{"id":2460,"date":"2025-01-26T20:53:53","date_gmt":"2025-01-26T20:53:53","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=2460"},"modified":"2025-01-26T20:53:53","modified_gmt":"2025-01-26T20:53:53","slug":"unicef-ya-kara-jan-hankalin-gwamnatin-najeriya-game-da-ilimin-yaya-mata","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/unicef-ya-kara-jan-hankalin-gwamnatin-najeriya-game-da-ilimin-yaya-mata\/","title":{"rendered":"UNICEF Ya Kara Jan Hankalin Gwamnatin Najeriya Game Da Ilimin &#8216;Ya&#8217;ya Mata"},"content":{"rendered":"<p>Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su kara himma wajen yara mata na samun damar yin karatu.<\/p>\n<p>Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah, ne ya yi wannan kiran a Kano a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta 2025.<\/p>\n<p>Ya kara da cewa alkaluma sun nuna cewa \u2018yan mata miliyan 7 da 600 ba sa zuwa makaranta, inda shiyyar Arewa maso Yamma da arewa maso gabas ke da kashi 48 cikin 100 na adadin.<\/p>\n<p>Ya danganta wannan kididdigar da abubuwan da suka hada da talauci da ka\u2019idojin zamantakewa da nuna wariyar jinsi, wadanda ke dakile bai wa \u2018ya\u2019ya mata damar samun ilimi.<\/p>\n<p>A lokacin da yake gabatar da bitar ayyukan UNICEF na inganta karatun yara mata da kuma ci gaba da karatu, shugaban ofishin kula da kananan yara na jihar Kano, Rahama Mohammed Farah, ya ce asusun ya samu\u00a0 hadin gwiwa da gwamnati da al\u2019umma wajen magance matsalolin.<\/p>\n<p>Ya ce UNICEF ta kuma yi amfani da tallafin kudi da sauran abubuwan karfafa gwiwa don karfafawa iyaye gwiwa, su yi rajistar \u2018ya\u2019yansu mata da tabbatar da ganin sun ci gaba da zuwa makaranta.<\/p>\n<p>Ya yi bayanin cewa, \u201c<em>UNICEF ya yi kokari matuka a wannan fanni, ciki har da bayar da kudade domin karfafa musu gwiwa wajen tura \u2018ya\u2019yansu mata zuwa makaranta tare da tallafa musu zuwa matakin sakandare\u201d.<\/em><\/p>\n<p>Ya yi bayanin yadda asusun ya ke inganta fasahar rubutu da karatun \u2018ya\u2019ya mata ta hanyar cibiyoyin karatun \u2018yan mata don \u2018yan mata (G4G), inda kimanin \u2018yan mata da ke zuwa makaranta miliyan 2 da 600 su ke samun ilimi ta hanyoyin sadarwa da suka hada da rediyo da talabijin a hakin yanzu.<\/p>\n<p>&#8220;<em>UNICEF ya kuma inganta kwazon malamai don ilmantar da &#8216;ya&#8217;ya mata, tare da kara yawan malamai a makarantun firamare 42,000<\/em>&#8220;, inji Farah.<\/p>\n<p>Ya yi bayanin cewa UNICEF ya kuma gina tare da gyara wuraren tsaftar ruwa a makarantu 33 a fadin jihohin Kano da Jigawa,\u00a0 wadanda \u2018yan mata 19,622 ke amfani da su.<\/p>\n<p>Ya ce asusun yana kuma\u00a0 aiki tare da masu tsara manufofi a fannin ilimi don tabbatar da ingantacciyar kariya ga yara da ayyukan makaranta ga yara mata, yayin da kuma yana inganta kwazon malamai\u00a0 da za su\u00a0 jagoranci\u00a0 yara mata.<\/p>\n<p>Taron manema labaran ya samu halartar \u2018yan jaridu\u00a0 daga jihohin Kano,\u00a0 da Jigawa da Katsina.<\/p>\n<p><strong><em>Usman Mohammed da Isma&#8217;il Adamu<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su kara himma wajen yara mata na samun damar yin karatu. Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah, ne ya yi wannan kiran a Kano a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":2461,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11],"tags":[723,704],"class_list":["post-2460","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","tag-ilimin-yaya-mata","tag-unicef"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/IMG-20250126-WA0036.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2460","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2460"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2460\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2462,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2460\/revisions\/2462"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2461"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2460"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2460"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2460"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}