{"id":3335,"date":"2025-03-08T14:28:01","date_gmt":"2025-03-08T14:28:01","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=3335"},"modified":"2025-03-08T14:29:02","modified_gmt":"2025-03-08T14:29:02","slug":"ramadan-imani-siyasa-dole-su-hadu-don-ci-gaban-kasa-ministan-yada-labarai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/ramadan-imani-siyasa-dole-su-hadu-don-ci-gaban-kasa-ministan-yada-labarai\/","title":{"rendered":"Ramadan: Imani, Siyasa Dole Su Hadu Don Ci Gaban Kasa \u2013 Ministan Yada Labarai"},"content":{"rendered":"<p>Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama\u2019a, Mohammed Idris, ya jaddada mahimmancin haduwar imani da siyasa, da kuma mulki wajen tsara makomar Najeriya gaba \u0257aya.<\/p>\n<p>Ya bayyana hakan ne a Kaduna, yayin Taron Ramadan na Shekara-shekara wanda Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA), Hukumar Rediyon Tarayya (FRCN), da Muryar Najeriya (VON) suka shirya.<\/p>\n<p>Da yake jawabi kan taken &#8220;Imani, Siyasa da Mulki: Shigar Malamai a Siyasa da Tasirinta,&#8221; Ministan ya yabawa masu shirya taron saboda jajircewarsu wajen ci gaba da gudanar da wannan muhimmin taro, wanda ya bayyana a matsayin wata muhimmiyar kafa ta tattaunawa a kasa.<\/p>\n<p>\u201cIna da yakinin cewa wannan jerin laccoci zai ci gaba da haifar da canji mai kyau a kasarmu.<\/p>\n<p>\u201cDuk da haka, a wannan wata mai alfarma na Ramadan, inda iyalai ke haduwa don yin addu\u2019a, yin nazari, nuna jituwa da jin\u0199ai ga juna, babu shakka, batutuwan imani da, siyasa da kuma mulki suna da dangantaka da jiya, yau da kuma gobe. Wajibi ne mu ci gaba da fahimtar yadda za mu tafiyar da su yadda ya dace.<\/p>\n<p>\u201cSai dai, yayin da muke kokarin fahimtar alakar imani da siyasa da kuma mulki, muna kuma fuskantar kalubalen siyasa na ciki da waje, wa\u0257anda ke tasiri ga yadda muke kallon hadin kan kasa a matsayin dunkulalliyar \u0199asa,\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>Ministan ya yaba da halartar manyan baki, ciki har da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani; Ministan Cigaban Kiwo Dabobi, Malam Idi Mukhtar Maiha; da kuma Mai Martaba Sarkin Zazzau, Jakadan Najeriya, Ahmed Nuhu Bamalli. Haka nan, ya gode wa fitattun malamai, Sheikh Morufu Onike Abdulazeez da Farfesa Ismaila Shehu, bisa gudummawar da suka bayar a wannan muhimmin tattaunawa.<\/p>\n<p>Da yake yin tsokaci kan muhimmancin Ramadan, Ministan ya bukaci \u2018yan Najeriya su yi amfani da wannan wata mai alfarma domin yin nazari da inganta hadin kai, da sabunta aniyar su ta bada gudunmawa ga ci gaban kasa.<\/p>\n<p>Ya jaddada irin nasarorin da aka samu a mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman sanya hannu kan kasafin kudi na Naira Tiriliyan 54, wanda ya ba da fifiko kan tsaro, ilimi, ci gaban ababen more rayuwa, kiwon lafiya da noma.<\/p>\n<p>Haka nan, Ministan ya yaba wa Shugaban Kasa kan kirkirar Ma\u2019aikatar Bunkasa Kiyo Dabobi ta Tarayya, wanda ya bayyana a matsayin muhimmin mataki da zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da inganta zaman lafiya a kasa.<\/p>\n<p>\u201cYayin da muke tafiyar da harkokin siyasa da mulki, tare da tasirin da suke da shi kan shawarwarin da muke yanke, yana da matukar muhimmanci mu zabi hanya madaidaiciya,\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>A karshe, Ministan ya bukaci \u2018yan Najeriya su rungumi dabi\u2019un soyayya, jin\u0199ai, da jajircewa a lokacin Ramadan da bayan sa.<\/p>\n<p>\u201cAllahu ya albarkaci iyalanmu, ya shiryar da matakanmu, ya kuma ba mu hikima a dukkan al\u2019amuranmu. Ramadan Kareem,\u201d in ji shi.<\/p>\n<p><strong><em>Rel\/Adamu Yusuf<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama\u2019a, Mohammed Idris, ya jaddada mahimmancin haduwar imani da siyasa, da kuma mulki wajen tsara makomar Najeriya gaba \u0257aya. Ya bayyana hakan ne a Kaduna, yayin Taron Ramadan na Shekara-shekara wanda Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA), Hukumar Rediyon Tarayya (FRCN), da Muryar Najeriya (VON) suka shirya. Da yake [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":18,"featured_media":3336,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[984,983,985,488,218,163,674],"class_list":["post-3335","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-ci-gaba","tag-imani","tag-kasa","tag-minista","tag-ramadan","tag-siyasa","tag-yada-labarai"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Minista-Muhammad-Idris.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3335","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/18"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3335"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3335\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3338,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3335\/revisions\/3338"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3336"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3335"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3335"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3335"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}