{"id":3196,"date":"2025-03-02T03:25:10","date_gmt":"2025-03-02T03:25:10","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=3196"},"modified":"2025-03-02T18:23:55","modified_gmt":"2025-03-02T18:23:55","slug":"malaman-furanare-116-sun-gabatar-da-adduoi-a-zaria","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/malaman-furanare-116-sun-gabatar-da-adduoi-a-zaria\/","title":{"rendered":"Malaman Furamare 116 Sun Gabatar da Addu&#8217;o&#8217;i a Zaria"},"content":{"rendered":"<p>Malamai daga makarantun firamare 116 dake karamar hukumar Zaria sun gudanar da taron addu&#8217;o&#8217;i na musamman ga shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajuddeen da gwamnatin jihar Kaduna.<\/p>\n<p>Malaman sun gudanar da addu&#8217;o&#8217;in ne domin nuna farinciki da godiya bisa yadda suke matukar kula da ilimi,wanda hakan ya inganta harkokin ilimin kuma ya kara bunkasa jin dadin Malaman yankin.<\/p>\n<p>Sakatariyar ilimi ta karamar hukumar Zaria, Dr Hassana Lawal ta shedawa manema labaru lokacin addu&#8217;o&#8217;in a zaria cewa a kalla Malaman makarantun firamare 2,225 ne suka amfana da tallafin kayan abinci domin gudanar da azumin watan Ramadan.<\/p>\n<p>A cewar ta,kayan abincin sun hada da kilo 25 na shinkafa da lita 4 na man gyada da fakitin tafiya da kuma kilo 10 na buhun garin samabita.<\/p>\n<p>&#8220;Wannan shine karo na 8 da shugaban majalisar wakilan ya baiwa malaman makarantar firamaren irin wannan tallafin tun daga lokacin da hau karagar shugabancin majalisar.<\/p>\n<p>&#8220;Baya ga tallafin kayan abinci,ya baiwa duk shugabannin makarantun firamare 116 da ke yankin kyautar babura domin saukaka masu zuwa wurin aiki,wanda a cewar ta abin godiya ne matuka&#8221;.<\/p>\n<p>Haka kuma sakatariyar ilimin ta yaba da kokarin da gwamnan jihar kaduna, Malam Uba Sani ke yi na bunkasa ilimi a jihar.<\/p>\n<p>Dr Lawal ta ce kokarin da gwamnan ke yi sun kushi gina ajujuwa 12 a makarantun firamare da dama a karamar hukumar Zaria baya ga tallafin kayan karatu, wanda hakan ne yasa dole su yi masu addu&#8217;o&#8217;in.<\/p>\n<p>Ta kara da cewa Malaman sun zami watan Ramadan ne domin gudanar da addu&#8217;o&#8217;in Allah ya baiwa shugaban majalisar wakilai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilimi nasara da kwarin gwiwa wajen ci gaba da bunkasa ilimi a jihar.<\/p>\n<p>A nashi jawabin, sakataren Kungiyar malamai na karamar hukumar Zaria, Malam Kasimu Mohammed ya ce tallafin kayan abincin ya taimaka wa Malaman matukar gaske.<\/p>\n<p>A don haka sai ya bukaci sauran yan siyasa da masu hannu da shuni da su yi koyi shugaban majalisar wakilan ta hanyar tallafawa Malaman makarantun firamare a yankunan su.<\/p>\n<p>Haliru Hamza<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Malamai daga makarantun firamare 116 dake karamar hukumar Zaria sun gudanar da taron addu&#8217;o&#8217;i na musamman ga shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajuddeen da gwamnatin jihar Kaduna. Malaman sun gudanar da addu&#8217;o&#8217;in ne domin nuna farinciki da godiya bisa yadda suke matukar kula da ilimi,wanda hakan ya inganta harkokin ilimin kuma ya kara bunkasa jin dadin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":3197,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11],"tags":[624,941,562],"class_list":["post-3196","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","tag-addua","tag-furame","tag-zaria"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/IMG-20250302-WA0003.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3196","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3196"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3196\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3199,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3196\/revisions\/3199"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3197"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3196"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3196"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3196"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}