{"id":3695,"date":"2025-03-30T16:30:41","date_gmt":"2025-03-30T16:30:41","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=3695"},"modified":"2025-03-30T21:28:00","modified_gmt":"2025-03-30T21:28:00","slug":"an-hori-dagatan-kasar-zazzau-su-sa-ido-akan-bakin-fuskokin-a-yankunan-su","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/an-hori-dagatan-kasar-zazzau-su-sa-ido-akan-bakin-fuskokin-a-yankunan-su\/","title":{"rendered":"An Hori Dagattan Kasar Zazzau Su Sa Ido Akan Bakin Fuskoki A Yankunan Su"},"content":{"rendered":"<p>Mai martaba Sarkin zazzau,kuma shugaban majalisar sarakunan jihar kaduna, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya bukaci Dagatan da ke masarautar zazzau da su rinka sanya ido sosai akan zirga-zirgar bakin fuskokin da ba su gane ba a cikin su.<\/p>\n<p>Ya yi kiran ne a sakon sa na sallah bayan kammala azumin watan Ramadan a fadar sa dake Zaria.<\/p>\n<p>Ahmed Nuhu Bamalli ya bayyana cewa harkar tsaron rayuka da dukiyoyin jama&#8217;a hakki ne na kowa amma ba gwamnati ita kadai ba,a don haka akwai bukatar ganin an hada karfi da karfe domin samun nasara a game da tsaron.<\/p>\n<p>Mai martaba Sarkin ya kuma bukaci Dagatan da su rinka kai rahoton zuwan duk wani bako ko bakuwa da kuma dalilin zuwan.<\/p>\n<p>Ya ce idan har aka dauki wannan matakin matsalar tsaro za ta ragu sosai,yana mai nuni da cewa sarakunan gargajiya na da muhimman rawar da za su taka game da tsaro.<\/p>\n<p>Haka kuma Sarkin na zazzau ya bukaci iyaye da su rinka sanya ido game da harkokin yau da kullum na &#8216;ya&#8217;yan su.<\/p>\n<p>Haka kuma ya gode wa gwamnan jihar kaduna da shugaban majalisar wakilai,Dr Abbas Tajuddeen, Iyan zazzau saboda irin aiyukan ci gaban da suke samar wa talakawa a zaria da sauran kananan hukumomin jihar kaduna.<\/p>\n<p>A wani labarin kuma,Limamin masallacin juma&#8217;a na rukunin kananan gidajen dake kofar Gayan,Zaria, Sheikh Dalhatu Bello Amaru ya yi Allah wadai da kisar Gilla da wasu yan ta&#8217;adda suka yi wa wasu mafarauta yan arewa su 11 a Uromi da ke jihar Edo.<\/p>\n<p>Ya yi Allah wadan ne a hudubar sa ta sallar idin karamar sallah da ya gudanar.<\/p>\n<p>Ya ce mutanen Arewa ba su amince da kisar gillar da aka yi wa maharban ba gaira ba dalili.<\/p>\n<p>Sheikh Bello Amaru ya yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Edo da su tabbatar da ganin an kamo duk mutanen da suka aikata laifin domin suma a kashe su domin ran su bai fi na mafarautar da suka kashe ba tare da wani dalili ba.<\/p>\n<p>Ya yi Bayanin cewa Allah ya bada umurnin cewa duk wanda ya kashe wani shima a kashe shi,amma hakan bai bada damar wani ya dsuki doka a hannun shi ba,hakki ne na hukumomin da abin ya shafa.<\/p>\n<p>Haliru Hamza<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Mai martaba Sarkin zazzau,kuma shugaban majalisar sarakunan jihar kaduna, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya bukaci Dagatan da ke masarautar zazzau da su rinka sanya ido sosai akan zirga-zirgar bakin fuskokin da ba su gane ba a cikin su. Ya yi kiran ne a sakon sa na sallah bayan kammala azumin watan Ramadan a fadar sa [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":3696,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11,6],"tags":[1071,260,765],"class_list":["post-3695","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","category-nishadi","tag-dagatai","tag-sallah","tag-zazzau"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/IMG-20250330-WA0026.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3695","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3695"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3695\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3707,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3695\/revisions\/3707"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3696"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3695"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3695"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3695"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}