{"id":2674,"date":"2025-02-07T08:20:32","date_gmt":"2025-02-07T08:20:32","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=2674"},"modified":"2025-02-07T08:20:32","modified_gmt":"2025-02-07T08:20:32","slug":"kisan-rimin-zakara-gwamnan-kano-ya-umarci-jamiar-bayero-ta-dakatar-da-rushe-gidaje","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/kisan-rimin-zakara-gwamnan-kano-ya-umarci-jamiar-bayero-ta-dakatar-da-rushe-gidaje\/","title":{"rendered":"Kisan Rimin Zakara: Gwamnan Kano Ya Umarci Jami\u2019ar Bayero Ta Dakatar Da Rushe Gidaje"},"content":{"rendered":"<p>Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci al\u2019ummar Rimin Zakara da ke karamar hukumar Ungogo domin jajantawa iyalan wadanda rikicin ya rutsa da su wanda ya yi sanadin asarar rayuka uku tare da jikkata wasu da dama.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A ziyarar tasa, Gwamna Yusuf ya gana da iyalan wadanda suka rasu, inda ya jajanta musu tare da bayyana cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin iyalan mutanen uku da suka rasu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma ba da umarnin a gaggauta biyan kudaden jinya ga duk wadanda suka jikkata tare da samar da kayan abinci don tallafawa iyalan wadanda abin ya shafa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cikin nuna jin kai, gwamnan ya bayyana shirin gina sabon masallacin Juma\u2019a a Rimin Zakara a matsayin sadaqatu jariya (dauwamammiyar sadaka) da aka sadaukar da rayukan ukun da suka rasu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Bugu da kari, gwamnan ya kaddamar da wani tsari na ci gaban al&#8217;umma, wanda ya hada da:<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ha\u0257a al&#8217;ummar yankin da tashar wutar lantarki ta kasa da Gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana domin samar da ruwa mai tsafta da Samar da cibiyar kula da lafiya ta farko don inganta ayyukan kiwon lafiya da ha\u0253aka hanyar ciyarwa don inganta sufuri a cikin Rimin Zakara.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Gwamna Yusuf ya yi kakkausar gargadi ga jami\u2019an tsaro kan amfani da harsasai masu rai kan \u2018yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba, yana mai jaddada cewa irin wannan abu ba abu ne da za a amince da shi ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Domin tabbatar da bin diddigin lamarin, gwamnan ya kafa kwamitin bincike da aka dorawa alhakin gano musabbabin faruwar lamarin tare da zakulo wadanda ke da hannu a lamarin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hakazalika, gwamnan ya kuma yi wa mahukuntan Jami\u2019ar Bayero ta Kano huduba a ofishinsa tare da umartar su da su dakatar da duk wani mataki na rusa gine gine a wajen.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma bayyanawa al\u2019ummar yankin kudurin sa na ganin an shawo kan rikicin fili da aka shafe sama da shekaru 40 ana yi tsakanin al\u2019ummar Rimin Zakara da Jami\u2019ar Bayero Kano.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban al\u2019ummar yankin, Baba Habu Mikail, ya nuna matukar godiya ga gwamnan bisa yadda ya nuna tausayi, inda ya bayyana cewa al\u2019umma ba za su taba mantawa da alherinsa ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci al\u2019ummar Rimin Zakara da ke karamar hukumar Ungogo domin jajantawa iyalan wadanda rikicin ya rutsa da su wanda ya yi sanadin asarar rayuka uku tare da jikkata wasu da dama. &nbsp; A ziyarar tasa, Gwamna Yusuf ya gana da iyalan wadanda suka rasu, inda ya jajanta musu tare da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":2675,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11,2,9,8],"tags":[534,39,97],"class_list":["post-2674","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","category-tattalin-arziki","category-tsaro","tag-gwamna","tag-kano","tag-ziyara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/e8002295-0ba2-4990-bca1-d070e73eabde-1.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2674","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2674"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2674\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2676,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2674\/revisions\/2676"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2675"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2674"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2674"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2674"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}