{"id":365,"date":"2024-03-09T23:10:49","date_gmt":"2024-03-09T23:10:49","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=365"},"modified":"2024-03-09T23:10:49","modified_gmt":"2024-03-09T23:10:49","slug":"nahcon-ta-bada-kujerar-hajji-ga-wacce-ta-lashe-gasar-karatun-alkurani-ta-duniya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/nahcon-ta-bada-kujerar-hajji-ga-wacce-ta-lashe-gasar-karatun-alkurani-ta-duniya\/","title":{"rendered":"NAHCON Ta Bada Kujerar Hajji Ga Wacce Ta Lashe Gasar Karatun Alkur&#8217;ani Ta Duniya"},"content":{"rendered":"<p>Hukumar Kula da Aikin Hajji\u00a0 ta Kasa NAHCON,\u00a0 ta bai wa Hajara Ibrahim Dan\u2019azumi, wadda ta lashe gasar kur\u2019ani ta duniya\u00a0 da aka kammala a kasar Jordan kujerar aikin Hajjin bana.<\/p>\n<p>Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mataimakiyar daraktan hulda da jama\u2019a na hukumar\u00a0 Fatima Sanda Usara, ta raba wa manema labarai.<\/p>\n<p>Hajiya Fatima Usara ta kara da cewa Shugaban Hukumar,\u00a0 Malam Jalal Ahmad Arabi, ya kuma taya Hajara\u00a0 Dan\u2019azumi murna bisa wannan nasara da ta samu.<\/p>\n<p>An gudanar da gasar tsakanin ranakun 17 zuwa 22 ga Fabrairu 2024, a kasar Jordan.<\/p>\n<p>Ma&#8217;aikatar kula da\u00a0 harkokin addinin musulunci ta\u00a0 kasar Jordan ce ke shirya\u00a0 gasar a duk shekara, wanda wannan shi ne karo na 18.<\/p>\n<p>Hajara Dan\u2019azumi, \u2018yar shekara 19 daga\u00a0 makarantar Abubakar Siddiq Community Islamic School, Gombe,\u00a0 daliba ce kuma a jami\u2019ar jihar Gombe, ta wakilci Najeriya a bangaren Hizfi 60 da Tajwidi. Ta samu kashi 99.5 cikin 100, wanda ya bata damar lashe gasar cikin sauran &#8216;yan takara da suka fito daga\u00a0 \u00a0kasashe 39.<\/p>\n<p>A cikin sakon taya murna ga Gwamnan Jihar Gombe, Mai Girma Alhaji Inuwa Yahaya, Malam Jalal Arabi ya bayyana jin dadinsa da yadda Hajara Ibrahim Dan\u2019azumi ta nuna kwazo.<\/p>\n<p>Shugaban Hukumar NAHCON wanda mataimakinsa Usman Nuraini ya wakilta a wata liyafa ta musamman da gwamnatin jihar ta shirya, ya sanar da baiwa Malama Hajara kyautar kujerar Hajji ta 2024.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A yayin bikin, Gwamna Inuwa Yahaya ya baiwa Hajara kyautar kyautar Naira miliyan biyar. Bugu da kari, gwamnan ya ba ta cikakken tallafin karatu tun daga digiri na farko zuwa na uku, sannan kuma an baiwa makarantar Islamiyyar da\u00a0 Hajara ke karatu kyautar Naira miliyan biyar &#8220;domin inganta ayyukanta da samar\u00a0 da i ingantaccen horar da dalibai&#8221;.<\/p>\n<p>\u201cKarramawar da Shugaban Hukumar NAHCON ya yi wa Hajara ta yi daidai da al\u2019adar sa na tukuicin kwazon aiki da kwazon da ya yi a fadin hukumar. Yakin Malam Arabi ne cewa amincewa da irin wadannan nasarorin zai sa wasu su sake yin irin wannan aikin yayin da suke dauke da wutar da ke aiwatar da kyawawan dabi\u2019u na addinin Musulunci,\u201d inji Hajiya Usara<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hukumar Kula da Aikin Hajji\u00a0 ta Kasa NAHCON,\u00a0 ta bai wa Hajara Ibrahim Dan\u2019azumi, wadda ta lashe gasar kur\u2019ani ta duniya\u00a0 da aka kammala a kasar Jordan kujerar aikin Hajjin bana. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mataimakiyar daraktan hulda da jama\u2019a na hukumar\u00a0 Fatima Sanda Usara, ta raba wa manema labarai. Hajiya Fatima [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":368,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11],"tags":[134,133],"class_list":["post-365","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kyautar-kujerar-hajji-ga-hajara-danazumi","tag-nahcon"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/FB_IMG_1709974691412-780x470-1.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/365","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=365"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/365\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":369,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/365\/revisions\/369"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/368"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=365"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=365"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=365"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}