{"id":280,"date":"2024-03-02T23:03:23","date_gmt":"2024-03-02T23:03:23","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=280"},"modified":"2024-03-02T23:03:23","modified_gmt":"2024-03-02T23:03:23","slug":"jihar-jigawa-za-ta-kafa-asusun-bada-agaji-ga-wadanda-ambaliyar-ruwa-ta-shafa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jihar-jigawa-za-ta-kafa-asusun-bada-agaji-ga-wadanda-ambaliyar-ruwa-ta-shafa\/","title":{"rendered":"Jihar Jigawa Za Ta Kafa Asusun Bada Agaji Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za ta kafa asusun bada agajin gaggawa na dindindin domin kula da Iftila\u2019in\u00a0 ambaliyar ruwa da ke faruwa a jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan jihar\u00a0 Hamisu Mohammed Gumel ya rabawa manema labarai a Dutse.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce gwamna Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da kwamitin kula da Iftila\u2019in\u00a0 ambaliyar ruwa a gidan gwamnati na Dutse.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cewarsa, kwamitin wanda Architect Aminu Kani ke jagoranta, yana da alhakin kammala kafa asusun bada agajin gaggawa na ambaliya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hamisu Gumel ya ci gaba da bayanin cewa, an dora wa \u2018yan kwamitin alhakin gudanar da ayyukansu cikin sauki da kuma tafiyar da asusun.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A jawabinsa yayin kaddamarwar, Gwamna Namadi ya bayyana jin dadinsa da irin ci gaban da aka samu kawo yanzu wajen magance matsalar ambaliyar ruwa a shekarar 2022.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma jaddada muhimmancin daukar matakin gaggawa wajen magance matsalolin da ke kan gaba a cikin rahoton kwamitin da ya gabata.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya yaba da kokarin da tsohon kwamatin ya yi, wanda ya tattara sama da naira biliyan 1 da aka ware domin samar da tallafi ga sama da mutane dubu talatin da hudu da Iftila\u2019in ya shafa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;<em>Manufar ita ce Asusun Tallafawa ya zama matakin gaggawa na farko don gyarawa da kuma bada\u00a0 agaji ga wadanda iftila\u2019in ya rutsa da su a kan tsari mai dorewa. Tuni tsohon kwamitin ya gabatar da wani daftarin kudirin doka amma yana bukatar a sake duba shi kafin a kammala shi domin daukar matakin da ya dace<\/em>.\u201d Inji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce Gwamna Namadi ya bayyana kwarin gwiwa kan yadda mambobin kwamitin za su iya cika aikinsu a cikin wa&#8217;adin watanni biyu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma kara da cewa Gwamnan ya\u00a0 ba su tabbacin tallafin kayan aiki da suka dace don saukaka gudanar da ayyukansu cikin sauki.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Usman Muhammad Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za ta kafa asusun bada agajin gaggawa na dindindin domin kula da Iftila\u2019in\u00a0 ambaliyar ruwa da ke faruwa a jihar. &nbsp; Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan jihar\u00a0 Hamisu Mohammed Gumel ya rabawa manema labarai a Dutse. &nbsp; Ya ce gwamna Umar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":281,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[100,99,59],"class_list":["post-280","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-ambaliyar-ruwa","tag-asusun-agajin-gaggawa","tag-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/IMG-20240303-WA0001.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/280","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=280"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/280\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":282,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/280\/revisions\/282"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/281"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=280"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=280"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=280"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}