{"id":3748,"date":"2025-04-03T16:08:59","date_gmt":"2025-04-03T16:08:59","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=3748"},"modified":"2025-04-03T16:08:59","modified_gmt":"2025-04-03T16:08:59","slug":"gwamnatin-jigawa-ta-yi-sabbin-nade-nade-a-fannin-ilimi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-jigawa-ta-yi-sabbin-nade-nade-a-fannin-ilimi\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Jigawa Ta Yi Sabbin Nade-nade A Fannin Ilimi"},"content":{"rendered":"<p>Gwamna Umar Namadi ya amince da na\u0257in Dr. Jummai Ali Kazaure a matsayin sabuwar shugabar Kwalejin Ilimi, Shari\u2019a da Nazarin Addinin Musulunci (JSCILS) da ke Ringim.<\/p>\n<p>Wannan na \u0199unshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar.<\/p>\n<p>A cewarsa, kafin wannan na\u0257i, Dr. Jummai ta kasance malama a Kwalejin Ilimi ta Jihar Jigawa da ke Gumel. Tana da digiri na uku (Ph.D.) a fannin Gudanarwa da Tsare-tsare, tare da gogewa a harkar koyarwa daga matakin firamare har zuwa manyan makarantu.<\/p>\n<p>\u201c<em>Dr. Jummai ta rike mukamai da suka gada da Darakta a Makarantar Sakandaren gwamnati ta \u2018yan mata da ke Kazaure da kuma Darakta a Makarantar Sakandare ta larabci da ke Babura. Mace ce mai\u00a0 kishin jasa da son cigaban ilimi da hidima ga al\u2019umma,\u201d<\/em>\u00a0in ji Sakataren Gwamnati.<\/p>\n<p>Haka kuma, Gwamna Namadi ya amince da na\u0257a Hassan Nayaya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Raya Ilimi ta Jihar Jigawa (JERA).<\/p>\n<p>\u201c<em>Kafin wannan mukami, Nayaya ya kasance mukaddashin Shugaban Hukumar. Ya samu digiri a fannin Lissafi daga Jami\u2019ar Bayero da ke Kano a shekarar 2000. Ya fara aiki a ma\u2019aikatar ilimi ta Jihar Jigawa ne tun daga shekarar 1992, har ya kai matsayin Darakta a shekarar 2020<\/em>,\u201d in ji sanarwar.<\/p>\n<p>Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa wa\u0257annan na\u0257e-na\u0257en suna daga cikin kokarin Gwamna na inganta shugabanci a fannin ilimi da ci gaban al\u2019ummar Jihar Jigawa.<\/p>\n<p>Sanarwar ta \u0199ara da cewa, an yi na\u0257in ne bisa cancanta, kwarewa da nagarta.<\/p>\n<p>\u201c<em>Yayin da ake taya sabbin shugabannin murna, ana fatan za su yi aiki tukuru domin ba da gudunmawa ga ci gaban Jihar Jigawa<\/em>.\u201d<\/p>\n<p>Sanarwar ta \u0199ara da cewa dukkan na\u0257e-na\u0257en sun fara aiki nan take.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><em><strong>Usman Muhammad Zaria\u00a0<\/strong><\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamna Umar Namadi ya amince da na\u0257in Dr. Jummai Ali Kazaure a matsayin sabuwar shugabar Kwalejin Ilimi, Shari\u2019a da Nazarin Addinin Musulunci (JSCILS) da ke Ringim. Wannan na \u0199unshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar. A cewarsa, kafin wannan na\u0257i, Dr. Jummai ta kasance malama a [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":3599,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11],"tags":[59,1082],"class_list":["post-3748","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","tag-jigawa","tag-jscils"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Jigawa-State-1.png","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3748","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3748"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3748\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3749,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3748\/revisions\/3749"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3599"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3748"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3748"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3748"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}