{"id":3639,"date":"2025-03-27T08:35:28","date_gmt":"2025-03-27T08:35:28","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=3639"},"modified":"2025-03-27T08:35:28","modified_gmt":"2025-03-27T08:35:28","slug":"nlc-a-zamfara-sun-bada-waadin-kwanaki-14-a-aiwatar-da-mafi-karancin-albashi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/nlc-a-zamfara-sun-bada-waadin-kwanaki-14-a-aiwatar-da-mafi-karancin-albashi\/","title":{"rendered":"NLC a Zamfara sun Bada Wa\u2019adin Kwanaki 14 a Aiwatar da Mafi Karancin Albashi"},"content":{"rendered":"<p>Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC a jihar Zamfara sun bayar da wa\u2019adin kwanaki 14 ga gwamnatin jihar, inda suka bukaci da a kawo karshen kura-kuran da aka samu wajen aiwatar da mafi karancin albashi na N70,000.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>An sanar da wa\u2019adin ne a wani taron manema labarai a Gusau bayan wani taron gaggawa da kungiyoyin kwadago suka yi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kungiyar NLC na jihar Zamfara, Malam Sani Halliru, ya bayyana rashin jituwar da ake samu wajen biyan albashin watan Maris a matsayin abin bakin ciki da damuwa ga ma\u2019aikatan gwamnati.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Ya zama dole mu kira wannan taron manema labarai saboda mun ji takaicin yadda gwamnatin jihar ke aiwatar da mafi karancin albashi,&#8221; in ji Halliru.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kara da cewa tun da farko gwamnatin jihar ta kafa kwamitin da zai sa ido a kan yadda za a aiwatar da sabon albashin tare da tabbatar wa ma\u2019aikata cewa za a fara aiki a watan Maris. Sai dai ya lura cewa albashin watan Maris da aka biya a baya-bayan nan ya gaza yadda ake tsammani.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cWasu ma\u2019aikata sun samu karin Naira 3,000 kacal, yayin da wasu suka samu N4,000, N5,000, ko kuma akalla Naira 7,000. Har ma fiye da haka, an cire wasu ma\u2019aikatan ba bisa ka\u2019ida ba daga cikin albashin ma\u2019aikata.\u201d Ya kara da cewa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Malam Sani Haliru ya kuma bayyana lamarin a matsayin cin amana, ya kuma yi gargadin cewa, idan gwamnati ta gaza magance wadannan matsalolin nan da makonni biyu, kungiyoyin za su dauki mataki.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shi ma da yake jawabi, Shugaban TUC, Sa\u2019idu Mudi, ya koka kan yadda har yanzu Zamfara ce jiha daya tilo da ba ta fara aiwatar da mafi karancin albashi na N70,000.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cDukkan shugabannin kwadago da ma\u2019aikata a jihar sun ji takaicin gazawar gwamnati wajen cika alkawarin da ta dauka.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cewar Mudi sun ji takaicin kwamitin da aka nada domin aiwatar da sabon albashin yaki yin aikin da ya dace.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya yi zargin cewa da gangan wasu mutane a cikin gwamnati ke yin zagon kasa wajen aiwatar da aikin tare da yin kira ga Gwamna Dauda Lawal da ya kaddamar da bincike kan lamarin tare da daukar matakin da ya dace.<\/p>\n<p>COV\/AMINU DALHATU<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC a jihar Zamfara sun bayar da wa\u2019adin kwanaki 14 ga gwamnatin jihar, inda suka bukaci da a kawo karshen kura-kuran da aka samu wajen aiwatar da mafi karancin albashi na N70,000. &nbsp; An sanar da wa\u2019adin ne a wani taron manema labarai a Gusau bayan wani taron gaggawa da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":3640,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,2,9],"tags":[448,17,115],"class_list":["post-3639","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-siyasa","category-tattalin-arziki","tag-albashi","tag-nlc","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/e42e81d7-44e4-4054-8575-697e4c7bf32a.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3639","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3639"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3639\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3641,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3639\/revisions\/3641"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3640"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3639"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3639"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3639"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}