{"id":2365,"date":"2025-01-23T09:18:38","date_gmt":"2025-01-23T09:18:38","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=2365"},"modified":"2025-01-23T09:18:38","modified_gmt":"2025-01-23T09:18:38","slug":"can-ta-yaba-saboda-agajin-gaggawa-ga-mutanen-da-fashewar-tanka-ta-shafa-a-neja","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/can-ta-yaba-saboda-agajin-gaggawa-ga-mutanen-da-fashewar-tanka-ta-shafa-a-neja\/","title":{"rendered":"CAN Ta Yaba Saboda Agajin Gaggawa Ga Mutanen Da Fashewar Tanka Ta Shafa a Neja"},"content":{"rendered":"<p>Kungiyar kiristocin Najeriya reshen jihar Neja (CCN) ta yaba da martanin gaggawar da gwamna Umar Mohamed Bago ya yi kan fashewar tankar da ta afku a mahadar Diko da ke karamar hukumar Gurara a jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban karamar hukumar Daniel Tsado wanda ya yi wannan yabon a cikin wata sanarwa da ya fitar a Minna, ya ce saurin mayar da martanin da Gwamnan ya yi sa\u2019o\u2019i kadan bayan faruwar lamarin na nuna matukar damuwarsa kan halin da al\u2019ummar jihar ke ciki.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Neja game da mutuwar da aka yi tare da bukatar wadanda suka rasa \u2018yan uwansu da su dauki wannan rashi kaddara daga Ubangiji, yana mai cewa mutuwa za ta iya zuwa ta kowace hanya kuma a kowane hali.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Venerable Daniel Tsado wanda kuma shi ne Mataimakin Cocin St Peter&#8217;s Anglican na Gbaiko a karamar hukumar Bosso, ya yi addu&#8217;ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon fashewar a ranar Asabar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma yi bayanin cewa daukacin Coci-coci na jihar suna bakin ciki kan wannan mummunan lamari tare da jajanta wa Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago kan rasuwar da aka samu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban ya kuma tabbatar da kudurin CCN reshen jihar Neja na goyon bayansu ga manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Gwamna Bago don cimma sabuwar ajandar Neja.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma yabawa gwamnatin tarayya bisa matakin da ta dauka na daukar nauyin biyan kudaden jinya ga wadanda abin ya shafa da ke cikin mawuyacin hali da aka tura zuwa Abuja, baya ga matakin da ta dauka na kafa wani kwamiti mai karfi da zai binciki musabbabin faruwar lamarin.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Kungiyar kiristocin Najeriya reshen jihar Neja (CCN) ta yaba da martanin gaggawar da gwamna Umar Mohamed Bago ya yi kan fashewar tankar da ta afku a mahadar Diko da ke karamar hukumar Gurara a jihar. &nbsp; Shugaban karamar hukumar Daniel Tsado wanda ya yi wannan yabon a cikin wata sanarwa da ya fitar a Minna, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":2366,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2,9,8],"tags":[670,701,476],"class_list":["post-2365","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","category-tattalin-arziki","category-tsaro","tag-bago","tag-hadari","tag-niger"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/01\/1e8027a5-a197-40b8-a1e9-e1983192a8f7.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2365","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2365"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2365\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2367,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2365\/revisions\/2367"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2366"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2365"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2365"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2365"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}