{"id":2468,"date":"2025-01-27T08:51:28","date_gmt":"2025-01-27T08:51:28","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=2468"},"modified":"2025-01-27T08:51:28","modified_gmt":"2025-01-27T08:51:28","slug":"an-bukaci-sarakuna-su-ci-gaba-da-yiwa-alumma-aiki","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/an-bukaci-sarakuna-su-ci-gaba-da-yiwa-alumma-aiki\/","title":{"rendered":"An Bukaci Sarakuna Su Ci Gaba Da Yiwa Al&#8217;umma Aiki"},"content":{"rendered":"<p>Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Danladi Jatau, ya bukaci sarakunan gargajiya da su ci gaba da karfafa hadin kai da zaman lafiya a yankunansu domin samun ci gaba a jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban majalisar ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin murnar cika shekaru 5 akan mulki da kuma murnar cika shekaru 50 da haihuwar HRH, Chim Nku, Mista Habila Adamu Aboki a karamar hukumar Akwanga.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mista Danladi Jatau, wanda ya bayyana muhimmancin hadin kai da zaman lafiya ga ci gaban al\u2019umma, ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya da su ci gaba da sasanta al\u2019ummarsu domin zaman lafiya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya taya sarkin mai daraja ta biyu murnar tare da yi masa fatan Allah ya kara masa lafiya da kariya da kuma hikima a shekaru masu zuwa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban majalisar ya kuma bukaci jama\u2019a da su ci gaba da addu\u2019a tare da marawa Gwamna Abdullahi Sule da sauran shugabannin baya domin samun nasara.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Tun da farko, HRH Mista Habila Adamu Aboki, Chim Nku, ya ce ya yanke shawarar shirya taron ne domin ya gode wa Allah a kan rayuwarsa da ta \u2019yan uwa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma yabawa Gwamna Abdullahi Sule da sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki da sauran jama\u2019a bisa goyon bayan da suke ba shi don samun nasara.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Basaraken ya yi amfani da wannan damar wajen tabbatar da aniyarsa na inganta hadin kai da zaman lafiya a tsakanin talakawansa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>COV\/Aliyu Muraki\/Lafia.\/Wababe<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, Danladi Jatau, ya bukaci sarakunan gargajiya da su ci gaba da karfafa hadin kai da zaman lafiya a yankunansu domin samun ci gaba a jihar. &nbsp; Shugaban majalisar ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin murnar cika shekaru 5 akan mulki da kuma murnar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":2469,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,6,2,9],"tags":[348,472,725],"class_list":["post-2468","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-nishadi","category-siyasa","category-tattalin-arziki","tag-nasarawa","tag-sarakuna","tag-shekara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/download-1.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2468","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2468"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2468\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2470,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2468\/revisions\/2470"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2469"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2468"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2468"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2468"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}