{"id":3382,"date":"2025-03-13T08:09:19","date_gmt":"2025-03-13T08:09:19","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=3382"},"modified":"2025-03-13T08:09:19","modified_gmt":"2025-03-13T08:09:19","slug":"an-bada-umarnin-sake-tsugunar-da-wadanda-harin-yan-bindiga-ya-rutsa-da-su-a-kebbi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/an-bada-umarnin-sake-tsugunar-da-wadanda-harin-yan-bindiga-ya-rutsa-da-su-a-kebbi\/","title":{"rendered":"An Bada Umarnin Sake Tsugunar Da Wadanda Harin \u2018Yan Bindiga Ya Rutsa Da Su A Kebbi"},"content":{"rendered":"<p>Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi, ya ba da umarnin cewa, wadanda harin da \u2018yan bindiga suka kai a sansanin \u2018yan gudun hijira da ke karamar hukumar Arewa ta jihar, su koma gidajensu nan da makonni biyu masu zuwa bayan an dauki matakai a yankunan da lamarin ya shafa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnan, ya ba da umarnin ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje sansanin \u2018yan gudun hijira da ke Kangiwa da Lakurawa suka kai musu hari tare da raba su da muhallansu a kauyukan Birnin Debe, Dan Marke da Tambo.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamnan ya ce, ya kai ziyarar ne domin jajanta wa wadanda abin ya shafa tare da ba shi damar samun rahoton halin da ake ciki a kan wannan mummunan lamari don jagorantar gwamnatin jihar ta dauki matakin da ake bukata tare da tantance halin da ake ciki da kuma tabbatar da matakan da suka dace da za a dauka cikin gaggawa domin kai daukin gaggawa ga wadanda abin ya shafa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A yayin da yake koka da cewa, ana kai hare-haren ne daga jihar Sokoto da ke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar, Gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa kan asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi, ya kuma yaba wa jami\u2019an tsaro da suka yi iya kokarinsu wajen ganin an shawo kan lamarin, ya kuma bukaci jama\u2019a da su rika kai rahoton duk wani motsi da suka samu ga hukuma domin daukar matakin da ya dace.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Tun da farko Shugaban Karamar Hukumar Arewa Alhaji Sani Aliyu ya godewa Gwamnan bisa daukar matakin gaggawa don ganin an shawo kan wannan mummunan lamari.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban ya kuma bayyana cewa an bayar da agajin ga wadanda abin ya shafa, inda ya ce iyalan kowannen wadanda suka rasa rayukansu sun samu Naira 500,000 yayin da kowanne daga cikin wadanda suka jikkata kuma ya samu N500,000.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A ranar Lahadin da ta gabata ne \u2018yan bindigar Lakurawa suka kai hari kauyuka 7 a karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi inda suka kashe sama da mutane 10 tare da kona gidaje da dama wanda hakan ya kasance harin ramuwar gayya biyo bayan kashe wani shugabansu mai suna Maigemu da jami\u2019an tsaro suka yi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Abdullahi Tukur<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi, ya ba da umarnin cewa, wadanda harin da \u2018yan bindiga suka kai a sansanin \u2018yan gudun hijira da ke karamar hukumar Arewa ta jihar, su koma gidajensu nan da makonni biyu masu zuwa bayan an dauki matakai a yankunan da lamarin ya shafa. &nbsp; Gwamnan, ya ba da umarnin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":3383,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,11,2,9],"tags":[534,139,625],"class_list":["post-3382","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","category-tattalin-arziki","tag-gwamna","tag-kebbi","tag-lakurawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/77d5d0cc-97a3-4125-a2f4-a15c3e408501.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3382","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3382"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3382\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3384,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3382\/revisions\/3384"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3383"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3382"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3382"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3382"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}