{"id":290,"date":"2024-03-02T23:46:21","date_gmt":"2024-03-02T23:46:21","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=290"},"modified":"2024-03-02T23:49:24","modified_gmt":"2024-03-02T23:49:24","slug":"manyan-attajiran-duniya-sun-halarci-bikin-auren-dan-wani-attajiri-a-indiya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/manyan-attajiran-duniya-sun-halarci-bikin-auren-dan-wani-attajiri-a-indiya\/","title":{"rendered":"Manyan Attajiran Duniya Sun Halarci Bikin Auren Dan Wani Attajiri A Indiya"},"content":{"rendered":"<p>Wasu daga cikin manyan masu fada a ji a duniya sun isa jihar Gujarat ta kasar Indiya domin halartar bikin auren mutum mafi dukiya a nahiyar Asiya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Daga cikin bakin akwai shugaban facebook Mark Zuckerberg da shahararriyar mawakiya Rihanna da tsohon wanda ya fi kowa arziki a duniya Bill Gates.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Dukkanin su sun halarci walimar da Mukesh Ambani, shugaban rukunin kamfanonin Reliance Industries, kuma attajiri mafi dukiya a nahiyar Asiya ya shirya domin murnan bikin auren dan shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Matashi Anant Ambani, mai shekara 28 a duniya zai auri masoyiyarsa Radhika Merchant a cikin watan Yuli.<\/p>\n<p>Shahararrun &#8216;yan wasan fina finan\u00a0 Indiya, Shah Rukh Khan da Amitabh Bachchan na daga cikin wadanda suka halarci walimar ta kwana uku wadda ta gudana a birnin Jamnagar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Yanzu haka Mukesh Ambani, mai shekara 66 a duniya shi ne mutum na 10 a jerin mutane mafiya kudi a duniya, inda dukiyarsa ta kai dalar Amurka biliyan 115, kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mahaifin Mukeh Ambani ne ya kafa rukunin kamfanin Reliance Industries a shekarar 1966, wanda katafaren rukunin kamfanoni ne da ya kunshi hadawa da sayar da kaya daban-daban sai kuma harkar hada-hadar kudi da na sadarwa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Anant Ambani shi ne dan\u2019auta a cikin \u2018yayan mahaifin nasa uku, wadanda dukkanin su suke cikin manyan shugabannin rukunin kamfanonin na Reliance Industries.<\/p>\n<p>Matashin na aiki a bangaren kasuwancin makamashi na rukunin kamfanonin kuma yana cikin shugabannin da ke tafiyar da lamurran gidauniyar rukunin kamfanonin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wannan kasaitacciyar walimar aure ta ji da gani daya ce daga cikin irin su da iyalan na Ambani suka yi kaurin suna wajen shiryawa.<\/p>\n<p>A shekarar 2018, shahararriyar mawakiyar Amurka, Beyonce na daga cikin wadanda suka cashe a walimar daurin auren \u2018yar Mista Ambani, Isha Ambani, wanda aka yi a birnin Udaipur. Tsofaffin sakatarorin harkokin waje na Amurka Hillary Clinton da John Kerry na daga cikin wadanda suka halarci walimar ta wancan lokaci.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wani rahoto na kafar yada labaru ta Bloomberg a wancan lokaci ya kiyasta cewa an kashe kudi dalar Amurka miliyan 100 a lokacin bikin &#8211; sai dai wani \u2018na kusa da iyalin Ambani\u2019 ya musanta batun, inda ya ce kudin da aka kashe bai wuce dala miliyan 15 ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Walimar ta wannan karo ta fara ne daga farkon wannan mako, inda iyalin na Ambani suka raba abinci ga al\u2019ummar garin Jamnagar.<\/p>\n<p>Sauran bakin da aka gani wurin taron sun hada da maidakin tsohon shugaban Amurka, Ivanka Trump, da tsoffin firaministocin Canada da Autralia, wato Stephen Harper da Kevin Rudd.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Wasu daga cikin manyan masu fada a ji a duniya sun isa jihar Gujarat ta kasar Indiya domin halartar bikin auren mutum mafi dukiya a nahiyar Asiya. &nbsp; Daga cikin bakin akwai shugaban facebook Mark Zuckerberg da shahararriyar mawakiya Rihanna da tsohon wanda ya fi kowa arziki a duniya Bill Gates. &nbsp; Dukkanin su sun [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":291,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,12,6],"tags":[105,104],"class_list":["post-290","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-ketare","category-nishadi","tag-bikin-dan-attajiri","tag-indiya"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/533178_7648211_updates.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/290","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=290"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/290\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":292,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/290\/revisions\/292"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/291"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=290"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=290"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=290"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}