{"id":2551,"date":"2025-02-01T18:34:56","date_gmt":"2025-02-01T18:34:56","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=2551"},"modified":"2025-02-01T18:34:56","modified_gmt":"2025-02-01T18:34:56","slug":"gwamnatin-jihar-kaduna-ta-biya-fiye-da-mahajjata-3000-kudadensu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-jihar-kaduna-ta-biya-fiye-da-mahajjata-3000-kudadensu\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Biya Fiye da Mahajjata 3,000 Kudadensu.  \u00a0"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hukumar Jin Da\u0257in Alhazai ta Jihar Kaduna ta biya fiye da Mahajjata dubu uku da suka kammala aikin Hajjin shekarar 2023 kudaden da Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) ta mayar masu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mai Magana da Manema Labarai na hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi, shine ya bayyana hakan sannan ya kara da cewa an turawa kowane mahajjati ya kar\u0253i sama da naira dubu sittin da \u0257aya a asusunsa bakinsa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON ta bayyana cewa an mayar da kudaden ne saboda katsewar wutar lantarki a lokacin da maniyyata ke Muna, wanda ya shafi tsarin sanyaya iska kuma hakan ya janyo musu matsala.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hukumar Alhazai na Jihar Kaduna ta ta yaba da hakurin wadanda har yanzun basu same kudadensu ba, inda ya bayyana cewa jinkirin ya faru ne sakamakon wasu maniyyata ba su bayar da cikakken bayanan asusun ajiyarsu na banki ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mallam Yunusa Abdullahi ya tabbatar da cewa an shirya sake fitar da wani zagaye na biyan kudaden a mako mai zuwa, kuma hukumar tana aiki tukuru don tabbatar da cewa dukkan alhazan 2023 da suka cancanta sun kar\u0253i ku\u0257insu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Jami\u2019in Hul\u0257a da Jama\u2019a ya jaddada muhimmancin gabatar da bayanan asusun banki cikin lokaci, yana kira ga duk maniyyatan 2023 da har yanzu ba su kar\u0253i ku\u0257insu ba su tuntubi jami\u2019in rijista na ofishin \u0199aramar hukumarsu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&#8220;Wa\u0257annan bayanai suna da matu\u0199ar muhimmanci don hanzarta mayar da ku\u0257i ga sauran Mahajjatan,&#8221; yana mai jaddada cewa KSPWA na da \u0199udirin tabbatar da an biya dukkan kudaden Mahajjatan mudin sun banyarda bayanan asusun bankinsu akan lokaci.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Idan baza a manta ba, Shugaban Hukumar, Malam Salihu Abubakar, ya ce, &#8220;Mun fahimci muhimmancin mayarda wa\u0257annan kudaden, kuma mun dukufa wajen tabbatar da cewa an kammala rabonsu cikin sauri da gaskiya.&#8221;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sanarwar ta bayyana cewa, baya ga kammala biyan kudaden mayarwa na shekarar 2023, hukumar ta riga ta fara mai da hankali kan shirye-shiryen aikin Hajjin bana.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Rel\/Adamu Yusuf<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; Hukumar Jin Da\u0257in Alhazai ta Jihar Kaduna ta biya fiye da Mahajjata dubu uku da suka kammala aikin Hajjin shekarar 2023 kudaden da Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) ta mayar masu. &nbsp; Mai Magana da Manema Labarai na hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi, shine ya bayyana hakan sannan ya kara da cewa an turawa kowane [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":21,"featured_media":2552,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[446,758,755,756,231,232,33,759,757],"class_list":["post-2551","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-446","tag-758","tag-biya","tag-fiyeda","tag-gwamnatin","tag-jihar","tag-kaduna","tag-kudadensu","tag-mahajjata"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/02\/IMG-20250201-WA0033.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2551","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/21"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2551"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2551\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2553,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2551\/revisions\/2553"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2552"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2551"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2551"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2551"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}