{"id":3455,"date":"2025-03-14T08:38:05","date_gmt":"2025-03-14T08:38:05","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=3455"},"modified":"2025-03-14T08:38:15","modified_gmt":"2025-03-14T08:38:15","slug":"gidauniya-za-ta-ci-gaba-da-tallafawa-matasan-jihar-sakkwato-seyi-tinubu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gidauniya-za-ta-ci-gaba-da-tallafawa-matasan-jihar-sakkwato-seyi-tinubu\/","title":{"rendered":"Gidauniyata Za Ta Ci Gaba Da Tallafawa Matasan Jihar Sakkwato &#8211; Seyi Tinubu"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alkawarin Samar da Dokar Shirye-Shiryen Matasa Da Ayyukan<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ministan ci gaban matasa, Ayodele Olawande, ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na karfafa matasa domin samar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin kasar nan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ministan ya ce ziyarar da ya kai jihar Sokoto na da nufin kara cudanya da matasa a cikin watan Ramadan da bayar da tallafi mai mahimmanci.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Olawande, wanda ya samu rakiyar Seyi Tinubu, ya jaddada mahimmancin shirye-shiryen da suka shafi matasa, ciki har da samar da dandalin tattaunawa kan ci gaban matasa na kasa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya yi nuni da cewa, shugaban kasa Bola Tinubu da Gwamna Ahmed Aliyu suna da manufa daya na ci gaban matasa, ta yadda za a yi amfani da albarkatun da aka ware wa Sokoto yadda ya kamata.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ministan ya kuma yaba da bullo da shirin ba da lamuni na dalibai, inda ya bayyana shi a matsayin wani gagarumin shiri na tallafawa daliban Najeriya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma ba da tabbacin cewa, akwai wasu shirye-shiryen da suka shafi matasa, inda Sokoto za ta ci gajiyar muhimman tsare-tsare a fannin noma, gidaje, da kuma shirye-shiryen horarwa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma kara ba da tabbacin cewa FG na kokarin samar da yanayi mai dacewa da matasan Najeriya za su ci gaba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nasa jawabin, gwamna Ahmed Aliyu na sokoto, ya bayyana ziyarar a matsayin wata shaida ga jajircewar da gwamnatin ta yi wajen karfafa matasa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya yabawa Seyi Tinubu, wanda shine wanda ya assasa Renewed Hope Youth Empowerment Initiative, bisa gudunmawar da yake bayarwa a harkokin siyasa da ci gaban tattalin arziki, yana mai kira gare shi da ya mika shirye-shiryensa ga matasan Sokoto.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnan ya kuma bayyana irin kokarin da gwamnatin sa ke yi na tallafa wa matasa da suka hada da nada matasa a manyan mukamai a gwamnati da samar da ilimi kyauta ga dukkan dalibai ba tare da la\u2019akari da addini ko kabila ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya yabawa Tinubu kan irin ayyukan alheri da yake yi a cikin watan Ramadan, musamman ga marasa galihu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Tun da farko, Seyi Tinubu ya bayyana kudirinsa na ci gaban matasa a Sakkwato, inda ya yi alkawarin cewa gidauniyarsa za ta ci gaba da tallafa wa ayyuka a fadin kananan hukumomin jihar 23.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Nasir Malali<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alkawarin Samar da Dokar Shirye-Shiryen Matasa Da Ayyukan &nbsp; Ministan ci gaban matasa, Ayodele Olawande, ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na karfafa matasa domin samar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin kasar nan. &nbsp; Ministan ya ce ziyarar da ya kai jihar Sokoto na da nufin kara cudanya da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":3456,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2,9],"tags":[1016,295,89],"class_list":["post-3455","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","category-tattalin-arziki","tag-seyi","tag-sokoto","tag-tinubu"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/hq720.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3455","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3455"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3455\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3458,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3455\/revisions\/3458"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3456"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3455"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3455"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3455"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}