{"id":3062,"date":"2025-02-24T20:35:08","date_gmt":"2025-02-24T20:35:08","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=3062"},"modified":"2025-02-24T20:35:08","modified_gmt":"2025-02-24T20:35:08","slug":"hukumar-npc-za-ta-gudanar-da-kidayar-jamaa-cikin-aminci-shugaba-tinubu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/hukumar-npc-za-ta-gudanar-da-kidayar-jamaa-cikin-aminci-shugaba-tinubu\/","title":{"rendered":"Hukumar NPC Za Ta Gudanar Da Kidayar Jama\u2019a Cikin Aminci- Shugaba Tinubu"},"content":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Tinubu ya ce Najeriya ta dauki wani muhimmin mataki na gudanar da kidayar jama&#8217;a da gidaje da aka jima ba a yi ba, inda\u00a0 ya tabbatar da cewa za a gudanar da aikin cikin inganci ta hanyar amfani da fasahar zamani.<\/p>\n<p>Shugaban ya ba da wannan tabbacin ne a wata ganawa da ya yi da jami\u2019an hukumar kula da yawan jama\u2019a ta kasa (NPC) a fadar gwamnati, shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin kidayar jama\u2019a ga tsare-tsare na kasa, tare da jaddada aniyarsa na tabbatar da tattara bayanai masu inganci.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya bayyana shirin kafa kwamitin da zai duba kasafin kidayar jama\u2019a da kuma gano hanyoyin samun kudade.<\/p>\n<p>Ya kuma jaddada bukatar hukumar kula da tantance &#8216;yan kasa (NIMC) ta taka rawar gani wajen gudanar da wannan aiki, tare da tabbatar da samar da ingantattun na\u2019urorin tantancewa da suka hada da tantance fuska da murya.<\/p>\n<p>Shugaban ya bayyana cewa ingantattun bayanan\u00a0 za su ha\u0253aka shirye-shiryen gwamnati, musamman a fannin aikin gona da walwalar jama&#8217;a.<\/p>\n<p>Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya tabbatar da kudurin na Tinubu, inda ya bayyana cewa rashin kudi ne ya janyo tsaikon kidayar jama\u2019a.<\/p>\n<p>Ya kuma bayyana cewa, NPC ta riga ta kammala muhimman ayyukan shirye-shirye da suka hada da kidayar jama\u2019a, sannan kuma hukumomin tantancewa da kididdiga daban-daban kamar su NPC, NIMC, NBS, da Ma\u2019aikatar Tattalin Arziki, suna\u00a0 aiki tare don inganta bayanan da ake da su.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Bello Wakili<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Tinubu ya ce Najeriya ta dauki wani muhimmin mataki na gudanar da kidayar jama&#8217;a da gidaje da aka jima ba a yi ba, inda\u00a0 ya tabbatar da cewa za a gudanar da aikin cikin inganci ta hanyar amfani da fasahar zamani. Shugaban ya ba da wannan tabbacin ne a wata ganawa da ya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":1040,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,9],"tags":[897,439],"class_list":["post-3062","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tattalin-arziki","tag-kidayar-jamaa","tag-shugaba-tinubu"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/President-Tinubu.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3062","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3062"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3062\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3065,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3062\/revisions\/3065"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1040"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3062"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3062"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3062"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}