{"id":3525,"date":"2025-03-18T20:39:15","date_gmt":"2025-03-18T20:39:15","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=3525"},"modified":"2025-03-18T20:39:15","modified_gmt":"2025-03-18T20:39:15","slug":"shugaba-tinubu-ya-dakatar-da-gwamnan-jihar-rivers-da-yan-majalisar-dokokin-jihar","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/shugaba-tinubu-ya-dakatar-da-gwamnan-jihar-rivers-da-yan-majalisar-dokokin-jihar\/","title":{"rendered":"Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Gwamnan Jihar Rivers Da &#8216;Yan Majalisar Dokokin Jihar"},"content":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers, inda ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa Ngozi Odu, da dukkan mambobin Majalisar Dokokin Jihar na tsawon watanni shida.<\/p>\n<p>A wani jawabi da ya yi\u00a0 ga alummar kasa ta kafafen yada labarai a ranar Talata, Shugaban kasan ya bayyana cewa an dauki wannan matakin ne sakamakon rikicin siyasa wanda ya ki ci ya ki cinyewa\u00a0 a jihar, ya kuma hana gudanar da gwamnati yadda ya kamata kuma ya tauye wa jama\u2019ar Jihar Rivers morar romon\u00a0 dimokuradiyya.<\/p>\n<p>Shugaban kasan ya nuna damuwarsa kan &#8220;<em>mummunan hali<\/em>&#8221; da jihar ke ciki, wanda ya kara muni bayan rushewar ginin Majalisar Dokokin Jihar da gwamnan ya yi a ranar 13 ga watan Disambar 2023. A cewarsa, duk da kokarin da &#8216;yan Najeriya masu kishin kasa suka yi don samun sulhu, rikicin ya ci gaba da tsananta.<\/p>\n<p>Da yake magana kan hukuncin Kotun Koli na ranar 28 ga Fabrairu, 2025, wanda ya zargi gwamnan da aikata ayyukan da suka sa\u0253a wa kundin tsarin mulki da raina doka, Shugaban kasa ya ce, &#8220;Babu gwamnati a Jihar Rivers, domin bangaren zartarwa ya rushe majalisar dokoki kuma yana mulki tamkar\u00a0 mulkin danniya.&#8221;<\/p>\n<p>Shugaban kasan ya kuma bayyana cewa ya samu rahotannin tsaro da ke nuna barazana ga kadarorin kasa, ciki har da lalata bututun mai da wasu \u2018yan bindiga da ake zargin masu biyayya\u00a0 ga gwamnan ne suka aikata, ba tare da daukar wani mataki\u00a0 don dakile su ba.<\/p>\n<p>Shugaban kasan ya nada tsohon Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Ibokette Ibas (Rtd), a matsayin mai kula da harkokin Jihar Rivers. Ya bayyana cewa bangaren shari\u2019a na jihar zai ci gaba da aiki kamar yadda ya saba, sannan sabon mai kula da jihar zai kasance yana tsara dokoki ne kawai da amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya.<\/p>\n<p>Shugaban kasan ya nuna fatan cewa wannan mataki zai tilasta dukkan bangarorin da abin ya shafa a Jihar Rivers su bi dokokin mulki tare da dawo da zaman lafiya.<\/p>\n<p><strong>Bello Wakili<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers, inda ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa Ngozi Odu, da dukkan mambobin Majalisar Dokokin Jihar na tsawon watanni shida. A wani jawabi da ya yi\u00a0 ga alummar kasa ta kafafen yada labarai a ranar Talata, Shugaban kasan ya bayyana cewa an dauki wannan [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":482,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2,8],"tags":[1028,1027,89],"class_list":["post-3525","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","category-tsaro","tag-dokar-ta-baci","tag-rivers","tag-tinubu"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/Tinubu-ECOWAS.webp","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3525","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3525"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3525\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3526,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3525\/revisions\/3526"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/482"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3525"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3525"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3525"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}