{"id":3235,"date":"2025-03-04T10:56:24","date_gmt":"2025-03-04T10:56:24","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=3235"},"modified":"2025-03-04T10:56:24","modified_gmt":"2025-03-04T10:56:24","slug":"kasafin-kudin-bana-zai-samarda-tsarin-tattalin-arziki-da-cigaban-%c6%99asa-ministan-labarai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/kasafin-kudin-bana-zai-samarda-tsarin-tattalin-arziki-da-cigaban-%c6%99asa-ministan-labarai\/","title":{"rendered":"Kasafin Kudin Bana Zai Samarda Tsarin Tattalin Arziki Da Cigaban \u0198asa: Ministan Labarai"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama&#8217;a, Mohammed Idris, ya bayyana kasafin ku\u0257in bana, wanda Shugaba Tinubu ya rattaba wa hannu kwanan nan, a matsayin tsari mai karfi da zai daidaita tattalin arziki da kwanciyar hankali a zamantakewa, da kuma cigaban \u0199asa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya bayyana hakan ne a yayin taron da ake da Ministoci karo na uku da aka gudanar a Cibiyar Manema Labarai ta \u0198asa, Abuja, a yau.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mohammed Idris ya jaddada cewa kasafin ku\u0257in wannan shekarar ya mayar da hankali kan zuba jari a sassa masu muhimmanci da ke da tasiri na kai tsaye kan jin da\u0257i da ci gaban tattalin arzikin \u0199asa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Kasafin ku\u0257i na 2025 ba kawai wata takarda ta ku\u0257i ba ce; yana nuna tsari mai \u0199arfi na daidaita tattalin arziki da kwanciyar hankali a zamantakewa, da kuma cigaban \u0199asa. Wannan kasafin ya maida hankali kan harkokin tsaro da ababen more rayuwa da ilimi da lafiya da ma\u2019adinai da noma da wasu sassa masu matu\u0199ar muhimmanci ga cigaban \u0199asa.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Wannan shekara ta 2025, shekara ce ta tabbatar da sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Tinubu ta aiwatar, domin a fara jin \u0257adin su a zahiri. Tuni muna gani a fili cewa farashin kayan abinci yana raguwa a hankali, wanda ke kawo sau\u0199i ga \u2018yan \u0199asa,&#8221; in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ministan ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta tabbatar da aiwatar da kasafin ku\u0257i yadda ya kamata, tare da nuna gaskiya da ri\u0199on amana wajen cimma burin shirin &#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Ina tabbatar wa \u2018yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiki tu\u0199uru wajen aiwatar da wannan kasafin ku\u0257i domin cimma cikakken tasirinsa a rayuwar al\u2019ummar mu. Don haka, ina kira ga duk \u2018yan \u0199asa su mara wa wa\u0257annan \u0199o\u0199ari baya, domin mu gina Najeriya,&#8221; in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ministan ya yaba wa kafafen ya\u0257a labarai bisa jajircewarsu wajen kawo rahotanni kan taron, yana jaddada muhimmancinsu wajen ya\u0257a sahihan labarai da suka dace, ba tare da son rai ba, tare da mai da hankali kan ci gaban \u0199asa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya nanata cewa kafafen ya\u0257a labarai suna ba da gudunmuwa wajen tabbatar da dorewar dimokura\u0257iyya da kuma tabbatar da cewa \u2018yan Najeriya na samun ingantattun bayanai kan manyan tsare-tsaren sauyi da gwamnati ke aiwatarwa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mohammed Idris ya bayyana cewa dimokura\u0257iyya tana bun\u0199asa ne ta hanyar tattaunawa bisa sani, fahimtar juna, da ha\u0257in gwiwa don cigaban \u0199asa. Saboda haka, ya yi kira ga kafafen ya\u0257a labarai da su ci gaba da kiyaye \u0199a&#8217;idodin daidaito, alhaki, da \u0199warewa a cikin rahotanninsu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;A wannan zamani da labaran \u0199arya da son rai ke iya rinjayar tunanin jama&#8217;a cikin sau\u0199i, sadaukarwarku ga gaskiya da adalci ya fi zama mai muhimmanci fiye da da. Dole ne mu yi aiki tare don tabbatar da cewa bayanan da ke tsara ra\u2019ayoyin jama\u2019a sun dace da ainihin gaskiyar yadda ake tafiyar da mulki, ba tare da son rai ko \u0199ayatarwa maras tushe ba,&#8221; in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Taron Minista karo na uku ya kuma samu halartar Ministan Masana&#8217;antu, Ciniki da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole, da Ministan kasa, Sanata John Owan Enoh.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Rel\/Adamu Yusuf<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama&#8217;a, Mohammed Idris, ya bayyana kasafin ku\u0257in bana, wanda Shugaba Tinubu ya rattaba wa hannu kwanan nan, a matsayin tsari mai karfi da zai daidaita tattalin arziki da kwanciyar hankali a zamantakewa, da kuma cigaban \u0199asa. &nbsp; Ya bayyana hakan ne a yayin taron da ake da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":21,"featured_media":3236,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2],"tags":[958,959,600,954,960,841,957,956,955],"class_list":["post-3235","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","tag-arziki","tag-cigaban","tag-kasafin","tag-kudin-bana","tag-asa-minista","tag-samarda","tag-tattalin","tag-tsarin","tag-zai"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/Screenshot_20250304-115505.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3235","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/21"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3235"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3235\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3237,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3235\/revisions\/3237"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3236"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3235"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3235"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3235"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}