{"id":264,"date":"2024-03-01T18:49:25","date_gmt":"2024-03-01T18:49:25","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=264"},"modified":"2024-03-01T18:49:25","modified_gmt":"2024-03-01T18:49:25","slug":"shugaban-majalisar-musulmi-ya-yi-kakkausar-suka-game-da-yadda-wasu-malamai-ke-sukar-junansu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/shugaban-majalisar-musulmi-ya-yi-kakkausar-suka-game-da-yadda-wasu-malamai-ke-sukar-junansu\/","title":{"rendered":"Shugaban  Majalisar Musulmi  Ya Yi Kakkausar Suka Game Da Yadda Wasu Malamai Ke Sukar Junansu"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban Majalisar Musulmi ta Kasa Ustaz Sadiq Abdulrahman Abiodun ya tunatar da malaman addinin musulunci bukatar yin amfani da hikima da kyautatawa yayin gabatar da wa\u2019azi akan ka\u2019idojin shari\u2019ar musulunci domin sanya mabiyan su akan turbar da ta dace.<\/p>\n<p>Shugaban\u00a0 ya sanar da hakan ne a taron bita ta yini guda da aka shiryawa malamai da limamam addinin musulunci a Kaduna.<\/p>\n<p>Ustaz Sadiq Abdulrahman Abiodun ya nuna rashin jin dadin sa bisa yadda wasu malaman addinin musulunci ke amfani da kafafen sada zumunta na zamani suna sukar junan su, wanda a cewar sa wannan bai dace da tsarin addinin musulunci ba, maimakon haka su yi amfani da kafafen wajen yada addinin musulunci.<\/p>\n<p>Shugaban ya ce ya zama wajibi ga Majalisar Kula da Addinin Musulunci ta Kasa ta janyo hankalin malamai su shiga taitayinsu, a matsayinsu na masu dora mutane akan tafarkin bautawa Mahalicci sannan su gudanar da tsaftatacciyar rayuwa.<\/p>\n<p>Ya yi kira ga iyaye musulmi su rika duba takardu da darussan da ake koyawa \u2018ya\u2019yansu a makarantu don gudun ka da a koya musu munanan dabi\u2019u da ka iya bata musu tarbiya.<\/p>\n<p>Da yake gabatar da makala akan muhimmancin ilimi ga rayuwar malaman addinin musulunci, limamin masallacin MCAN a Kabala da Unguwan Mu\u2019azu, Alfa Abdulrasheed Muhammed Jami\u2019u Al-Iraqi, ya ce ya zama wajibi malaman addinin musulunci su zurfafa neman ilimin addini domin ilmantar da mabiya dokokin shari\u2019ar musulunci sau da kafa a kasar nan.<\/p>\n<p>Ya shawarce su da kada su nuna son rai da jahiltar fannin da basu da kwarewa akai, don gudun kada su yada karya akan addinin musulunci, wanda yin hakan ka iya batar da mutane.<\/p>\n<p>Shi ma a makalar da ya gabatar mai taken, Dabarun Gabatar da Wa\u2019azi, wanda malamai ya kamata su rika amfani da su, Alfa Ahmed Busairy ya ce ya zama wajibi malaman addinin musulunci su lakanci ilimin nahawu, baya ga sanin Qur\u2019ani da Sunnah.<\/p>\n<p>Ya kara da cewa, akwai bukatar malaman addinin musulunci su yi amfani da hikima da nuna juriya da hakuri yayin gabatar da wa\u2019azi, kasancewar suna mu\u2019amula da mutane masu sabanin fahimta.<\/p>\n<p>Taron bitar na yini guda ya samu halartar malami da Limaman addinin musulunci daga kungiyoyin musulunci da dama.<\/p>\n<p><strong>Shamsuddeen<\/strong><em><strong> Munir Atiku<\/strong><\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; Shugaban Majalisar Musulmi ta Kasa Ustaz Sadiq Abdulrahman Abiodun ya tunatar da malaman addinin musulunci bukatar yin amfani da hikima da kyautatawa yayin gabatar da wa\u2019azi akan ka\u2019idojin shari\u2019ar musulunci domin sanya mabiyan su akan turbar da ta dace. Shugaban\u00a0 ya sanar da hakan ne a taron bita ta yini guda da aka shiryawa [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":265,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[33,94,50],"class_list":["post-264","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kaduna","tag-majalisar-musulmi-ta-kasa","tag-taro"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/IMG-20240301-WA0024.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/264","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=264"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/264\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":266,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/264\/revisions\/266"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/265"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=264"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=264"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=264"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}