{"id":2597,"date":"2025-02-04T18:28:20","date_gmt":"2025-02-04T18:28:20","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=2597"},"modified":"2025-02-04T18:28:20","modified_gmt":"2025-02-04T18:28:20","slug":"an-bukaci-gwamnoni-su-yi-koyi-da-gwamnatin-neja-wajen-magance-rikicin-manoma-da-makiyaya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/an-bukaci-gwamnoni-su-yi-koyi-da-gwamnatin-neja-wajen-magance-rikicin-manoma-da-makiyaya\/","title":{"rendered":"An Bukaci Gwamnoni Su Yi Koyi Da Gwamnatin Neja Wajen Magance Rikicin Manoma Da Makiyaya"},"content":{"rendered":"<p>An shawarci gwamnonin jihohin Arewa da su yi koyi da gwamnatin jihar Neja wajen magance matsalolin rikicin makiyaya da manoma a yankin domin samun ci gaba mai dorewa.<\/p>\n<p>Shugaban kungiyar Miyetti Allah ta kasa MACBAN, Dokta Baba Usman Ngelzarman ne ya bayar da wannan shawarar a wajen wani taro na musamman na karramawa\u00a0 tare da tabbatar da lakabin gargajiya ga wasu fitattun Fulani guda biyu a jihar Neja, da aka gudanar a fadar Sarkin Minna.<\/p>\n<p>Dokta Baba Usman Ngelzarman ya bayyana cewa, hanyar da Gwamna Mohammed Umar Bago na Jihar Neja ya bi na samar da sakamako mai kyau, ta yadda za a rage yawan rikicin makiyaya da manoma a jihar abin a yaba ne matuka.<\/p>\n<p>A cewarsa hakan ya sanya bangarorin 2 sun kara fahimta da mutunta juna, wanda ya haifar da karuwar kudaden shiga a jihar da ma Najeriya baki daya.<\/p>\n<p>Mai martaba Sarkin Minna Dr Umar Faruk Bahago, ya jaddada bukatar masu rike da mukaman gargajiya a yankinsa su rika gudanar da ayyukansu bisa tsoron Allah,\u00a0 ta hanyar yin adalci ga kowa, don samun nasara.<\/p>\n<p>A nasa jawabin sabon Jauro Minna kuma Kwamishinan kula da harkokin Makiyaya da kiwo na jihar Neja, Umar Ahmed Rebe ya yi alkawarin kara himma wajen inganta alakar manoma da makiyaya, wadda\u00a0 za ta ci gaba da\u00a0 kasancewa cikin kwanciyar hankali da walwala domin samun kyakkyawan sakamako.<\/p>\n<p>A nashi jawabin, Wakilin Fulanin Minna, Alhaji Hassan Usman Shiroro, ya yi kira ga Fulanin jihar Neja da su ci gaba da zama lafiya da kowa domin bunkasa ci gaban jihar Neja cikin hanzari, yana mai jaddada cewa zaman lafiya shi ne abin da ake bukata na duk wani ci gaba mai ma\u2019ana.<\/p>\n<p><strong><em>Daga Aliyu Lawal<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>An shawarci gwamnonin jihohin Arewa da su yi koyi da gwamnatin jihar Neja wajen magance matsalolin rikicin makiyaya da manoma a yankin domin samun ci gaba mai dorewa. Shugaban kungiyar Miyetti Allah ta kasa MACBAN, Dokta Baba Usman Ngelzarman ne ya bayar da wannan shawarar a wajen wani taro na musamman na karramawa\u00a0 tare da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":2599,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,10,9,8],"tags":[686,634],"class_list":["post-2597","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-noma","category-tattalin-arziki","category-tsaro","tag-jihar-neja","tag-kungiyar-miyetti-allah"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/IMG-20250204-WA0016.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2597","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2597"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2597\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2600,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2597\/revisions\/2600"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2599"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2597"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2597"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2597"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}