{"id":3558,"date":"2025-03-20T08:46:51","date_gmt":"2025-03-20T08:46:51","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=3558"},"modified":"2025-03-20T08:46:51","modified_gmt":"2025-03-20T08:46:51","slug":"masarautun-kano-zasu-gudanar-da-hawan-daba-a-bikin-sallah-karama","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/masarautun-kano-zasu-gudanar-da-hawan-daba-a-bikin-sallah-karama\/","title":{"rendered":"Masarautun Kano Zasu Gudanar da Hawan Daba A Bikin Sallah Karama"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci daukacin masarautun Jihar hudu da su fara shirye-shiryen Bikin Sallah Daba domin ganin jama\u2019a da maziyarta sun ji dadin bukukuwan Sallah.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wannan umarni na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, bayan wani taron buda baki da suka yi da sarakunan gargajiya a dakin taro dake gidan gwamnatin Kano.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cewar sanarwar, gwamna Yusuf ya jaddada cewa al\u2019ummar jihar na zurfafa kallon al\u2019adar sanya sabbin tufafi a ranar Sallah, tare da yin jerin gwano don shaida wa sarakunan su a kan doki, da kuma yin musabaha.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Don haka, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba, kuma ba za ta bari wani makiya su tauye wa \u2018yan kasa wannan hakki da suke da shi ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma tabbatar wa da jama\u2019a cewa dukkanin hukumomin tsaro a jihar za su ba da himma wajen samar da kariya ga jama\u2019a a yayin bikin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamna Yusuf ya kuma bayyana cewa za a kaddamar da Majalisar Masarautar Jihar Kano a watan Afrilun bana domin samun damar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnan ya ci gaba da bayyana cewa za a sanar da ka\u2019idojin majalisar, \u00a0da sauran muhimman abubuwan da suka shafi majalisar a ranar kaddamarwar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya yabawa sarakunan bisa irin balaga da kyakkyawar alaka da suka nuna tun bayan nada su, inda ya ce wannan shi ne karo na farko a tarihin jihar da ake samun kwakkwarar alaka tsakanin sarakunan musamman ta fuskar matsayi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da yake mayar da jawabi, Shugaban Majalisar Masarautar Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya tabbatar da cewa alakar da ke tsakaninsa da sarakunan masu daraja ta biyu abu ne na musamman.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya yi kira ga Gwamna Yusuf da ya yi amfani da cibiyoyin gargajiya don yada manufofi da tsare-tsare yadda ya kamata ga al\u2019umma, tare da tabbatar da aiwatar da su cikin inganci.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nasu bangaren, Sarkin Karaye, Muhammad Muhammad Maharaz; Sarkin Rano, Amb. Muhammad Isa Umaru; da mai martaba Sarkin Gaya Dr. Aliyu Ibrahim Abdulkadir a madadin jama\u2019arsu, sun nuna jin dadinsu ga Gwamna Yusuf bisa samar da takin zamani da samar da ababen more rayuwa a fannonin ilimi, lafiya da hanyoyin sadarwa a yankunansu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci daukacin masarautun Jihar hudu da su fara shirye-shiryen Bikin Sallah Daba domin ganin jama\u2019a da maziyarta sun ji dadin bukukuwan Sallah. &nbsp; Wannan umarni na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, bayan wani taron [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":3560,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[7,3,5,1,11,4,6,2,9],"tags":[576,39,472],"class_list":["post-3558","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-fasaha","category-ilimi","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","category-nishadi","category-siyasa","category-tattalin-arziki","tag-daba","tag-kano","tag-sarakuna"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/41ea2a30-3605-43d3-92ea-5572697a3170.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3558","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3558"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3558\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3561,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3558\/revisions\/3561"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3560"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3558"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3558"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3558"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}