{"id":3503,"date":"2025-03-17T06:37:05","date_gmt":"2025-03-17T06:37:05","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=3503"},"modified":"2025-03-17T06:52:22","modified_gmt":"2025-03-17T06:52:22","slug":"coret-za-ta-samar-da-ayyuka-3000-ga-matasa-a-jihohin-kaduna-da-jigawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/coret-za-ta-samar-da-ayyuka-3000-ga-matasa-a-jihohin-kaduna-da-jigawa\/","title":{"rendered":"CORET Za Ta Samar da Ayyuka 3,000 Ga Matasa A Jihohin Kaduna Da Jigawa"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kungiyar Ha\u0257in Kan Masu Kiwon Gargajiya ta Afrika wato CORET, tare da ha\u0257in gwiwar \u0198ungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ECOWAS, sun bayyana shirinsu na samar da ayyuka guda dubu uku ga matasa ta hanyar sarrafa madara a sarkar darajar madara a Jahohin Kaduna da Jigawa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban Shirin na CORET, Dr. Umar Hardo, ne ya bayyana hakan yayin taron horaswa da \u0199ungiyoyin ha\u0257in kai Sha biyu da aka za\u0253o wanda ya gudanar a yankin Ladduga dake \u0199aramar hukumar Kachia a Jihar Kaduna.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-3504\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Screenshot_20250317-071719-300x297.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"297\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Screenshot_20250317-071719-300x297.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Screenshot_20250317-071719-150x150.jpg 150w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Screenshot_20250317-071719-80x80.jpg 80w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Screenshot_20250317-071719.jpg 720w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Taron horaswar na tsawon kwanaki biyu ya ha\u0257a shugabanni daga \u0199ungiyoyin kiwo na madara guda goma sha biyu, masu tara madara, da shugabannin al&#8217;umma. Wannan shiri da ECOWAS ta \u0257auki nauyi, zai fara aiki gwaje ne a \u0199auyuka biyu, a Ladduga a Jihar Kaduna da kuma Maigatari a Jihar Jigawa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Haka kuma, an samu goyon baya daga Hukumar Ci gaban Kasar Sweden, inda ake aiwatar da aikin ta hanyar ha\u0257in gwiwar wasu \u0199ungiyoyi kamar Hukumar Kula da Makiyaya da kuma da sauran su.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Dr. Umar Hardo ya bayyana cewa taron horaswar na nufin bai wa \u0199ungiyoyin ha\u0257in kai horo da ilimi a duk fannoni na samar da madara domin cigabansu<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;CORET ta riga ta shiga ha\u0257in gwiwa da kamfanoni irin su Milk Copal, Nestl\u00e9 da Farm Fresh. Kuma an gina cibiyoyin tarin madara masu amfani da hasken rana a Ladduga da Maigatari,&#8221; in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Dr. Umar Hardo ya \u0199ara da cewa an tsara horaswar ne akan matasa dari hu\u0257u, amma matasa dari tara da ashirin da uku daga Ladduga suka nuna sha\u2019awar shiga, lamarin da ya nuna yadda matasa ke da sha\u2019awar shiga \u0199ungiyoyin ha\u0257in gwiwa.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-3506\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Screenshot_20250317-071656-228x300.jpg\" alt=\"\" width=\"228\" height=\"300\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Screenshot_20250317-071656-228x300.jpg 228w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Screenshot_20250317-071656.jpg 720w\" sizes=\"auto, (max-width: 228px) 100vw, 228px\" \/><\/p>\n<p>Ya ce daga cikinsu, an za\u0253i matasa dari hu\u0257u daga Maigatari, Jihar Jigawa don samun horo a cikin shirin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;CORET ta sanya hannu kan yarjejeniya da Ma&#8217;aikatar Noma ta Tarayya da kuma Ma&#8217;aikatun Noma na Jihohin Kaduna da Jigawa domin aiwatar da wannan aiki,&#8221; in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban Shirin ya bayyana cewa wannan wani babban cigaba ne a tarihin Najeriya, domin wannan ne karon farko da ake gina cibiyoyin tara madara masu na&#8217;urorin sanyaya madara domin sau\u0199in jigilar ta ba tare da ta lalace ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa wani sashi na shirin, shi ne gina cibiyoyin tara madara tare da horas da mahalarta a matsayin masu tara madara daga karkara wa\u0257anda za su kula da wadannan cibiyoyi da kuma \u0199ungiyoyin ha\u0257in ksn.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-3505\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Screenshot_20250317-071739-240x300.jpg\" alt=\"\" width=\"240\" height=\"300\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Screenshot_20250317-071739-240x300.jpg 240w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Screenshot_20250317-071739.jpg 720w\" sizes=\"auto, (max-width: 240px) 100vw, 240px\" \/><\/p>\n<p>A cikin Kasidarshi, Tsohon Darakta na Raya Al\u2019umma da \u0198ungiyoyin Ha\u0257in Kai a Jihar Kaduna, Mista Yohanna Kabirat, ya ce horon ya mayar da hankali ne kan \u0199ungiyoyin ha\u0257in Kai da gudanarwa, da shugabanci domin su gudanar da \u0199ungiyoyinsu cikin nasara.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya jaddada muhimmancin \u0199ungiyoyin ha\u0257in kai wajen ci gaba mai \u0257orewa ga membobinsu, musamman matasa na Ladduga.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mista Kabirat ya shawarci mahalarta su isar da ilimin da suka samu ga sauran membobinsu, musamman wajen yin bayanawa kowa bayyanai ba tareda an boye ba wanda shi ne babban kalubalen da ya jefa \u0199ungiyoyi da dama cikin matsalolin kudi a baya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Tsohon Daraktan a karshe yace tushen nasarar kowace \u0199ungiyar ha\u0257in Kai shine bin dokokin \u0199ungiyar yadda ya kamata.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da suke magana da Radio Nigeria Kaduna, wasu daga cikin mahalarta taron, Sufyanu Umar da Fatima Isa, sun bayyana farin cikinsu da horon da aka basu, inda suka ce sun samu \u0199warewa ta musamman wajen tafiyar da \u0199ungiyoyinsu cikin nasara da inganci.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mahalarta taron horaswar sun yaba wa CORET da sauran abokan ci gaba bisa shirya taron horaswar da suka ce zai sauya rayuwarsu ta fannin samar da madara.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sun bayyana cewa ilimin da suka samu zai kasance ginshi\u0199i mai \u0257orewa ga rayuwarsu da ci gabansu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Rahoto daga Adamu Yusuf.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; Kungiyar Ha\u0257in Kan Masu Kiwon Gargajiya ta Afrika wato CORET, tare da ha\u0257in gwiwar \u0198ungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ECOWAS, sun bayyana shirinsu na samar da ayyuka guda dubu uku ga matasa ta hanyar sarrafa madara a sarkar darajar madara a Jahohin Kaduna da Jigawa. &nbsp; Shugaban Shirin na CORET, Dr. Umar Hardo, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":21,"featured_media":3507,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[446,758,265,1026,59,895,33,341,841],"class_list":["post-3503","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-446","tag-758","tag-ayyuka","tag-coret","tag-jigawa","tag-jihohin","tag-kaduna","tag-matasa","tag-samarda"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Screenshot_20250317-071631.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3503","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/21"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3503"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3503\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3511,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3503\/revisions\/3511"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3507"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3503"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3503"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3503"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}