{"id":2819,"date":"2025-02-14T09:04:05","date_gmt":"2025-02-14T09:04:05","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=2819"},"modified":"2025-02-14T09:04:05","modified_gmt":"2025-02-14T09:04:05","slug":"ku-ajiye-makamanku-ba-tare-da-wani-shara%c9%97i-ba-kafin-lokaci-ya-%c6%99ure-gwamna-lawal","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/ku-ajiye-makamanku-ba-tare-da-wani-shara%c9%97i-ba-kafin-lokaci-ya-%c6%99ure-gwamna-lawal\/","title":{"rendered":"Ku Ajiye Makamanku Ba Tare Da Wani Shara\u0257i Ba Kafin Lokaci Ya \u0198ure &#8211; Gwamna Lawal"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bibiyar \u2019yan ta\u2019adda har sai an fatattake su, an ruguza su tare da mur\u0199ushe su.<\/p>\n<p>Gwamnan ya mi\u0199a kayan aikin da gwamnatin jihar Zamfara ta samar domin kafa hedikwatar tsaro ta dakarun sojin &#8216;Operation Safe Corridor&#8217; na jihohin Arewa maso Yamma.<\/p>\n<p>A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa &#8216;Operation Safe Corridor&#8217; zai ta tabbatar da canja \u0199wa\u0199wale, ha\u0257e kai magance duk al&#8217;amuran da suka shafi \u2019yan bindiga.<\/p>\n<p>Sanarwar ta \u0199ara da cewa, an tsara shirin ne a \u0199ar\u0199ashin Operation Safe Corridor a yankin Arewa maso Gabas, wanda ya yi nasarar sauya \u0199wa\u0199walen tsoffin maya\u0199an Boko Haram tare da gyara tubabbun su.<\/p>\n<p>\u201cShirin Arewa maso Yamma na neman bayar da tsarin tuba ga mutanen da ke da hannu cikin ayyukan \u2018yan bindiga. Wannan yun\u0199urin zai \u0199unshi horar da su wajen sana&#8217;o&#8217;i, canja musu tunani, da sake musu fasalin a\u0199ida.&#8221;<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya ce gwamnatin jihar ta samar da wurin ne a matsayin wani shiri na taimaka wa gwamnatin tarayya wajen magance matsalar &#8216;yan bindiga da ya addabi Zamfara da Arewa maso Yamma sama da shekaru goma.<\/p>\n<p>\u201cIna so in sake mayar da al\u0199awarin da gwamnatinmu ta yi na tallafa wa wa\u0257annan tsare-tsare da sauran dabaru masu inganci da ake amfani da su wajen kai wannan ya\u0199i zuwa ga \u2019yan bindigar har sai an fatattake su yadda ya kamata tare da mur\u0199ushe su.<\/p>\n<p>\u201cAmma ga wa\u0257anda suka yi niyyar mi\u0199a makamansu ba tare da wani shara\u0257i ba da son rai, suna da \u2018yancin yin hakan. Kafa Hedikwatar Rundunar Tsaro ta Operation Safe Corridor na Arewa maso Yamma zai ba da dama da masu niyyar tuba tare da gyara musu \u0257abi&#8217;arsu.<\/p>\n<p>\u201cA kan wannan batu, ina so in mi\u0199a godiyata ga Babban Hafsan Tsaron \u0198asa, Janar Christopher Musa, na ganin jihar Zamfara ta cancanci karbar ba\u0199uncin Operation Safe Corridor na 3 a \u0199asar nan.<\/p>\n<p>\u201cIna kuma so in gode wa shugaban kwamitin aiwatar da ayyukan Operation Safe Corridor na Arewa maso Yamma, Manjo Janar EV Onumajoro, wanda kuma shi ne Babban Hafsan Harkokin Tsaro na Hedikwatar Tsaron Nijeriya, da tawagarsa saboda ganin Zamfara ta dace da kafa hedikwatar wannan muhimmin dakaru.<\/p>\n<p>\u201cDaga \u0199arshe muna godiya ga Shugaban \u0198asa Bola Ahmed Tinubu, kuma Babban Kwamandan Askarawan Tarayyar Nijeriya, bisa dukkan \u0199o\u0199arinsa da goyon bayansa ga hukumomin tsaro da ke aiki a jihar.<\/p>\n<p>\u201cAbin da ake bu\u0199ata shi ne \u0199ara \u0199arfafa nasarorin da aka samu wajen mur\u0199ushe ayyukan \u2019yan bindiga da sauran aikata laifuka. Ina so in tabbatar muku da \u0199udurinmu na yin komai don ganin cewa wannan shirin ya yi nasara. A garemu a yau, wannan shi ne haihuwar sabuwar Zamfara mai tsari.<\/p>\n<p>&#8220;Da wa\u0257annan &#8216;yan kalamai, ina so in mi\u0199a wannan cibiyar domin yin aiki a matsayin hedikwatar Operation Safe Corridor na Arewa maso Yamma domin amfanin jihar Zamfara da kuma \u0199yaunatacciyar \u0199asarmu Nijeriya.&#8221;<\/p>\n<p>Tun da farko, Manjo Janar Onumajuru, wanda ya wakilci Babban Hafsan Tsaron \u0198asar, ya yaba wa Gwamna Lawal bisa goyon bayan da yake baiwa sojoji a ya\u0199in da ake da \u2019yan bindiga a Zamfara.<\/p>\n<p>\u201cOperation Safe Corridor dakaru ce mai aiki da cikakken tsari. Tana aiki a matsayin hanyar samar da zaman lafiya. Bayan karbar ragamar wannan ginin, za mu ci gaba da ha\u0257a kai da Gwamna da al\u2019ummar Zamfara, wa\u0257anda su ne masu ruwa da tsaki a wannan aiki, domin tabbatar da ha\u0257in kai da samun nasara.<\/p>\n<p>Aminu Dalhatu\/Gusau<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bibiyar \u2019yan ta\u2019adda har sai an fatattake su, an ruguza su tare da mur\u0199ushe su. Gwamnan ya mi\u0199a kayan aikin da gwamnatin jihar Zamfara ta samar domin kafa hedikwatar tsaro ta dakarun sojin &#8216;Operation Safe Corridor&#8217; na jihohin Arewa maso Yamma. A [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":2820,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2,9,8],"tags":[828,23,115],"class_list":["post-2819","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","category-tattalin-arziki","category-tsaro","tag-lawal","tag-tsaro","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/abdc022f-262d-40ab-bd25-7d172b253b7c.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2819","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2819"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2819\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2821,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2819\/revisions\/2821"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2820"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2819"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2819"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2819"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}