{"id":3404,"date":"2025-03-13T08:58:37","date_gmt":"2025-03-13T08:58:37","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=3404"},"modified":"2025-03-13T08:58:37","modified_gmt":"2025-03-13T08:58:37","slug":"cutuka-biyar-da-ake-%c9%97auka-a-lokacin-zafi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/cutuka-biyar-da-ake-%c9%97auka-a-lokacin-zafi\/","title":{"rendered":"Cutuka Biyar Da Ake \u018aauka A Lokacin Zafi"},"content":{"rendered":"<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\">Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi garga\u0257i a baya-bayan nan dangane da \u0199aruwar yanayin zafi a sassan \u0199asar, yayin da jihohi da dama suke fuskantar \u0199arin matsanancin zafi.<\/p>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\">Garga\u0257in ya kuma nuna cewa, tsananin zafin da za a yi fama da shi cikin kwanaki uku ko hu\u0257u masu zuwa wanda zai haddasa damuwar da yanayin na zafi kan haifar a jihohi goma sha tara na \u0199asar daga yankin arewa ta tsakiya da yankin gabashin \u0199asar.<\/p>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\">Kan haka ne muka tuntu\u0253i likita domin ya yi mana \u0199arin bayani game da cututtuka biyar da aka fi kamuwa da su a lokacin zafi da kuma hanyoyin kare kai.<\/p>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\"><b>San\u0199arau &#8211;\u00a0<\/b>Dakta Hassan Ibrahim, likita a asibitin Biba da ke jihar Kaduna ya ce cutar san\u0199arau na faruwa ne galibi idan aka samu cunkoson jama&#8217;a a wuri \u0257aya da ya ha\u0257u da zafi.<\/p>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\">A cewarsa, &#8220;\u0199wayoyin cuta za su shiga jikin mutum sai su shafi \u0199wa\u0199walwa sai a samu irin wannan.&#8221;<\/p>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\"><b>Zazza\u0253in cizon sauro &#8211;\u00a0<\/b>Likitan ya ce idan yanayin zafi ya zo, mutane suna yawan bu\u0257e jikinsu domin su sha iska. Ya ce &#8220;mutane sun fi zama a waje lokacin fa\u0257uwar rana, lokacin da sauro ke tasiri da tafiyar da maleriya.<\/p>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\">Hakan yana yawan taso da cutar maleriya a jikin mutane, kamar yadda likitan ya fa\u0257a.<\/p>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\"><b>Fesowar \u0199uraje &#8211;\u00a0<\/b>A lokacin zafi ne ake yawan zufa lamarin da ke janyo fesowar \u0199uraje a jikn mutane wanda a cewar Dakta Hassan, idan ba a kula da su ba, &#8220;aka yi irin wata sosawa, yana iya kawo ciwo da wata \u0199wayar cuta za ta iya ratsawa.&#8221;<\/p>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\"><b>Amai da gudawa &#8211;\u00a0<\/b>Dakta Hassan ya ce a irin wannan lokaci na zafi ne aka fi samun \u0199uda da ru\u0253ewar abinci. Ya ce idan ba a kula da abincin da muke ci ba, aka bari \u0199uda suka yi damalmala a kai, hakan zai iya kawo ciwo a ciki idan aka ci.<\/p>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\"><b>\u0198onewar ruwa a jiki &#8211;\u00a0<\/b>A irin wannan yanayin, jikin mutum na yawan bushewa musamman a tsakanin dattijai. A cewar likitan, abin da ke sa mutum ya ji \u0199ishirwa, idan mutum na da rauni, ba za su samu jikinsu ya ankarar da su cewa su sha ruwa ba, ana so a ri\u0199a shan ruwa a kai a kai.<\/p>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<h2 id=\"Hanyoyin-kariya\" class=\"bbc-u15yok eglt09e0\" tabindex=\"-1\">Hanyoyin kariya<\/h2>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\">Dakta Hassan Ibrahim ya ce muhimman matakan da ya kamata mutane su \u0257auka wajen kare kansu daga kamuwa da cuta a lokacin zafi shi ne tabbatar da cewa ana samun yanayin &#8220;shiga da fita ta iska&#8221; ta hanyar bu\u0257e taga a wuraren kwana da wuraren aiki da kuma rage cunkoson jama&#8217;a a wuri guda.<\/p>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\">Ya kuma ce akwai bu\u0199atar a ri\u0199a amfani da gidan sauro idan za a kwanta domin kare kai daga kamuwa da cutar maleriya inda ya ce akwai bu\u0199atar a ta\u0199aita zama a waje da yamma.<\/p>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\">A cewar likitan, babban matakin da ya kamata mutane su kiyaye shi ne na tabbatar da tsaftar abincin da za ake ci musamman \u01b4a\u01b4an itatuwa da kuma tabbatar da tsaftar jiki.<\/p>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\">\u0198arin wani matakin shi ne yawaita wanka a kai a kai domin rage yanayin zafi a jiki.<\/p>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\">Sai kuma yawaita shan ruwa domin gujewa \u0199onewar ruwa a jiki inda ya shawarci masu azumi da su yawaita shan ruwa da zarar sun yi bu\u0257a baki.<\/p>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<h2 id=\"Abin-da-ya-sa-aka-fi-kamuwa-da-cututtuka-a-yanayin-zafi\" class=\"bbc-u15yok eglt09e0\" tabindex=\"-1\">Abin da ya sa aka fi kamuwa da cututtuka a yanayin zafi<\/h2>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\">Dakta Hassan Ibrahim ya bayyana cewa dalilin shi ne, galibin cututtuka sun fi ha\u0253aka a lokacin zafi saboda yanayin tsaurin jiki da inda jiki ke tafiya.<\/p>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\">&#8220;Jiki yana da yadda yake gyara kansa a duk yanayin da ya shiga, lokacin zafi yana zuwa masa da \u0199arin matsi da yadda jikin zai fitar da zafi da inda zai ri\u0199e daidai.&#8221; in ji likitan.<\/p>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\">&#8220;A lokacin zafi, mun \u0199ara wa jikinmu aiki, saboda a ciki \u0257umi gare shi kuma yana son ya ri\u0199e \u0257umi kuma a lokacin zafi, jikinmu yana \u0199ara aikin fitar da \u0257umi waje yana kuma \u0199o\u0199arin samun abin sanyi da zai iya daidaita yanayin da yake tafiyar da aikin.&#8221;<\/p>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\">Likitan ya ce a irin wannan yanayi da jiki ke tsintar kansa a lokacin zafi, &#8220;akwai rauni da ke tasar da cutuka da za su yi tasiri.&#8221;<\/p>\n<\/div>\n<div class=\"bbc-19j92fr ebmt73l0\" dir=\"ltr\">\n<p class=\"bbc-1y32vyc e17g058b0\" dir=\"ltr\">A cewar shi, kashi 90 na cututtuka a duniya yana da ala\u0199a da wani abu na sarari saboda akwai \u0199wayoyin cuta da suka fi tasiri a yanayin zafi.<\/p>\n<\/div>\n<\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi garga\u0257i a baya-bayan nan dangane da \u0199aruwar yanayin zafi a sassan \u0199asar, yayin da jihohi da dama suke fuskantar \u0199arin matsanancin zafi. Garga\u0257in ya kuma nuna cewa, tsananin zafin da za a yi fama da shi cikin kwanaki uku ko hu\u0257u masu zuwa wanda zai haddasa damuwar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":3407,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[7,3,1,11,4,8],"tags":[1005,926,1004],"class_list":["post-3404","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-fasaha","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","category-tsaro","tag-kariya","tag-nijeriya","tag-zafi"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/71a8ea60-ff40-11ef-b4cb-67926e35576f.jpg.webp","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3404","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3404"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3404\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3408,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3404\/revisions\/3408"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3407"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3404"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3404"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3404"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}