{"id":2905,"date":"2025-02-19T06:54:36","date_gmt":"2025-02-19T06:54:36","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=2905"},"modified":"2025-02-19T11:19:49","modified_gmt":"2025-02-19T11:19:49","slug":"an-bukaci-dillalai-da-su-rage-farashin-kayan-abinci","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/an-bukaci-dillalai-da-su-rage-farashin-kayan-abinci\/","title":{"rendered":"An Bukaci Dillalai Da Su Rage Farashin Kayan Abinci"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin tarayya ta yi kira ga masu siyar da kayan abinci da su rage farashin kayan domin rage tasirin hauhawar farashin kayayyaki da tsadar kayan abinci ga \u2018yan Najeriya.<\/p>\n<p>Ministan noma da samar da abinci Alhaji Abubakar Kari ne ya yi wannan roko a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa a bikin ranar noman alkama na shekarar 2025 da gwamnatin jihar Jigawa ta shirya.<\/p>\n<p>Ministan wanda ya bayyana yadda wasu marasa kishin kasa ke je fa masu amfani da kayan abinci cikin rudami, ya bukaci masu kishin kasa da su nuna yadda ake ci gaba da samun ragi farashin kayan abinci a bangarori daban daban.<\/p>\n<p>\u201cGwamnatin tarayya tana sane da yadda farashin kayan abinci ya ragu sosai a manyan kasuwanni, musamman na kayan masarufi kamar su gari, shinkafa, fulawa da spaghetti.<\/p>\n<p>\u201cDuk da haka, abin damuwa ne yadda \u2019yan kasuwa da yawa, masu yin burodi, da masu shaguna suka ki yin la\u2019akari da wannan ragi na farashin, wanda hakan ya hana \u2018yan Nijeriya samun sassaucin da ya kamace su.<\/p>\n<p>\u201cA watannin da suka gabata, masu ruwa da tsaki a harkar samar da abinci sun nuna damuwa kan tashin farashin kayayyakin abinci amma yanzu farashin ya ragu.<\/p>\n<p>\u201cMisali, farashin fulawa ya ragu daga Naira 81,000 a kowane buhu zuwa kasa N60,000 da Spaghetti daga Naira 20,000 zuwa Naira 15,000, don haka adalci ne kuma masu amfani da su sun ci gajiyar wannan ragi.<\/p>\n<p>\u201cGwamnati ta kuduri aniyar tabbatar da samar da abinci kuma za ta ci gaba da hada hannu da masu ruwa da tsaki domin magance wannan matsala.<\/p>\n<p>\u201cDon haka ina kira ga daukacin \u2019yan kasuwa da su nuna halin da ake ciki a kasuwanni a halin yanzu a farashinsu, kuma su yi aiki da gaskiya don saukaka wa \u2018yan Najeriya.<\/p>\n<p>&#8220;Cutar da masu &#8216;yan Nijeriya a lokacin da ake bu\u0199atar taimako shine mafi rashin kishin \u0199asa kuma ba za a yarda da shi ba,&#8221; in ji Ministan.<\/p>\n<p>Ya sanar da bayar da gudunmawar injunan ban ruwa dubu goma, dana feshi dubu goma, da lita dubu goma na maganin ciyawa, da sauran lita dubu goma na maganin kwari, da buhunan takin gargajiya, da sauran kayayyaki na Naira biliyan biyar domin tallafawa manoma a jihar Jigawa.<\/p>\n<p>A nasa jawabin gwamna Umar Namadi ya yabawa gwamnatin tarayya bisa tallafin da take baiwa manoman jihar.<\/p>\n<p>Ya ce an fara samun sauyi a harkar noman alkama a jihar Jigawa a shekarar da ta gabata inda gwamnatin tarayya ta kebe kayan noma na musamman ga manoma dubu takwas bisa tallafin kudi.<\/p>\n<p>Ya ce manoman sun noma hekta dubu arba\u2019in na alkama domin karawa kokarin gwamnatin tarayya, ya ce gwamnatin jihar ta tallafa wa manoma 16,454 da rancen Naira biliyan 2.2, wanda suka amince za su biya bayan girbi.<\/p>\n<p>Gwamna Namadi ya ce aikin ya samu nasara, inda aka samu farfadowar kashi 80 cikin 100 kuma ya jawo kudaden shiga sama da Naira biliyan 8 ga tattalin arzikin jihar.<\/p>\n<p>Usman Muhammad Zaria<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin tarayya ta yi kira ga masu siyar da kayan abinci da su rage farashin kayan domin rage tasirin hauhawar farashin kayayyaki da tsadar kayan abinci ga \u2018yan Najeriya. Ministan noma da samar da abinci Alhaji Abubakar Kari ne ya yi wannan roko a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa a bikin ranar noman alkama [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":2906,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,11,2,9,8],"tags":[852,853,59],"class_list":["post-2905","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","category-tattalin-arziki","category-tsaro","tag-ajinci","tag-farashi","tag-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/IMG-20250219-WA0005.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2905","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2905"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2905\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2908,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2905\/revisions\/2908"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2906"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2905"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2905"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2905"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}