamani, domin tabbatar da cewa hukumar na da kwararrun shugabanni da za su jagoranci kirkire-kirkire da inganta ayyukan fasahar sadarwa\u00a0 a ciki da wajen jihar&#8221; in ji SSG.<\/p>\n<p>Malam Bala Ibrahim ya \u0199ara da cewa an za\u0253i wa\u0257anda aka na\u0257a ne bisa cancanta, \u0199warewa, da nagarta.<\/p>\n<p>Ya bukaci dukkan wa\u0257anda aka na\u0257a da su yi aiki tukuru don aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati bisa kyakkyawan.<\/p>\n<p>Sanarwar ta \u0199ara da cewa, dukkan wa\u0257annan nade-naden sun fara aiki ne nan take.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Usman Muhammad Zaria<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin Dr. Mohammed Hassan a matsayin Darakta Janar na farko na Hukumar Fasahar Sadarwa da inganta Tattalin Arzikin ta fasahar zamani ta Jihar Jigawa. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar a Dutse. Kafin nadin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":3755,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[7,1,11],"tags":[1084,59],"class_list":["post-3754","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-fasaha","category-labarai","category-labaran-gida","tag-fasahar-sadarwa","tag-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/04\/IMG-20250403-WA0031.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3754","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3754"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3754\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3756,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3754\/revisions\/3756"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3755"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3754"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3754"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3754"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}