{"id":2546,"date":"2025-01-30T21:14:26","date_gmt":"2025-01-30T21:14:26","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=2546"},"modified":"2025-01-30T21:14:26","modified_gmt":"2025-01-30T21:14:26","slug":"shugaba-tinubu-ya-jinjinawa-yan-najeriya-mazauna-kasashen-waje-bisa-nuna-halin-dattaku","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/shugaba-tinubu-ya-jinjinawa-yan-najeriya-mazauna-kasashen-waje-bisa-nuna-halin-dattaku\/","title":{"rendered":"Shugaba Tinubu Ya Jinjinawa &#8216;Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje Bisa Nuna Halin Dattaku"},"content":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa rahotanin da ya samu game\u00a0 kyawawan dabi\u2019u da \u2018yan Nijeriya mazauna kasashen waje suke nunawa a kasashen da suke, yana mai cewa hakan zai zaburar da matasa kan dabi\u2019un da ke kara martabar kasa.<\/p>\n<p>Shugaban ya yabawa \u2018yan Najeriya mazauna kasashen waje yayin da ya karbi wasiku daga jakadan kasar\u00a0 Kanada a Najeriya, Pasquale Salvaggio, da jakadan Saliyo, Dr Julius F. Sandy, a fadar gwamnati.<\/p>\n<p>Har ila yau, shugaba Tinubu ya karbi wasikun amincewa da nuna gamsuwa daga Legesse Geremew Haile, jakadan kasar Habasha a Najeriya, da Archbishop Michael Francis Crotty, shugaban Bishop Bishop na fadar Vatican a Najeriya.<\/p>\n<p>Babban Kwamishinan na Kanada ya shaida wa Shugaba Tinubu cewa \u2019yan Najeriya suna da himma a fannin ilimi, da wasannin motsa jiki, da kimiyya, da lafiya, da kasuwanci a kasarsa.<\/p>\n<p>Ya ce &#8216;yan Najeriya a Kanada suna nuna kyawawan dabi\u2019u da wayewa, da kwazo yayin\u00a0 cimma burinsu.<\/p>\n<p>Salvaggio, wanda a baya ya yi aiki a Ghana da Cote&#8217;Ivoire, ya ce Kanada na neman fadada sha&#8217;awarta a kan man fetur da iskar gas, da al&#8217;amuran da suka shafi fasahar zamani, da noma, a dangantakar ta Najeriya.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya yaba da nasarorin da \u2018yan Najeriya suka samu a kasashen waje, yana mai bayyana su a matsayin abin zaburarwa ga mutane da dama.<\/p>\n<p>A wani taron da ya yi da babban jakadan Saliyo kuwa, shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa, muradin Najeriya na ci gaban gabar tekun Yamma da Afirka shi ne abin da ya sa a gaba.<\/p>\n<p>Shugaban ya shaida wa jakadan cewa jarin da Najeriya ta yi a Saliyo na tsawon shekaru da dama ya taimaka wajen ci gaban Afirka da kuma inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.<\/p>\n<p>Jakadan ya godewa shugaban kasar bisa goyon bayan da Najeriya ke bayarwa wajen cigaban kasarsa.<\/p>\n<p>Ya ce\u00a0&#8220;<em>A Saliyo, &#8216;yan Najeriya sun fi &#8216;yan kasar <\/em><em>\u00a0yin kasuwanci, yawancin malamai a makarantu &#8216;yan Najeriya ne, babu bambanci tsakanin dan Najeriya da dan Saliyo idan kana tafiya a kan titin Freetown.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>&#8220;<em>Muna bukatar ci gaba da neman zaman lafiya a nahiyarmu, ya kamata mu hada karfi da karfe wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, kalubalen da muke fuskanta a Afirka shi ne rashin tsaro, wanda ke hana ci gaba, ba mu da wanda zai kawo mana zaman lafiya, ssai in mun yi aiki tukuru.<\/em>&#8221; in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Bello Wakili<\/em><\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa rahotanin da ya samu game\u00a0 kyawawan dabi\u2019u da \u2018yan Nijeriya mazauna kasashen waje suke nunawa a kasashen da suke, yana mai cewa hakan zai zaburar da matasa kan dabi\u2019un da ke kara martabar kasa. Shugaban ya yabawa \u2018yan Najeriya mazauna kasashen waje yayin da ya karbi wasiku [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":1536,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,12],"tags":[89,751],"class_list":["post-2546","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-labaran-ketare","tag-tinubu","tag-xyan-najeriya-mazauna-kasashen-waje"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/05\/Bola-Tinubu-2.png","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2546","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2546"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2546\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2547,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2546\/revisions\/2547"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1536"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2546"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2546"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2546"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}