{"id":283,"date":"2024-03-02T23:18:37","date_gmt":"2024-03-02T23:18:37","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=283"},"modified":"2024-03-02T23:50:59","modified_gmt":"2024-03-02T23:50:59","slug":"jagoran-mulkin-sojin-chadi-ya-bayyana-aniyar-takara-gabanin-zabe","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jagoran-mulkin-sojin-chadi-ya-bayyana-aniyar-takara-gabanin-zabe\/","title":{"rendered":"Jagoran Mulkin Sojin Chadi Ya Bayyana Aniyar Takara Gabanin Zabe"},"content":{"rendered":"<p>Jagoran gwamnatin sojin Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno ya bayyana aniyarsa ta yin takara a zaben shugaban kasar mai zuwa, wanda aka tsara za a yi a ranar 6 ga wata Mayun wannan shekarar, kwanaki 3 kacal bayan da aka kashe babban abokin hamayyarsa a wani yanayi mai sarkakiya.<\/p>\n<p>Deby Itno ya dare karagar mulkin Chadi ne a shekarar 2021, bayan mutuwar mahaifinsa Idriss Deby Itno a yayin da ya ke jagorantar yaki da \u2018yan tawaye, bayan sama da shekaru 30 a kan mukamin shugaban kasar da ke yankin Sahel.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mahamat Idriss Deby Itno, ya bayyana a wani jawabi da ya gabatar wa al\u2019ummar kasar cewa zai yi takarar shugabancin kasar a karkashin gamayyar da gwamnati ta hada.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A shekarar 2021 ce aka nada Deby a matsayin jagoraan gwamnatin soji, kuma a lokacin ne ya yi alkawarin mika mulki ga farar hula a cikin watanni 18.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Amma Deby ya tsawaita wannan wa\u2019adi da karin shekaru 2, kuma gwamnatinsa ta yi amfani da karfi fiye da kima wajen murkushe masu zanga-zangar adawa da matakin nasa a watan Oktoban shekarar 2022.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A ranar Talatar da ta gabata ce gwamnatin sojin Chadi ta sanar da cewa a ranar 6 ga watan Mayu za ta gudanar da babban zaben kasar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Masu lura da al\u2019amura na cewa Deby mai shekaru 39 yana da yakinin lashe zabe, duba da cewa an kashe babban abokin hamayyarsa, kuma dan uwansa, Yaya Dillo Djerou, kuma ga shi mahukunta sun murkushe sauran \u2018yan adawa.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Jagoran gwamnatin sojin Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno ya bayyana aniyarsa ta yin takara a zaben shugaban kasar mai zuwa, wanda aka tsara za a yi a ranar 6 ga wata Mayun wannan shekarar, kwanaki 3 kacal bayan da aka kashe babban abokin hamayyarsa a wani yanayi mai sarkakiya. Deby Itno ya dare karagar mulkin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":284,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,12],"tags":[103,101,102],"class_list":["post-283","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-ketare","tag-jagoran-mulkin-soji","tag-kasar-chadi","tag-takara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/jad20230214-ass-tchad-idriss-deby-itno-01-1256x628-1677231818.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/283","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=283"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/283\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":285,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/283\/revisions\/285"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/284"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=283"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=283"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=283"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}