{"id":3598,"date":"2025-03-22T09:40:57","date_gmt":"2025-03-22T09:40:57","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=3598"},"modified":"2025-03-22T09:40:57","modified_gmt":"2025-03-22T09:40:57","slug":"gmbni-ta-yi-allah-wadai-da-kisan-gillar-wani-almajiri-a-jihar-jigawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gmbni-ta-yi-allah-wadai-da-kisan-gillar-wani-almajiri-a-jihar-jigawa\/","title":{"rendered":"GMBNI Ta Yi Allah-wadai Da Kisan Gillar Wani Almajiri A Jihar Jigawa"},"content":{"rendered":"<p>Wata kungiya mai suna Grassroots Mobilizers for Better Nigeria Initiative (GMBNI), ta yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa wani\u00a0 Almajiri a \u0199aramar hukumar Gwaram, Jihar Jigawa.<\/p>\n<p>\u0198ungiyar ta bayyana matu\u0199ar bakin ciki da \u0253acin rai game da wannan cin zarafin da aka yi wa yaron, wanda ya kai ga mutuwarsa cikin mawuyacin hali.<\/p>\n<p>A cewar jami\u2019in yankin Arewa maso Yamma na kungiyar ta GMBNI, Abbas Rufa\u2019i Wangara, rahotanni sun nuna cewa wani Malamin makarantar Allo ya yi wa yaron bulala da har ta kai ga mutuwarsa.<\/p>\n<p>Lamarin ya \u0199ara muni\u00a0 inda ake zargin Malamin ya yanke kan gawar\u00a0 yaron, ya cire mazakutarsa gabansa na sirri, sannan ya binne gawar a wani \u0199aramar rami.<\/p>\n<p>GMBNI ta bayyana wannan aika-aika a matsayin cin zarafin \u0257an Adam.<\/p>\n<p>\u0198ungiyar ta mi\u0199a ta\u2019aziyyarta ga iyalan mamacin, tana mai jaddada cewa babu wani yaro da ya kamata ya fuskanci irin wannan zalunci, musamman a wurin da ake koyar da ilimi da tarbiyya.<\/p>\n<p>GMBNI ta nanata bu\u0199atar gaggawar yin gyara a tsarin ilimin Almajiranci, wanda ya da\u0257e yana fama da sakaci, cin zarafi, da rashin kulawa.<\/p>\n<p>Ta yi kira ga hukumomi a dukkan matakai da su \u0257auki matakan da suka dace don kare Almajirai tare da tabbatar da sun sami ingantaccen ilimi cikin kyakkyawar kulawa.<\/p>\n<p>\u0198ungiyar ta kuma bukaci hukumomin tsaro da na shari\u2019a da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin, tare da tabbatar da cewa an hukunta wanda ya aikata wannan danyen aiki ba tare da \u0253ata lokaci ba.<\/p>\n<p>Shugabar GMBNI, Ambasada (Dr.) Fatima Mohammed Goni, ta sake jaddada aniyar \u0199ungiyar na kare ha\u0199\u0199in yaran da ke cikin mawuyacin hali.<\/p>\n<p>Ta yi kira ga \u0199ungiyoyin farar hula, \u2018yan kasa da al\u2019ummar duniya baki \u0257aya da su ha\u0257a kai wajen neman adalci ga mamacin da kuma tashi tsaye wajen tabbatar da\u00a0 adalci da daidaito ga dukkan yara a Najeriya.<\/p>\n<p>Usman Mohammed Zaria<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Wata kungiya mai suna Grassroots Mobilizers for Better Nigeria Initiative (GMBNI), ta yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa wani\u00a0 Almajiri a \u0199aramar hukumar Gwaram, Jihar Jigawa. \u0198ungiyar ta bayyana matu\u0199ar bakin ciki da \u0253acin rai game da wannan cin zarafin da aka yi wa yaron, wanda ya kai ga mutuwarsa cikin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":3599,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[1045,1046,59],"class_list":["post-3598","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-almajiri","tag-gmbni","tag-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Jigawa-State-1.png","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3598","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3598"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3598\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3600,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3598\/revisions\/3600"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3599"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3598"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3598"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3598"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}