{"id":3212,"date":"2025-03-03T12:45:43","date_gmt":"2025-03-03T12:45:43","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=3212"},"modified":"2025-03-03T12:45:43","modified_gmt":"2025-03-03T12:45:43","slug":"gwamnatin-jihar-kano-ta-kaddamar-da-shirin-ciyarwar-na-watan-ramadan","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-jihar-kano-ta-kaddamar-da-shirin-ciyarwar-na-watan-ramadan\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar Da Shirin Ciyarwar Na Watan Ramadan"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da shirin ciyarwa a watan Ramadan na shekarar 2025 a hukumance, da nufin samar da abincin buda baki ga mabukata 91,000 a fadin jihar.<\/p>\n<p>Shirin wanda zai dauki tsawon kwanaki 27 yana daga cikin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na tallafawa dimbin al&#8217;ummarta a watan na Ramadan.<\/p>\n<p>Mataimakin gwamnan jihar Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo wanda kuma shi ne shugaban shirin, ya kaddamar da shirin a hukumance a cibiyar Dandali dake karamar hukumar Fagge.<\/p>\n<p>Ya nuna jin dadinsa da yadda aka gudanar da shirin cikin kwanciyar hankali, tare da yin kira ga kamfanonin da abin ya shafa da su tabbatar da isar da abinci cikin lokaci da inganci a dukkanin cibiyoyin ciyar da abincin.<\/p>\n<p>Za a aiwatar da shirin a\u00a0 cibiyoyin ciyar da abinci 91 da aka ke\u0253e, inda aka tanadar da\u00a0 masu dafa abinci don ciyar da mutum 91,000\u00a0 abinci a kowace rana.<\/p>\n<p>Gwamnatin jihar Kano ta ware makudan kudade domin tabbatar da nasarar shirin, inda ta nuna aniyar ta na tallafawa marasa galihu a wannan wata na Ramadan.<\/p>\n<p>Bikin kaddamar da shirin ya samu halartar manyan jami\u2019an gwamnati da suka hada da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, da kwamishinan harkokin addini, Sheikh Tijjani Auwal.<\/p>\n<p><strong><em>Daga Khadija Aliyu<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da shirin ciyarwa a watan Ramadan na shekarar 2025 a hukumance, da nufin samar da abincin buda baki ga mabukata 91,000 a fadin jihar. Shirin wanda zai dauki tsawon kwanaki 27 yana daga cikin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na tallafawa dimbin al&#8217;ummarta a watan na Ramadan. Mataimakin gwamnan [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":3213,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[943,39,218],"class_list":["post-3212","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-ciyarwa","tag-kano","tag-ramadan"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/IMG-20250303-WA0011.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3212","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3212"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3212\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3214,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3212\/revisions\/3214"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3213"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3212"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3212"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3212"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}