{"id":2643,"date":"2025-02-06T08:58:59","date_gmt":"2025-02-06T08:58:59","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=2643"},"modified":"2025-02-06T08:58:59","modified_gmt":"2025-02-06T08:58:59","slug":"gwamnatin-niger-ta-karbi-yara-21-da-aka-ceto","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-niger-ta-karbi-yara-21-da-aka-ceto\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Niger Ta Karbi Yara 21 Da Aka Ceto"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin jihar Neja ta karbi yara ashirin da daya da aka kama a kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar yayin da ake safarar su zuwa Sudan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Yakubu Garba wanda ya bayyana haka a lokacin da yake karbar yaran a madadin gwamnatin jihar Neja a Minna, ya ce an kama yaran ne a cikin kasashen Kamaru da Mali da Jamhuriyar Nijar da kuma Sudan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kwamared Yakubu Garba ya bayyana cewa yaran da aka ceto \u2018yan karamar hukumar Magama ne a jihar Neja, amma ya yaba da kokarin gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da kuma hukumar fataucin bil\u2019adama bisa nasarar ceto yaran.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ci gaba da cewa ta\u2019addancin ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya sashe na 34 karamin sashe na 1 da sashe na 13 na kundin tsarin mulkin kasa da ya haramta duk wani nau\u2019in safarar mutane a kasar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da yake mayar da martani, daya daga cikin iyayen yaran da aka ceto, Jamilu Usman wanda ya bayyana \u2018ya\u2019yansa biyu Umar Jamilu mai shekaru 6 da Maruf Jamilu mai shekaru 5 ya bayyana cewa Malam Abubakar sananne ne a wurinsu wanda ya yi karatu a Jamhuriyar Nijar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa sun ba wa \u2018ya\u2019yansu damar tafiya da Malam Abubakar Jamhuriyar Nijar domin samun ilimin addinin Musulunci, inda ya jaddada cewa shi ne shugaban makarantar firamare ta Tungan Gari da ke karamar hukumar Magama, yana da mata hudu da \u2018ya\u2019ya talatin kuma zai ajiye aiki nan da shekaru biyar masu zuwa, shi ne ya sa suka bashi \u2018ya\u2019yansu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sai dai ya kara da cewa suna biyan dubu 35 ga kowane yaro kowane wata domin su sami damar samun ilimin da ake bukata.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>KARSHEN ALIYU LAWA\/Wababe<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin jihar Neja ta karbi yara ashirin da daya da aka kama a kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar yayin da ake safarar su zuwa Sudan. &nbsp; Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Yakubu Garba wanda ya bayyana haka a lokacin da yake karbar yaran a madadin gwamnatin jihar Neja a Minna, ya ce an kama yaran [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":2645,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,5,1,11],"tags":[476,785],"class_list":["post-2643","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","tag-niger","tag-safarar-yara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/9f78fe82-dd51-4c48-95cc-be2a97a06283.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2643","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2643"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2643\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2646,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2643\/revisions\/2646"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2645"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2643"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2643"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2643"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}