{"id":2686,"date":"2025-02-07T08:59:04","date_gmt":"2025-02-07T08:59:04","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=2686"},"modified":"2025-02-07T08:59:04","modified_gmt":"2025-02-07T08:59:04","slug":"shugaba-tinubu-ya-sauke-shugabar-jamiar-abuja-farfesa-aisha-maikudi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/shugaba-tinubu-ya-sauke-shugabar-jamiar-abuja-farfesa-aisha-maikudi\/","title":{"rendered":"Shugaba Tinubu Ya Sauke Shugabar Jami&#8217;ar Abuja Farfesa Aisha Maikudi"},"content":{"rendered":"<p>Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sauye-sauyen shugabanci a jami\u2019o\u2019in gwamnatin tarayya da dama da suka hada da Jami\u2019ar Abuja wadda a yanzu ake kira da Jami\u2019ar Yakubu Gowon.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai Bayo Onanuga ya ce a jami\u2019ar Yakubu Gowon, shugaba Tinubu ya rusa majalisar zartarwa gaba daya tare da sauke Farfesa Aisha Sani Maikudi daga mukaminta na shugabar Jami\u2019ar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sanata Lanre Tejuoso, wanda a halin yanzu shi ne uban Jami\u2019ar Aikin Gona ta Makurdi ne aka nada shi a matsayin Uban Jami\u2019ar Yakubu Gowon. Sanata Joy Emordi, wacce a yanzu ita ce shugabar jami\u2019ar ilimi ta Alvan Ikoku za ta gaje shi a Makurdi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya nada Farfesa Lar Patricia Manko a matsayin mukaddashiyar shugaban jami\u2019ar Yakubu Gowon na tsawon watanni shida. Ba za ta cancanci neman matsayin Shugabancin Jami&#8217;ar ba idan aka tashi neman shugaba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Bugu da kari, shugaba Tinubu ya cire Farfesa Polycarp Emeka Chigbu daga mukaminsa na Shugaban jami\u2019ar Nsukka (UNN), kafin wa\u2019adinsa ya kare a ranar 14 ga watan Fabrairu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>An nada Farfesa Oguejiofu T. Ujam a matsayin magajinsa na tsawon watanni shida kuma ba zai cancanci neman mukamin na dindindin ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gen. Ike Nwachukwu ya koma Uban Jami&#8217;ar Uyo. Shugaba Tinubu ya nada Injiniya Olubunmi Kayode Ojo a matsayin sabon shugabar UNN. A baya, Ojo ya rike wannan matsayi a Jami\u2019ar Tarayya ta Lokoja da Jami\u2019ar Tarayya ta Oye-Ekiti.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Farfesa Zubairu Tajo Abdullahi, wanda a halin yanzu shi ne Uban Jami\u2019ar Uyo, an nada shi ya gaji Ojo a Jami\u2019ar Tarayya ta Lokoja.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sanata Sani Stores shi ne sabon Shugaban Jami\u2019ar Ilimi ta Alvan Ikoku, wanda ya gaji Sanata Joy Emordi. Sanata Stores dan majalisa ne a Jami&#8217;ar Najeriya, Nsukka.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Bugu da kari kuma, Barista Olugbenga Kukoyi, wanda dan majalisa ne a jami\u2019ar Najeriya, Nsukka, an nada shi a matsayin sabon shugaban jami\u2019ar Nnamdi Azikiwe da ke Awka a jihar Anambra.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sanarwar ta bayyana cewa duk nade-naden mukamai sun fara aiki ne nan take.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya jaddada cewa, wadannan sauye-sauyen na nuni da kudirin gwamnatinsa na farfado da harkar ilimi mai zurfi a Najeriya ta hanyar jagoranci da rikon amana.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sanarwar ta kara da cewa sake fasalin na da nufin karfafa harkokin mulki da nagartar ilimi a bangaren ilimin manyan makarantun Najeriya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Bello Wakili<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sauye-sauyen shugabanci a jami\u2019o\u2019in gwamnatin tarayya da dama da suka hada da Jami\u2019ar Abuja wadda a yanzu ake kira da Jami\u2019ar Yakubu Gowon. &nbsp; A wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai Bayo Onanuga ya ce a jami\u2019ar Yakubu Gowon, shugaba [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":2687,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11,2,9,8],"tags":[425,793,794,795],"class_list":["post-2686","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","category-tattalin-arziki","category-tsaro","tag-abuja","tag-aihs","tag-aisha","tag-maikuid"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/images.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2686","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2686"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2686\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2688,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2686\/revisions\/2688"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2687"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2686"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2686"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2686"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}